CONTINUE PAGE 5

97 6 0
                                    

Taufiq yayi kasa da Kansa zuciyarsa na tafasa ya kasa cewa uffan.haj saratu ta numfasa tace " To ni dai bansan me Haj murjanatu take son ayi Mata ba ,duk abinda tace ana kokarin yi duk dai don asami zaman lafiya Amma na rasa dalilin da yasa kullum take kokarin bata al'amarin nan, abin ya Fara damuna kwarai da gaske ,don ina ganin ko Anyi auran nan tamkar ba zaa samu wani kwanciyar hankali ba".
  Haj Bilkisu tace cikin fusata " na rasa gane me take so Kuma me take nufi, Ko itace Yar Karuna iya karyar arzikin da zata dinga yi kenan, shin su kadaine masu kudi Kuma mu din bamu da rufin asiri ne meye abin kushe agaremu ,me yasa take jindadin wulakantamu?"
  Haj laraba tace don Allah don son Annabi abar maganar nan kadama akara yinta.
  A sukwane Taufiq ya tashi ya fita batare da yace komai ba Haj laraba ta bishi da cewa " Adaiyi hakuri Taufiq babu komai rayuwarma guda nawa take".
  
  Haj Bilkisu ta juya ta cigaba da maganganun ta na bacin rai ayayinda Haj laraba ta cigaba da tausa su .azahiri Haj saratu abin ya Fara fita kanta ta gaji da wadannan kananan maganganun ,kamar yadda ta kasa gane ina matsalar take? Me Haj murjanatu take nufi? Meye tunaninta akan danta Taufiq?.irin tambayoyin da Haj saratu take ta yima kanta kenan.

    Taufiq na zaune asaman kujerar fslonsa ya harde hannayensa a gaban kirjinsa Yana Kada kafafuwa Kaida kallon fuskarsa kasan Yana cikin damuwa.ya tashi ya shiga sintiri a tsakiyar falonsa.
  Yana tunanin halinda yake ciki agame da lamarin mujaheeda.ya daga Kai ya na Karema falon kallo, ahankali ya tambayi Kansa shin meye aibun wannan wajen da mujaheeda ba zata iya Zama aciki ba?, Me yasa Haj murjanatu take kokarin daukarsa a sakarai ? Wane irin nakasu gareshi da suke kokarin kaskantar dashi shin ahaka zai auri mujaheeda idan ya aureta wace irin rayuwa zaiyi da ita.
   Shin mujaheeda ta dace dashi kuwa? A hankali ya Sami Kansa da ba Kansa amsa da cewa mujaheeda bata dace dashi ba.
  Rayuwar su ba zata taba Zama dai dai ba da muguwar rawa gwamma kin tashi baya Jin zai iya auran mujaheeda bayan duk wadannan abubuwan dake fsruwa.
Me zai hana bazai rabu da ita ba ya Sami dai dai dashi.
  Ya koma ya zauna Yana kokarin sama Kansa natsuwa da dangana akan mujaheeda.
Ahankali ya Ciro wayarsa daga aljihunsa ya Danna ya Kira mujaheeda bugu daya acikin na biyu ta dauka.
  " Taufiq" Bai amsa ba yace cikin dakakkiyar murya " na kiraki nayi miki godiyar cin mutuncin da mahaifiyarki tayima yan' uwana " mujaheeda ta yi saurin cewa " don Allah kayi hakuri nima banjidadi ba Kuma bana gidan hakan ya faru don Allah kayi hakuri"
  Ya girgiza Kai yace " ba lefinki bane don haka basai kin Bani hakuri ba,tunda lamarin nan ya Zama haka ina ganin muyi hakuri kawai da juna Allah ya hada kowa da rabon sa don Bana Jin Zan cigaba da jure irin wannan bakin wulakancin daga mahaifiyarki,Wanda ke kanki da da gaske kina min son da kike ikirarin kina yimin da baki bari hakan na fsruwa ba Amma tunda haka kika zaba na hakura abar maganar aure.....?
  Adaburce mujaheeda ta Mike duk ta gigice tace " Abin bai Kai haka ba  don Allah Ka daina wannan maganar ta yaya zakace Ka fasa don Allah kayi hakuri "
  Ya girgiza Kai yace " kiyi hakuri Amma ina son ki sanar da mahaifiyarki na hakura da auran yarta ta je ta aura Miki Wanda take so Wanda zata samu natsuwa dashi, ni na hakura "
Yana Gama fadin haka ya kashe wayarsa.lokaci daya mujaheeda ta kwala ihu Wanda ya dawo da hankalin Haj murjanatu kanta da take zaune afalo da saurin gaske ta tashi ta taho dakin .
  Shigowarta yayi dai dai da lokacin da mujaheeda ta sulale kasa ta Fadi sumammiya tana dafe da gefen kirjinta idanun Haj murjanatu suka firfito nan da nan ta fita hayyacinta Tayo Kan yarta tana adduar Allah yasa ba ciwon zuciyarta bane ya tashi .
    DAGA TASKAR YAR GIDAN           IMAM .

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now