NI MA MATARSA CE PAGE 4

118 11 0
                                    

Hakkin mallaka nawa ne ban yarda a juya mun labari ta ko wace siga ba, a guji karanta Shi a YouTube ba tare da izinin marubuciyar ba.

                FREE PAGE 4
            *******************
      Haj murjanatu  daya daga cikin manya manyan gidajenta ta zabama mujaheeda inda zata zauna tare da mijinta,bayan da mujaheeda ta tabbatar Mata da gidan yayi Mata ya dace da tsarinta.Duk da gidan lafiya lau yake baida wata matsala haka tasa akara gyara Shi tace tana bukatar amaida Shi sabo.

    Ta bangare daya Kuma tuni duk kayan dakin mujaheeda sun sauka daga Dubai Bana tsammanin hatta cokali an sayama mujaheeda daga Nigeria komai daga waje aka sayo.
Hatta kayan da zata sa na biki daga waje akayo order su.mujaheeda Kam ta samu dukkan gata don idan gata Yana yawa hakika yakamata yayima mujaheeda yawa.shirye shirya ake sosai na auren Shi Kansa gidansu gani kawai Alh Mustapha labaran yayi anata gyara babu KO Neman shawararsa hakan yasa shima baisa Kansa aciki ba,don yafi kowa sanin halin Matarsa na kushe da gwasala musamman idan batasa Ka acikin lamarinta ba.
   Shi Kam Taufiq ya rasa abinda yasa ya Sami Kansa da rage zumudi da kaguwa akan auran Nasa KO don fitintunun da suke ta biyo baya ne oho,sai dai duk wani shiri shima ta bangarensa angama.
  Taufiq yayi sallama ya shiga dakin mahaifiyarsa Haj saratu inda take zaune tare da babbar yarsa Haj Bilkisu ,Haj saratu ta dago cike da walwala ta dubeshi tace " yauwa Taufiq Ka karaso" ya lalubi kujera ya zauna Yana Dan murmushi yace " Eh umma " sannan ya dubi Haj Bilkisu yace " Ashe kina gidan" tace "eh Ka tasoni " yace " ni kuwa?" .
  Haj saratu tace " Ka tasota mana,lefe ta kawo tace angama hada komai Kuma ya kamata akai tunda bikin nan Bai wuce Saura sati biyu ba" ya gyada Kai yace "to shine sai an kirani," ya dubi Haj Bilkisu yace "to Ai yaya keya kamata kisa Rana ki kwashi Wanda zaki kwasa kuje Ku Kai musu" Haj Bilkisu tace "to Amma dai ai a sanar da can gidan su mujaheedan cewa zaa kawo lefe" Taufiq yace " badamuwa idan kinsa lokaci sai ki gaya min ni kima Saina sanar dasu zaku zo".Haj saratu tace "eh hakan zaayi,ke kina ganin yaushe zaa Kai musu kayan" ta tambaya tana kallon Haj Bilkisu.
  
     Haj Bilkisu ta jinjina Kai tace " AI umma ina ganin me zai hana akai musu gobe idan yaso sai Taufiq ya sanar dasu zamu zo gobe,tunda an Riga angama komai ai babu amfanin cigaba da ajiyarsu" Haj saratu ta juya ta dubi Taufiq tace"To kaji ?" .
  Ya gyada Kai yace " eh, badamuwa Zan sanar dasu insha'Allah,goben sai akai kawai" " To Allah ya kaimu" cewar Haj saratu.
    Haj Bilkisu ta gyara zamanta tana duban Taufiq tace " AI gaskiya kayi kokarin hada lefen nan ,don koina zaa Kai su to babu yadda zaayi a kushe kayi matukar kokari , Allah dai yasama auren albarka" gaba daya suka hada Baki da Amin.
  Haj Bilkisu tace " To yanzu shikenan ba'anan gidan zaku zauna ba,agaskiya fitinar mahaifiyar mujaheeda yayi yawa,duk kyan da wajen can yayi sun raina " Taufiq ya cije baki alamar har yanzu ransa Bai masa dadi ba akan hukuncin Haj murjanatu.yace " babu yadda zanyi yaya tunda Abba ya Bani umarnin na amince,Amma insha'Allah sauri zanyi na kammal gidana mu koma can don Bana Jin Zan laminci wulakanci akan zamana agidanta,don matukar ina kaunar rayuwar yanci dole nabar musu gidansu," Haj Bilkisu tace " kwarai kuwa kayi tunani me kyau ai kawai kayi kokari Ka kammala gininka,don Bana Jin wannan matar zata sa maka Ido ba tare da tayi kokarin juyaka ba matukar kana Zama agidanta karshema gori ya biyo baya " Taufiq yace " Saima kinga irin katon gidan data bamu ,
  Don mujaheeda ta kirani dole sai naje Naga gidan idan yayi min na gaya Mata Bassi nazo ba matukar yayi Mata shikenan,Amma yadda ta matsa yasa naje,gidan yayi girma da yawa Amma tunda na fahimci yayi Mata Kuma saboda ita mahaifiyarta take son mu zauna agidan yasa nace yayi don Bana son ma wata doguwar magana".
   
Haj saratu ta saki tsaki ahankali tace "shikenan dai anyi Mata abinda take so,sam bana Jin wani kwanciyar hankali matukar ba auren nan Naga an daura ba,gaskiya Taufiq ina tausaya maka don banjin kayi dacen suruka sai dai babu yadda zaayi basa Bai tsallake kaddararsa "
   Haj Bilkisu ta aje numfashi ahankali tace " umma sai dai addua tunda Shi Taufiq yaji ya gani Kuma Yana kaunar yarta hakanan zai cigaba da hakuri,Amma sangarta da ràshin tarbiyyar mujaheeda waye Bai sani ba,Shi Taufiq dinma AI yafi kowa sani ,kuma wace shawarace baa bashi ba Kan Kada ya Kai Kansa Amma soyayya ta makantar da Shi,AI aikin Gama ya Riga ya gama Allah dai yasa ayi a sa'a kawai".

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now