BARAGURBIN KYAU 7

3 1 0
                                    


*BARAGURBIN KYAU*

*_Aysha D Fulani_*

*SHAFI NA BAKWAI*

*Page 7*

*_Afuwan don Allah rashin wuta ke hanani typing kulum_*


                    بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

_______Shiga cikin motar nai da sauri itama Ramatu ta shiga ɗayan bangaren, a guje naja motar nabar harabar  makarantar mu, mutanen da suke wurin ne suka dinga bin mu da kallo, saboda yau sunga abin da basu taba gani ba a kaina.
Kusan duk makarantarmu sunansa cewa bani da wani aboki ko wata ƙasa wacce za'a kallah a nuna, balle bangare samari wai a ce wance saurayina na ne aaa babu.
Jiyowa nai gurin Ramatu da tuni ta shiga rudani, dariya nai a fili ta jiyo tana kallona. "Taya kika gane Hamdan Ramatu?". Na aika mata da tambaya.

"Kamaninshi sun ɓaci da Shahid, tabbas kowa ya ganshi yasan cewa yaronshi ne sai dai son zuciya ya sa ka ƙi fadin gaskiya".

Ramatu Hamdan baida imani kwatata wallahi wannan ba komai bane a wurin shi, kinsan Allah ina komawa gida zan fadi wa Abba sai dai duk abin da zai faru ya faru.

Muna faka mota Ramatun tashige gida nima nai cikin gida,  ina shiga nai karo da Abba zai tafi masallaci ya, sai da nabari ya dawo sannan na same shi a daki na na sanar da shi.

Cike da mamaki Abba ya  rike baki  yana fadin, "Duk abin da zai yi miki kadda ki kulashi yanzu ba kince yana gun ƴan sanda ba, ki kyale lamarin a hanuna Allah ya ƙara kiyayewa".

"Ameen".

Na amsa na mike nabar dakin, ina shiga nai sallah nakwanta bacci sosai nayi sai daga baya na tashi naci abinci wanda rabona da shi tun daren jiya.

Dakin Umma na shiga na iske Shahid sai wasa yake akan gado, ya hau ya sako ita kuma umma na mai magana kadda ya karya mata gado. Yana ganina ya rugu inda nake yana mun Oyoyo.

Riko shi nai ina tambayarshi ya gida,na  zauna nake sanar da Umma abin da ya faru, mamaki fal ranta take fadin "Lallai bai da hankali amma ki kyale shi wallahi zamuyi maganin shi sannu, yanzu zuwa yai yafara tara maki jama a makaranta lallai bai da hankali".

Sallamar Ramatu ce ta dakatar da maganar da muke miƙewa nai muka koma dakina, nasan mai ya kawo Ramatu cigaban labarina take nema. Ramatu na kira sunan ina murmushi, kin san sanda Hamadar ya mai dani cikakkiyar mace, a lokacin na sha wuya amma dayake so ya rufe mun ido haka na kasa magana, a cikin dakin baki na gasa jikina.

Haka muka cigaba da rayuwa, Hamdan irin jarabbabun mazanan ne, da haka nima ya maida ni kalarshi ban iya jure kwana uku batare da ya kusance ni ba.

A tagafe kuma suna chan suna soyewa sai dai shi Hamdan bai san da wa yake tare ba, kwanci tashi asarar mai rai muna wannan rayuwar ni da shi soyayyar su da Zainab tai kamari, tayyada ya kosa yana ga wacece Zainab a rayuwar.

Wata rana nashiga gidansu Zainab nai dakinsu ina shiga tana wanka, cikin hukuncin Allah ta bar wayar a fili kuma da layin da suka saba waya. Kwai ba sai ga kiran wayar ya shigo wayar, hannu na kai na dauka ganin hasken wai a take  nai karo da number shi, inda Allah ya taimakeni wayar na silent, a hankali na dinga bin number da kallo har ta katse.

Aiko tana yankewa na bincike wayar tsaf abin da ban taba yima wani ba kenan, amma a ranar nayi shi, kuma na cikaro da tashin hankali iri-iri domin sakon soyayya ne kala-kala, da wanda yai mata da wanda taimai. Jin alamar tahowarta ya sa na maida wayar da  sauri na goge abubuwan da na duba.

Da dariyarta tashigo na dauke kaina duk da zuciyata na cike da rudani da ban mamakin taya haka zata faru akan a kanki na, daure wa zuciyata nai muka taba hira na taso nai mata sallama.

Ina shigowa gida hankalina a tashe na kule a ɗaki na rasa mai zanyi kuka ihu ko mai, zuciyata ce ta ban shawarar in dauki waya in gaya Hamdan ina son ganinshi yau don inyi mai dabara inga tabbacin abun da nake nema.

Aiko akai sa'a yana free, yace in jirashi zuwa magrib zai shigo. Haka na zauna adakina sai lokacin sallah ne kawia na fito. Ina idar da sallah aiko sai ga kiranshi na amsa na fito, har nazo bakin kofah na tuna a gaggauce na maida wayata daki na boye.

