ƘANWAR MAZA 3

2.9K 48 2
                                    

                   ƘANWAR MAZA

      BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Page3

'yan matasan yaran maza sun girmi Rumaisa, kuma duk da haka ƙarfin namiji da na mace ba ɗaya bane ba.
Tana cikin tafiya ta ji ana ke!ke! Ta tsaya waiwaya ta ga da wa ake.

tawagar yara ta gani sun nufota gadan-gadan, tana ganinsu ta san masu dukanta ne, sam bata karaya ba, maimakon ta gudu sai ta durƙusa ta fara kwasar duwatsu, ta shirya duk wanda ya kawo kai, sai ta ƙwale masa kai da dutse.

Amma a haka sai da wasu daga cikin su suka cim mata.

Sani Yayan Habiba, ya na zuwa ya kwarfeta da ƙafarsa ta faɗi ƙasa, wani danƙo ya ɗauko a aljihunsa, ya fara dukanta da shi, duka take kai masa ko ta ina da allonta har ta samu ta tashi tsaye da ƙyar a kan ƙafafuwanta.

Ta yi kukan kura ta kafa masa haƙora a kafaɗarsa, tsananin azabar zafi ya sanya ya kurma wani uban ihu ya ja da baya, dan har ƙashinsa ya ji haƙoram Ruma, sai ka ce mayya.

Ganin ta gigita Sani, wasu daga abokan nasa kuma suna fama da raɗaɗin jifan da suka sha, ya sanya ta durƙusa ta ɗauki takalminta da hijjabinta a hannu, ta tsula da gudun tsiya.
Rufa mata baya yaran suka yi, suna a taro ta, amma kamar walƙiya haka take sheƙa da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba sai da ta kai filin ball ɗin su Yaya Aliyu. Suna tsaka da ball, sai ratsa cikin ƙartin mazan nan take sai gata a tsakiyar filin da maza ke uban gudu suna ball, ta cinma Aliyu a tsakiyar filin ƙwallon ta rirriƙe shi.

Mamaki ne ya kama shi, ganin hijjabinta a hannu, kanta sai hula idanunta duk sun yo waje, tana ta haki tana waige-waige.

Riƙeta yayi yana tanbayarta lafiya? Wasu daga cikin abokansa suma suka tsaya suna tambayarta ko lafiya, amma taƙi magana sai ajiyar zuciya take yi.

Aliyu ya ja ta gefe, ya sanya mata hijjabinta, ya kalleta a tsanake ya ce 'Menene?" Shiru ta yi bata yi magana ba sai sauke numfashi take.

Haushi ne ya fara kama shi ya ce "Dan ubanki menene, me aka yi miki kika biyoni nan cikin maza?" Yayi mata maganar a hasale.

Fara gaya masa abin da ya faru tayi, kuka ya ƙwace mata.
Ɗan shiru yayi sannan ya ce "Amma ina fatan baki yi kukan a gaban yaran ba?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Kin taimaki kanki, dan da kin yi musu kuka wallahi sai na ƙara miki".

Cikin shesheƙa ta ce "Ban yi ba"

Aliyu ya ce "Bari na canza kayana muje, ɗaya bayan ɗaya ki rakani gidajensu sai naci uban yaran nan, dani suke zancen"

Ya zaunar da ita a gefe, aka cigaba da tambayarsa meya sami Rumaisa ya ce musu babu komai, su cigaba da ball ɗin su, shi zai tafi.

Su Sani kuwa tun da Allah ya sanya Ruma ta ɓace musu, suka haƙura da binta, amma suka yi alwashin sai sun kuma saka ranar da zasu naɗa mata duka, dan tayi musu ɓarna sosai.

Suna tafe a hanya, Aliyu ya ce "Ke amma ba a banza zan je rama miki ba, sai idan ki yadda zaki wanke mini kayan ball ɗina da takalmina".

Cikin hanzari ta ce "Eh na yadda, zan wanke maka"
ya ce "To shikenan"

Ya sakata a gaba har ƙofar gidan su Habiba, Aliyu ya aika yaro yace a kira masa Sani.
Sani ya zata a cikin abokansa ne wani yake nemansa, yana ta fama da kafaɗarsa saboda cizon da Rumaisa tayi masa, sai ka ce an sare shi da manjagara a wurin ba haƙorin ɗan Adam ba, ga Habiba ita ma sai kuka take, leɓe yayi suntum ya kusa haɗewa da hancinta, bakin yaƙi rufuwa saboda dukan da ta sha da allo a fuska, sai da bakin ya fashe, banda dukan da ta yi mata a ka da allon, da take jin tamkar an mata rawani da tukunyar ƙarfe saboda nauyin da kanta zuwa fuskarta yayi mata, ba ta iya banbance a wani sashi na fuskarta hancinta da bakinta suke.

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now