NI MA MATARSA CE PAGE 41

257 10 0
                                    

NIMA MATARSA CE
                NA
HABIBA ABUBAKAR IMAM
  ( YAR GIDAN IMAM )
BABI NA ARBA'IN DA DAYA
          *********

  Tun daren ranar ta sanar da Mallam kallah da sabira batun zuwanta jigawa ita da Mallam Umar.

Mallam kallah yayi Mata kallon tsaf yace " Kai Shi Ko Mallam kallah da shegiyar tattaga ya ke , da tsabar iyayi, meye nasa na daukarki kuje jigawa, Kenan Shi yama yarda da karyar taki"
  Sabira ta tabe baki tace " iyayi ko kinibibi, su suka sani, yin hakan dai bashi zai kankare Miki zargi da bakin fentin da ake ganinki da shi ba".

Kai kawai Hajara ta jinjina ba tare da tace komai ba, domin dai ta gaji da yi musu bayanin gsskiyarta tunda ba zasu taba yarda da ita ba, to tana ganin yi musu bayanin kullum baida wani amfani.

Maganganun da suka cigaba da yi ne marasa dadi yasa Hajara ta tashi ta shige daki.haka ta kwana cikin godiya ga Allah daya hadata da Mallam Umar domin ayanzu dai damuwa ta Fara yi Mata sauki.

Washegari da wuri Mallam Umar ya zo , sai da ya Samu kebewa da Mallam kallah yayi masa bayanin dalilin zuwansu jigawa.mallam kallah ya tamke fuska yace " zadai Ka wahalar da kanka kawai , domin duk abinda Hajara ta gaya maka karya ne , bansan dai dalilin da yasa kake son sa kanka a wahala ba" ya girgiza Kai yace " Banga karya acikin idon Hajara ba, Kuma taimako bsi taba Zama wahala ba, ni na ji ina son na taimaketa don haka babu wata damuwa in sha Allah".

Fahimtar da Mallam kallah yayi na cewar Mallam Umar bazai taba sautarensa ba yasa yayi shuru , daga bisani yayi musu fatan dawowa lafiya.
   Har Hajara da malllam Umar suka Kai jigawa muhseena tana hannunsa.Babu abinda ya bace ma Hajara domin har kofar gidan Alh ta Kai Mallam Umar .

Sai dai wannan Karon wani maigadin suka tadda ba Wanda suka taba gani ba.mallam Umar ya tsaya yayi masa bayani sosai na mutumin da suke nema.
   Maigadin yayi Jim alamar tunani daga bisani yace " gaskiya bansan wani mutum haka ba, domin bashi bane agidan, ni Kaina ban wuce watanni uku da Fara aiki ba, Kuma gadin kawai nake yi na gida domin har yanzu babu Wanda ya tare agidan". Idanun Hajara suka cika da kwalla ta Kara sa hannu ta rungume yarta.
    Mallam Umar ya numfasa cike da damuwa, baisan dalilin da yasa tun daga ranar da Hajara ta bashi Labarinta yaji Yana so ya taimaketa ba , tausayin ta Kuma da tausayin yarta suka tsaya masa arai , yadda ko me yake yi baya rabo da tunaninsu.

Ya dubi Hajara yace " Bana son ki cigaba da sa ma kanki damuwa, domin babu maganin da hakan zai yi Miki".
Ya Kara numfasawa yace " bazai yuwu mu ce zamu cigaba da nemansa a babban gari irin wannan ba, domin abinda kamar wuya,Amma ina son ki sani  Allah baya zaluunci ya Kuma Sanya Shi abin haramtawa a gare mu, don haka ki sama ranki Allah zaiyi Miki sakayya ko a dade ko ajima ".

Cikin hawaye tace " yanzu shikenan haka yata zata rayu bata San ubanta ba ?" Ya dubeta sosai yace " ko kin ganshi yanzu , kina tsammanin cikin ruwan sanyi zai karbi muhseena amatsayin yarsa ( ya girgiza Kai) bazai taba amsarta cikin dadin rai ba, Kuma a matsayin sa na me kudi Bana Jin. Zamu iya yaki dashi tunda ayanzu an maida kudi sune komai,". Ya gyara tsayuwarsa Yana cigaba da kallonta yace " KO da nace mu zo, mun zo ne kawai saboda ko da mun ganshi ya San Yana da ya da ke ko ya amince ko Bai amince ba ya dai sani ". Gaba daya Hajara ta rushe da kuka me karfi,  tana fadin " ya zanyi da rayuwata, Bana Jin Zan cigaba da rayuwa a Durmi , kawai Ka tafi Ka barni anan domin idan na cigaba da Zama a can bazan taba rabuwa da tashin hankali da damuwa ba, mutanen garin Kuma ba zasu taba yi min Uzuri ba haka Zan zauna yata ta taso su cigaba da jifanta da mummunar Kalmar shegiya, karshe su jefa Mata tsanata kamar yadda suka jefama kansu".

Tausayin ta ya Kara kama Shi ya yi kasa da Kansa ya na nazarin maganar da yake son ya fada Mata.

Zuwa Dan wani lokaci ya dago ya zuba Mata Ido cike da wani yanayi da yake Jin bazai iya Hana Kansa faden abinda ke cikin ransa ba yau.
      "Hajara" ya Kira sunanta a tausashe, ta amsa ahankali ba tare data dube Shi ba.yace " ina son ki kwantar da hankalinki, ni Umar Zan amshi yarki muhseena amatsayin yata Zan riketa Zan bata sunana a matsayin uba Zan kare Mata martaba da mutunci amatsayin ta na ya ta, daga karshe Zan aureki domin Zama Uwa da uba ga Hajara ba tare da mun rarraba kanmu ba".

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 26, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now