Fuskata cike da fara'a na zauna muka dinga hira, har yake tambayata dalilin neman shi haka, dariya nai na nuna babu komai kawia mai Ina son in ganshi ne ya sa na bukaci yazo.

Hira ta dauko dadi sosai na dube shi, nace mai baby zanje bayi plz sanmu wayarka na shiga bayi don Allah kaga babu wani haske a wurin.

Aiko Allah ya taimake ni ya miko mun wayar babu key a jiki, ina shiga na bincike wayar tsaf kuma naga abubuwan da nagani a wayar Zainab, hankalina a tashe na jingina a bango hawaye ne yafara bin kumatuna.

Daurewa nai na seta kaina na fito daga bayin, zama nai na daure zuciyata muka karasa hirar ana kiran isha'i yai mun sallama ya tafi.

Da kyar na iya kai kaina ɗakinmu, ina shiga na zube akan gado, kaina sai wani irin sarawa yake, tambayar kaina nake mai ke shirin faruwa ne, salati da sallalami na dingayi wallahi na shiga mugun firgici a ranar.

Kuma wani abun Allah shine tun daga wannan ranar idan na daga waya na kira Hamdan sai ya dinga cemun shi aiki ya yi mai yawa ba zai samu zuwa, itama Zainab ta dena shigowa gidanmu kamar ɗa da kusan ko wani lokaci muna tare.

Damuwa tunani suka hadu suka cunkushe mun ƙwaƙwalwa, lissafina gaba ɗaya ya kwace na rasa ina zan saka kaina in samu maslah wa zan gaya ma damuwata ya fuskance ni har ya san wani hali nake ciki.

Ashe abin da ban sani ba shine a wannan rana da Hamdan ya zo gidanmu a lokacin Zainab sukayi alkawarin bayyana wa junan ko'ita din wacece kuma da alkawarin idan ya ganta zai so ta fiye da yadda yake sonta a  boye.

Na rasa ina zansa kaina a hankali damuwa ta fara cimmi ni, ganin Hamdan shiru an ɗebe sati biyu babu shi a gidanmu wanda in yayi nisan zuwa shine kwanan hudu, kuma idan nakira shi kulum maganar itace yana aiki. Kuma dama hutun makaranta muke.

Ranar da ya cika sati biyu muka wayi gari da rasuwar mahifinsa, sosai muka shiga tashin hankali, Abbana da Abban Zainab dasu akai komai na wurin rasuwar haka mamana da maman Zainab suma sunje gaisuwa.

Har daki Baba ya sameni yace mushirya da Zainab anjima su Adda zasuzo muje gaisuwar tare, aikawa Zainab nai ta amsa da zatazo in lokacin ha yi yi.

Ana idar da la'asar muka kama hanya gidan tunda bawani Ni sane damu ba, abun mamaki baya karewa muna zuwa Hamdan yai wani kicin-kicin da raina ni duk a daukata zafin mutuwa ne, haka muka shishiga cikin gidan mukayi gaisuwa a kowani bangaren muka fito.

A baya Hamdan ya yi sati biyu bai zo ba sanadiyar rasuwar mahaifinshi ya ƙara wani sati biyun, da na kira shi a wayar maganar da ya gaya mun itace wai kadda na dame shi banda hankali ne banga abin da ya faru ba.

Katse wayar ya yi ya barni da'ita a hannu ina kallan ikon Allah wanda bai karewa.

Daga ranar na fara zazzaɓi damuwa ta sani gaba, na rasa ina zan saka raina kuma zazzaɓi mai zafi ga amai yin duniya mama ta tambayeni ko mun samu matsalah da Hamdan na ce mata aaa hidimar gida ce tai mai yawa. Zazzaɓi kamar wasa ya zama gaske babu ci bare sha, idan naci abinci ma sai na amayar.

Da farko Abba cewa ya yi zazzabin cizon sauro ne ko kuma shawara, haka na dinga anfani da magungunan gida amma ciwo kamar karo shi ake, duk wannan ciwon da nake ko leke Zainab ba taiba. Ina daki na mama ta iske ni ta tambayeni mai kefaruwa tsakanina da Zainab, dubanta nai nace mama idan na baki amsa ki gamsu da abin da zan gaya miki, nima ban sani ba amma ki jira lokaci in Sha Allah komai zai bayyana.

Kallonna tai cike da mamaki tana gyada kai Abba ne ya shigo ɗakin sanye da wani tirare mai kamshi, sai dai ni ina jin kanshi hankalina ya tashi nafara sheka amai. Ai babu shiri mama ta dauke  muka tafi asibiti.


✍️Aysha D fulani.
Facebook Aisha D Fulani.
What's app 09064234445.
Wattapd Fualni010.
Tiktok Fulani010.
Arewa book Aysha d fulani.



BARAGURBIN KYAUWhere stories live. Discover now