ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.P11
Girgiza kai kawai Abubakar ya yi, ya ja bakinsa ya tsuke.
"Yaya ya na ji kuma kayi shiru?"
"To ruma ba dole na yi shiru ba, kowa yana nemawa kansa mafita a rayuwa, amma ke in da ki ka dosa daban?"
"To wai me na faɗa ba dai-dai ba?"
"Yanzu ke tsakanin ki da Allah, kin taɓa ganin mace a titi tana bada hannu a ƙasar hausa?"
Ta ɗan yi shiru sannan ta girgiza masa kai ta ce "A'a, to mawaƙiya fa ko film?"
Abubakar ya ce "Ba kushe sana'ar wani zan yi ba, amma ki yi tunanin wani abun daban"
"To ba sai a buɗe mini kanti ba"
"Yanzu a unguwar nan gaya mini shagunan da ki ka ga mata ne a ciki suke sayar da abu?"
Ta yi farat ta ce "Ga maman Olu beyerabiya"
"To ke bayerabiya ce?"
"A'a amma dai....."
"Kin ga, ya isa haka, dama ni a kan career ki nake magana, tun da baki gane me nake nufi ba shikenan" ita sam ba ta ga aibun abin da ta ce tana so ba, dan haka ko a jikinta ta share.
Gwaggo ta fara shirin tafiya, su Yasir suna ta murna, dan dama duk ta ishe su da faɗa da azabar saka ido.
Shi kansa mai sunan Baba murna yake ta tattara ta tafi ta bar musu gida su huta, dan ta saka shi a gaba da yawa, dan ma Allah ya taimaki Abubakar bai fi sati ba ya koma makaranta.
Amma kullum cikin surutu takewa mama "Hauwwa wannan zagada zagadan yaran naki, duk sun isa aure amma kin tare su a gaba kina ado da su a gida, ga ƙauye can muna da mata burjik, amma dan mugunta kin tare su kin hana su motsi'Mama ta ce "Haba Gwaggo, guda nawa yaran suke, haryanzu su Baba basu haɗa talatin ba fa, duk girman jiki ne, kuma kina ganin irin rayuwar da ake sai godiyar Allah, babu mai ƙwaƙwarar sana'a sai ƙarfin hali, idan suka ɗauko aure da yaya za su riƙe?"
"Ba wani nan, idan mutum yayi aure Allah zai warware, amma kallesu dan Allah tuma-tuman gwauraye ki na ado da su a gida, babu mai mata, kalli dai wannan zagaren, sai dai ya shigo fuska kamar bajimin sa, ya zo ya ɗau abinci ya fita yana zazzare ido kamar wani zaki, ko fara'a ba ya yi, kai haka zaka yi wa matar ma idan an aureka?, ko da yake ma wace macence za ta auri mutum ba fara'a ba komai fuska kamar kunun kanwa ba rahama"
Lomar Abincinsa kawai yake kawai, ko motsi bai yi ba, balle ya nuna ya san da shi take, yana jin ta ya share ta.
Ruma kamar ta kwashe da dariya, jin an ce fuskar yaya Umar kamar kunun kanwa, amma sanin ruwa ba sa'an kwandon ba ne ya sanya ta ja bakinta ta tsuke."Umaru da kai fa nake" A hankali ya ɗago idanunsa ya yi mata wani irin kallo, ya mayar da kan sa ya cigaba da cin abinci.
"To Allah ya kyauta, ka ma dai mayar da ni mahaukaciya, ka je ka ƙarata, tattara kayana ma zan yi na bar muku gidan ku, gobe goben nan zan bar garin nan.
A hankali yasir ya ce "Alhamdilillah, Allah ya raka taki gona"
A rikice ruma ta ce "Haba Gwaggo, ni bana son ki tafi, dan Allah ki zauna bamu gaji da ganinki ba".Huzaifa ya yi ƙasa da murya ya cewa Abdallah"Ji munafukar 'yar nan, ko a gidan uban waye bamu gaji da ganin na ta ba, mata duk ta addabi mutane?"
Abdallah ya ce "Ashe ka manta wacece ruma, ai wannan yarinyar tsaf sai ta haɗa yaƙin duniya na uku, duk abin da ta san za ta aikata wanda ba a so shi take yi"'
YOU ARE READING
ƘANWAR MAZA
De TodoLabarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuwa da ƙaddararta, ko wace iri ce ƙaddarar ta ta?