ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.12
Mai sunan Baba ya kalleta a tsanake ya ce "Sata ki ka koma yi kenan ko?"
Ta girgiza kai da sauri ta na zazzare ido.
"Ba zaki buɗe baki ki yi mini magana ba?"
"A'a Yaya wallahi ba sata nake yi ba"
"To idan ba sata ba, me ki ka yi, kin san su masu bikin ne, ko kuma sun sanki, idan ba sata ba baki suka yi, ko nan aka aike ki?" Ta girgiza masa kai.
Ya ce "Good, tashi ki je ki yi alwala ki yi salla, zan gauraya da ke, tashi maza ina jiran ki"
Huzaifa da yake ta huci, ya cika ya batse kamar ya sha yeast ya ce "Wallahi yau sai na lallasaki, za ki gane baki da wayo"
Gwaggo ta ce "Ku dai din ga haƙuri yarinya ce, ƙuruciya ce kawai take damunta"
Huzaifa ya yi ƙwafa ya ce "Ba ƙuriciya da yarinta ba, Allah ya sa ɗanyar ƙwaƙwalwa ce a kan ta da ba ta nuna ba, sai na lallasata na koya mata hankali"
Duk da tana cikin tashin hankalin rashin sanin hukuncin da za ta fuskanta, hakan bai hanata murguɗawa Huzaifa baki ba, tana harararsa, duk da laifin da ta tafka masa.
Daga shiga banɗaki alwala ta tsiri kashi, duk dan ta ɓata lokaci kar ayi mata hukunci mai wahala, ta na fitowa, Umar ya ce a tsakar gida za ta yi sallar, dan haka ta ɗau hijjabi ta tayar da salla.
Ita kanta ba ta san adadin raka'ar da ta yi ba, kawai yin sallar take cike da zullumi, a sujudar ƙarshe kuwa kai kace neman gafara take ko bacci tayi, amma babu ɗaya nazari kawai take.
Haka ta idar ta saka addu'a, abin da ba ta saba ba, ko sallar ta yi sai mama ta yi ta faɗa sannan take zaman yin addu'a.Ganin taƙi sallame addu'a ne ya sanya Umar yi mata wani irin kallon, da babu shiri ta shafa addu'a ta tashi.
Ya ce "Oya, kamun kunne"
Cikin marairaicewa ta ce "Dan girman Allah Yaya.....
"Shut up! Zaki abin da na ce ko kuwa?"
Jiki a sanyaye, ta durƙusa ta kama kunnenta, nan da nan jikinta ya hau rawa, ta fara gajiya ta saka kuka.
Gwaggo ta ce "Kai ina mace ina wannan goho, kai meyasa ba ka tsoron Allah ne? Ke tashi dalla wannan wace irin azaba ce?"
Ruma ta ce "A'a Gwaggo, ba zan iya tashi ba sai ya ce dan Allah ku tayani bashi haƙuri"
Mai sunan Baba yayi shiru, ya ƙi kula Gwaggo, ta dubi mama ta ce "Ke ba zaki saka baki ya ce ta tashi ba, tun da ni ban isa ba?"
Mama ta ce "Ba haka bane Gwaggo, ai gara a din ga hukunta ta idan ba haka ba, sangarta da rashin jin da zata yi sai Allah ruma ba ta ji sam" ƙarshe mai sunan Baba ya tashi ya bar gidan ma gaba ɗaya ruma kuma ko da wasa ba ta tashi ba daga kamun kunnen, sai dai ta cika musu gida da koke-koke da magiya.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, na tuba na bi Allah, dan Allah ki bashi haƙuri ya ce in tashi"
"Babu ruwana, ba dai ba kya ji ba, ai na gode Allah da ya bani waɗanda zasu hukunta ki idan ki ka yi ba dai-dai ba, kuma kar ki sake kiran sunana"

YOU ARE READING
ƘANWAR MAZA
RandomLabarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuwa da ƙaddararta, ko wace iri ce ƙaddarar ta ta?