page 38

144 7 4
                                    

NIMA MATARSA CE
        NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
  ( YAR GIDAN IMAM )
BABI NA TALATIN DA TAKWAS
            **********
   Sosai Alh yake son Hajara ya rasa sukuni ,kullum zuciyarsa tana Kara kwadaita masa Hajara.

Ayayinda ita bata gane komai ba aikin gabanta take yi kawai.kullum tana tare da yar Haj shakuwa mai tsanani ta Kara shiga tsakaninsu .

Hajara tayi matukar Samun nutsuwa bata da damuwar komai domin tana cikin wadatuwa da komai, kamar yadda tasan can ma iyayenta wahala ta Ragu musu tunda suna Samu daga aikin da take yi naira bata dauka su take turoma.idan ma akwai abinda ke damunta to ba zai wuce maganar sani ba da babu wata hanya ta haduwarsu, tana son sani bata son duk wata baraka da zata iya shiga tsakaninsu. Bata gane sani na cikin damuwa akan zamanta a jigawa ba sai wani zuwa da tayi gida kusan fada sukayi sosai domin yace lalle sai dai ta aje aikin ta dawo gida Wanda ta kasa yi masa alkawarin zata iya yin hakan domin alokacin ta Kara tabbatar da cewa itace gatan iyayenta kusan ci da shansu da kudin maganin mahaifinta duk ta sanadiyyar aikin nan take samunsu domin ita kanta tasan cewa ta hadu da mutanen kirki babu abinda zata ce ma Haj sai dai godiya mara musaltuwa.

   Don haka haka ta dawo jigawa babu wata cikakkiyar fahimta tsakaninta da sani , abin Kuma Yana damunta Yana kuma yi Mata ciwo, sai dai bata da yadda zatayi iyayenta sune gaba akan komai.

Lokacin dawowar Mallam sule asibiti yayi sun dawo Kuma likita ya duba ya Kara dibar masa watanni shida akan ya dawo asa ranar aiki , sun Kuma Kara masa mgunguna, wannan daga ranar aikin da sukeyi ya Fara sa ma su zainabu shakkun ayya kuwa ba suna Jan maganar bane saboda suna ganin ko ciwon nasa Bana tashi bane, domin dai har alokacin jikinsa cikin tsanani yake sai dai sauki na Allah.kwanakinsu biyu agidan Haj ta Kara bada mota da Kayan abinci aka maidasu gida.

  Alokacin ne bayan dawowarsu gida aka Sanya ranar Auren Hajara da sani watanni Tara masu zuwa.duk da daga sanin har mahaifansa babu wani Wanda ya nuna jindadi ko sha'awar hakan, kawai dai sun Zama kamar Yan abi yarima asha Kida.

Aranar da Hajara ta sanar da Haj ansa ranar aurenta , ta tayata murna ta Kuma Fara tunanin ranar da zasu rabu domin tasan zata shiga damuwar rashinta kasancewar ta saki jiki ta shaku da Hajara yarta ma ta shaku da ita tabbas tasan ranar rabuwa akwai matsala da damuwa.

Amma ta bangaran Alh kuwa ranar kasa bacci yayi , ta yaya Hajara zatayi aure bayan itace mace ta farko da yake Jin tamkar numfashinta zai fita idan ya tuna bazai iya samunta a matsayin Mata ba.ya rasa inda zaisa kanta Bai tabbatar ya fada masifar kaunarta ba sai awannan daren da Sam ya kasa runtsawa washegari ma haka ya tashi kamar Wanda yayi jinya duk Wanda ke gidannan ya fahimci akwai canji da matsala atare da Alh ,ya kasa ci ko sha, sai wani azababben ciwon Kai da ya addabe shi.bai Samun sauki sai ya dubi Hajara .lamarin ya zamto tamkar wata masifa agareshi.

Washegari bayan fitar Haj .Alh ya rutsa Hajara a dakinta, tayi gaggawar tashi daga Kan gadon tana kallonsa cike da tsarguwa da daburcewa tace muryarta na rawa " kana son wani abu ne?  Ya girgiza Kai gami da zaunawa a gefen madubin kusa da gadon yayi Mata kallon tsaf sannan yace " koma ki zauna magana nake son yi da ke" asanyaye ta koma ta zauna tana kallonsa hakanan taji gabanta na matukar faduwa.

  " Ansa Miki ranar aure Ko?" Cike da mamakin tambayar tace " eh " .ya ja numfashi ya aje sannan yace " hakanne yasa naji zuciyata ba zata iya dauka ba" tayi saurin cewa " me yasa?" Ya dubeta sosai kamar daga sama Hajara taji yace " saboda ina matukar sonki fiye da komai a rayuwata Hajara" tayi zumbur ta Mike tana yi masa kallo Mai cike da mamaki tace " subhanallah me zanji haka, don Allah kayi hakuri Ka rufa min asiri Ka daina wannan maganar Kada Ka Kara yinta don Allah" ya Matso kusa da ita yace " Bana tsoron kowa ya ji Hajara ina sonki " ta juya da sauri zata fita daga dakin nan da nan yasa hannu ya fisgota ya dawo da ita cikin dakin

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now