ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.P5
Sak suka yi gaba ɗayansu, lomar da Yaya umar ya haɗiya ya ji taƙi wucewa tana kai komo a wuyansa kamar zata dawo. Amma ya basar kamar bai san me suke faɗa ba.
Huzaifa kuwa tsam ya miƙe yana faɗin "Ai sai da na ce kar ki saurareta ki ka ƙi, sai ku san abin da zaku gaya mata" yana maganar ya bar tsakar gidan.
Mama ta rasa mai zata cewa Ruma da hankalinta zai ɗauka, sam yarinyar bata tunani dai-dai da shekarunta."Wai ya na ji kin yi shiru? Me kuma nayi?" Ta yi maganar cikin taɓara.
Cikin ƙarfin hali mama ta ce "Ke a ina ki ka ji wannan kalmomin da ki ka tambayeni?"
"Mama ya kuma ki ke tambayata bayan nima tambayarki nayi"
"Ki amsa mini dan ubanki" mama tayi maganar a hasale.
Ta ɗan cuna baki sannan ta ce "Ba wani ne ya gaya mini ba, kece ki ke jin radiyo ranar, na ji ana cewa ayi wankan janaba idan aka yi ko me? Oho na manta shi ne nake son na san meye janaban, kuma meye wankan. Shi kuma fayɗe idan aka faɗa a radiyo sai na ga hankalinki ya tashi kina girgiza kai kina Allah ya tsare zuriyar musulmi baki ɗaya, shine nake son na san menene?"
"Tirƙashi, aiki ga mai ƙareka mama Allah ya bamu alkhairi " Yaya Aliyu ya faɗa yana ƙoƙarin shigewa ɗaki.
Yaya Usman ya ce "Kuma duk abin da ake faɗa a radion babu wanda ki ka riƙe sai wannan?"
Ruma ta ce "To ai akwai wasu ma, mantawa nake yi ne sai yanzu na tuna"
Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Kina jina ko Ruma?"
"Eh ina jinki"
"Yauwwa, zan gaya miki zan miki bayani, amma ba yanzu ba sai an kwana biyu, yanzu ko na yi miki bayani ba zaki gane ba, kuma nan gaba ko ba a gaya miki ba ma, zaki gane da kan ki".
Cike da yarinta ta ce "Nan da kwana biyu ranar asabar kenan, in Allah ya yarda zan tuna miki ki gaya mini"
"Ba wanna kwana biyun nake nufi ba hansai, sai kin ƙara girma da hankali"
Cikin mamaki Ruma ta ce "Yaushe kuma zan ƙara girman da hankali, wancan karon ma fa na taɓa tambayarki menene MATA MAZA, ki ka ce mini sai na girma, na tambayeki menene haila ki ka ce mini ba yanzu ba, amma da zan yi wani abun sai ki ce ina girma amma bana hankali wane irin girma ki ke son nayi to?"
"Ke tashi ki wuce ki kwanta dan uwarki, kawai kin saka mutane a gaba da tambayoyinki na shirme, ko a gidan uban wa ki ke jiyo wannan manyan maganganun oho miki, wuce kan na karya ki biyu, ba zaki tambayi abu daidai da hankalinki ba sai wanda ya fi ƙarfin kanki" sai da ta kalli in da Yake zaune yana bata umarni, bayan da fari yayi kamar bai san me suke yi ba.
A hankali ta tashi ta nufi ɗaki, tana tunanin menene aibun tambayarta?.
Tafiya ta yi ɗaki, ta gyara shimfiɗarta ta kwanta, tana tunanin meyasa kullum tayi tambaya sai ace mata ba yanzu ba sai an kwana biyu, ko ace wai tana tambayoyin da suka fi ƙarfin ƙwaƙwalwarta me hakan yake nufi kenan?. Da wannan tunane-tunanen bacci yayi awon gaba da ita.

YOU ARE READING
ƘANWAR MAZA
RandomLabarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuwa da ƙaddararta, ko wace iri ce ƙaddarar ta ta?