PART ONE

33 1 0
                                    

*BARAGURBIN KYAU*

*_Aysha Adam Alhassan Ɗan Fulani_*
           (Fulani)

A duk lokacin da zanji an ambaci wani abu waishe shakuwa ko kuma aminta ko ince aminiya, sai naji gaba ya yi wawan bugun da yai sanadiyar tarwatsa rayuwarta. Duba da yadda amana tai kanranci baza muce babu na Allah ba amma mafiya yawan su, maciya amana ne, domin da najikin ka ake cin amanar ka.
Aminiya wata kalmace wacce ake wa laƙabi da abin da ya shiga jikin ka ya zauna daram, tamkar fatar jikin ka. A wasu lokutan idan naga mutum yana rayuwa shi kadai sai in tuhumi kaina meye dalilin hakan, ganin babu mai bani amsa hakan yasa na ke jan bakina nai gum. A lokacin rayuwa tai mun juyin yuyayi wai kwado ya fada a ruwan zafi. A sannan ne nagane cewa rayuwa mutum shi daya itace mafi alkairin domin babu amini na kwarai.

SHAFIN FARKO.
Page 1


                    بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Kasan cewar yau juma'a yasa jama'a ke tafaman kai kawo jefi-jefi. Hannun Shahid ta riko, suna tafiya sai labarin masallacin juma'a yake ba ta, dariya tai ta dubeshi tana fadin, "Toh mai yasa baka ragomun alewa ba kashen kayan ka ai babu ruwana da kai wallahi".

  Hango Hamdan na tunkaro ya sa tai kicin-kicin da fuska, kara rike hannun Shahid tai tana  kokarin tsallaka titi da mutanen  suke ke kai komo,  sakamakon ba'a dade da sakkowa sallar juma'a ba, kuma wasu sun tsaya daurin Aure.
Saurin da Hamdan yakeyi ne ya fara bata tsoro duk da ta dake amma kirjinta sai dukan tara-tara yake, kokarin tsallaka titin take,  taji ya riƙe hannun Shahid da karfi ya jashi ya  kusa rinjayar ta, tana juyowa ta dauke shi da wani irin mari wanda yai ƙara tass, har sai da ya jawo hankalin mutanen wurin.

Saurin dafe wurin da marin ya  sauka ya yi yana dubanta, hankali tashe ya buɗe baki zai mata magana, amma ina bai samu dama ba saboda ta rigashi fara nata managar cikin daga murya take fadin.
"Sakin mun hannun ɗana ko nai maka ihun barawo, wannan wani irin naci ne don girman Allah, billahi muddin baka dena bibiyar rayuwata ba sai na yi maka abin da yafi wannan muni".

"Wallahi Hamdan na tsaneka duniya da lahira, na gaya maka kafita daga rayuwata idan kuma ka ƙi kiji wallahi Allah sai na maka abun da baka taba tsanmmani ba a duniyar ka, banza wawa dakiki wanda bai san darajar dan adam ba, kuma gani ga Shahid idan ka kara kokarin taba shi billahilazi sai kayi na dan sanin banza butulu".

Wani Dattijo ne da kalaman Mardiyya na karshe suka sauka akan kunne shi yai saurin wai-wayowa yana fadin "Asha! ke kuwa yarinya don Allah kiyi hakuri haba wannan ai bai kamace ki ba, tun dazu ina kallan duk abin da ke faruwa amma meya ya haduku don Allah?".

Kallan tsohon Mardiya tayi tana sake kallan titi domin taga mutane sun fara taruwa, "Kayi hakuri Baba wannan ba hurumin ka bane amma dukkan maci amana karshen shi in Sha Allah sai yafi wannan ƁARAGURBIN".

Bata jira cewar tsohon ba ta  tsallaka da sauri tana jan Shahid yaron da bai wuce shekara shida ba, tsohon ne ya juya yana duban Hamdan da  ya daskare a tsaye tamkar mutum mutumi.

Dafashi tsohon ya yi yana fadin, "kayi hakuri yaro kilah sonta ka ke take maka wannan wulaƙanci ko?".
Sabule hannun tsohon ya yi ya soma tafiya batare da yace mai uffan ba.

