ƘANWAR MAZA 6

1.5K 15 1
                                    

ƘANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.

*AFUWAN BAN EDITING BA*

P6

Iya ƙarfinta take ihu, tana kiciniyar sai ya sauketa, amma yayi burus da ita, sai da ya je soron gida, sannan ya sauketa ya ja hannunta zuwa cikin gidan.

Aliyu ne a tsakar gida yana yiwa mama wanki, ya ɗago ya kallesu ya ce "Ya dai, ya kake jan ta tana ihu, makarantar fa?"

Hauzaifa bai amsa masa ya tambaye shi"Mama tana nan?"

"Eh tana nan" Aliyu ya bashi amsa.

Jin ihun ruma ne ya sanya mama katse sallar walahar da take yi, ta fito tana tambayar lafiya.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Yaya Umar, shi ma ya yi shirin fita. Duk suka zubo musu ido suna jiran jin ba'asi.

"Mama wallahi yarinyar nan ba ta da mutunci, daga sakata a makarantar nan ta fara tayar mana da hankali, yaushe yarinyar take da sikila ban sani ba?".

Mama ta ɗan yi sororo ta ce "Wace irin sikila kuma?"

"To haka ta je ta ce wai sikila ce da ita, ta tashi tsaye ma ta ƙi sai a bayana na goyota"

Yaya Umar ya kalleta ya ce "Ke meya sameki?"

Cikin in da in da ta ce "Dukana aka yi, kuma wallahi na ji zafi sosai shi ne na ce musu sikila ce da ni, na ga wata 'yar makarantar bokonmu ba a dukanta saboda sikila ce ita".

"Shi ne ki ke yiwa kan ki fatan ciwo saboda baki da hankali, ke dama za a zauna da ke baki yi abin da za a dake ki bane ba, me ki ka yi aka dake ki?" Yayi maganar cikin tsare gida.

Cikin kuka ta ɗage ƙafar wandonta, shatin bulala ya kwanta a kan fatarta, ta kalli mama ta ce "Mama kin ga fa, dan Allah a cireni wallahi ni ba zan iya makarantar nan ba, wai ban iya karatu ba shi ne aka yi mini wannan dukan, ni wallahi ba zan iya karatun nan ba, ga duka ga karatu mai yawa, da wanne zan ji?"

Cikin tsawa Yaya Umar ya ce "Wuce mu je makarantar, sai kin ci ubanki yau, ai dama karatu aka turaki ba wasa ba"
A karo na farko ta yi wa yaya Umar gardama tana kuka, ta riƙe hannun Huzaifa, ta ɓuya a bayansa.

"Ni nake miki magana ki ke ɓuya a bayansa, ba zaki fito ki wuce ba"

"Dan girman Allah kayi haƙuri, wallahi idan suka san ƙarya nake, sai sun kusa kashe ni, wallahi duka ake na tashin hankali a makarantar nan" kuka take wiwi kamar wadda aka yiwa mutuwa, mama dai ta kasa magana.
Huzaifa kuwa janyota ya yi daga bayansa, ya ce Wallahi ba zai kareta ba sai dai ayi mata duk abin da za ayi mata.

Yaya Sadik ne ya fito daga ɗakinsu, yana zuwa ya ture Umar, ya kamo hannun Rumaisa, ya wuce da ita ɗakin su.

Suna shiga ya zaunar da ita, shima ya zauna ya ɗan ƙura mata ido sannan ya ce "Auta, meke damunki ne, kullum sai an yi rigima dake an ce ba kya ji, ke ko haushi ba kya ji?"

Ta girgiza kai ta ce "Wallahi ina jin haushin yadda aka tsane ni kullum ace bana ji"

"To yanzu meyafaru, har aka dake ki ki ke cewa sikila ce dake? Kin san sikila kuwa meyasa ki ke fatan wannan ciwon?"

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now