Tsallakawar Mardiya ke da wuya sai ga dan sahu yazo ta tareshi, kwatance tai mai ya dau hanya.

Tunda Hamdan ya fara tafiya tamkar wanda aka zare mai lakar jikinshi haka yake taka kasa, mamakine ya cika mai zuciya abin da bai taba tsanmmani Mardiya za ta mai ba yau shine take mawannan cin kashi a bainar duniya, shin ina son da ta take mai ina kaunar da take ikirarin tana mai, shin ko dai karya take mai dama ba don shi take ba, innalillahi wani'inna alaihi raji'un.
Tafiya ya ke yana zance zuci wanda ya fara fitowa waje, domin yadda yaga mutane suna kallanshi.

Kofar get din gidanshi ya tura mai gadi dake zaune bakin kofar dakinshi hannunshi rike da Qur'ani yana karatu  ya bishi da kallo, ganin bai kalli inda ya ke ba yasa shima ya mai da hankali shi kan karatun da yake.

Yana shiga cikin gidan ya wuce ɓangaren shi wanda ke cikin gidan, Zainab da ke aiki a kichin ta hango shigar shi falo. A jiye soson hannunta tai ta fito ta nufi inda ya shiga.
Bakinta dauke da sallama ta murda kofar falon wayam taga babu kowa a ciki, haka yasa ta miƙe ta shiga bedroom din shi, nan ma murda kofar tai ta shiga da sallama, yana kwance yai rigigine gabanta ne ya fadi ganin shi a irin wannan yanayin da bata taba gani ba.
Dear takira sunanshi tana hawa gadon, jin shiru yasa ta karasa ta shafo fuskarsa jin ruwa kamar na hawaye yasa ta zaro ido waje, Abu Amrah ta kira sunansa da karfin gaske wanda ya bayyana firgicin ta a fili ƙarara.
Miƙewa ya yi yana zauna, yana dubanta fuska cike da hawaye ya furta. "Plz fitarmun a dakina don Allah".
Kallan shi tai adan tsoroce kafin tamike tana fadin "Don nazo ina tambayarka shine haddamu wani tsawa mtswwwww! taja tsaki don ma nadamu da kai shine zaka mun haka, toh ka mutu a haka kai ka sani".
A harzuke ya mike tsaye saukar mari taji a gefen kuncinta, da sauri ta dafe wurin ta kallanshi girgiza kai tai tana fadin, "Ni ka mara dan nazo ina maka magana".
Gabanta ya matso yana jan tsaki cike da jin ɗacinta ya furta, "Kirama don Allah nace Ubanwa yai sanadiyar fadawata cikin wannan iftila'in idan bake zaki fita ko sai na miki wanda yafi na farko".

Saurin fita tai dan dago hannu yai da niyyar marinta.

Tunda Mardiya ta shiga cikin dan sahu ta jawo Shahid i jikinta sosia ranta ke mata zafi sai ambaton kamal hasbunallahu wani'iimal wakil take domin samun sassauci daga abin da takeji yana motso mata.

Wasu sirraran hawaye ne masu dumi su kai nasarar sauko mata akan kuncinta, ido ta kurawa Shahid tana kallan tsantsar kamar Hamdan a fuskar sa murmushin da yafi kuka ciwo tai, da za tai kukan da yafi wannan yawa  a lokacin da taji sauki akan abun da takeji yana kokarin bullowa ta zuciyarta.
Tsayuwar keken ne ya sanar da'ita isowar su bakin layin, sauka tai ta ciro kudinshi ta mikamai. Hannun Shahid taja suka shiga cikin gida, a bakin kofah suka tarar da Adda zaune wacce ta bisu da sannu da zuwa, ganin fuskar Mardiya chunkushe da bacin raine yasa ta wurgo mata tambayar Lafiya.

"Idan har Hamdan bai fita a rayuwata ba na rantse da tsarkin mulkin Allah zan rabashi da dukkan wani farin ciki na rayuwarsa, koma in rabashi da rayuwar baki ɗaya".

✍️Aysha D fulani

Facebook Aisha D Fulani

What's app 09064234445

Wattapd Fualni010

Tiktok Fulani010

BARAGURBIN KYAUWhere stories live. Discover now