3

245 36 5
                                    

*

Akwai abubuwa da yawa dake iya taba zuciya, su yi mata ramin da a wani lokacin zaka nemi abinda zai cike ta ka rasa, kamar misali Takaici, takaici na yadda bamu da ikon canza wasu abubuwan daga muhallinsu zuwa ra'ayinmu a rayuwa, a yau ina takaicin yadda bani da ikon canja mazaunin kalamai da kamshi, da na rarrraba ku zuwa duniyoyi mabanbantan da zasu iya mantar daku matsalolin ku.

Don ba zan kira turarukan Scentmania by Sana da turare kadai ba, duniya ce mai zaman kanta da zata canja akalar tunaninka, ta daga DARAJARKA a idanun duk wanda ya rabe ka... wannan shafin yana dauke da tallan turarukan Scentmania by Sana! Designer oil perfumes ne da suke da kama jiki da kaya, irin wanda kake tafiya ka bar al'umma da mararin kamshinka a guri. (07065525409)

***

Danja ta tsaida motocin da tayoyinsu ke tsere akan titin, a lokaci guda kuwa suka shiga tsayawa bi da bi suna jeruwa cikin layin da zai kai kowannensu ga inda suka nufa, a sannan ne kuma mabaratan dake tsaye tsamo-tsamo daga gefen titin  suka hanzarta wajen bazuwa tsakanin motocin kowanne da kalar bararsa.

"Alhaji Allah ya kare, Alhaji dan ya Rasulullahi ka taimaka min ƴa ta ce bata da lafiya..."

Wata dattijuwa daga cikin mabaratan ta shiga rero tata barar yayin da take bi 1tsakanin motocin, kalamanta na karshe suka fiqto daidai sanda ta tsaya gaban wata shimfidaddiyar farar mota da ta dauki idanunta.

A lokaci guda kuwa mai tukin motar ya juyo daga kokarin danna wayarsa da yake yi ya kalle ta, tana tsaye ne sanye da wani koren hijabi da baiyi kama da tunaninsa ba, amma cikin sakan guda guda tunanin nasa ya dauke shi ya watsa shi baya, zuwa wani lokaci da shekaru suka wuce dashi, fuskar matar ta canja, yanayin kayan jikinta ma suka canja, ta koma mahaifiyarsa sak! sannan a gabanta wani yaro ya baiyana, yaron dake dauke da fuskarsa ta kuruciya.

Kammaninsu a bushe suke sannan idanunsu na dauke da kalolin tashin hankalin da kana kallonsu zaka gane.

"Alhaji dan Allah dan Annabi, Alhaji ka taikama mana, ƴata ce kwance a asibiti bamu dako sisi..."

Muryar mahaifiyar tasa ta wancan lokacin ta cika kunnensa da wannan karyayyen amon da yake iya tunawa, karyayyen amon da shine abu mai karfi da yake iya rikewa tare da ita a yanzu, don dashi ne ta koma ga mahaliccinta, bai sake jin wani abu daga gare ta ba bayan shi...

A idanunsa yaga yadda motar da suke tsaye a gabanta ta wuce su da matsanancin gudu yayin da mahaifiyar tasa tayi saurin kamo shi ta rungume, kamar tana tsoron motar zata iya take shi.

Horn din da yaji daga bayansa ya dawo dashi zuwa zahiri, ya lura danja ta canja an basu hannu har an fara tafiya, kuma duk da gilashin motar akwai tint mai tsananin duhu da baza'a a iya hango na ciki ba, matar nan tana tsaye tana barar kamar ta san yana kallonta ne.

Sai kawai ya yi saurin zuge gilashin yayi mata alama da hannu cewar ta biyo shi sannan ya figi motar zuwa tsallaken danjar, yana ganin mai motar bayansa yana daga hannu cikin masifa sanda ya wuce shi,  bai ko kara kallonsa ba a hankali ya gangara da motar gefen titin ya tsaya.

Ai kuwa yana tsayawar, hayaniyar mabaratan nan ta cika kunnensa kafin ma ya gansu.

"Alhaji a bamu na annabi.... Alhaji Allah ya kiyaye... Alhaji don manzon Allah..."

Maimakon matar da ya kira kusan gabadayansu ne suka rufe shi, kowanne hannunsa akan gilashin motar suna tattabawa. Sai kawai ya bude dashbord din gaban motarsa ya zaro rafar yan dari biyu-biyu sababbi, ya zuge gilashin dake daya kujerar sannan ya shiga rarrabawa kowannensu guda biyu, abinda ya dada rikita su kenan wadanda suka tsaya ta gilashin gefensu suka zagayo daya bangaren a take aka shiga kokawar mika hannu.

Yana jin tasirin addu'o'in da suke masa bayan sun karba da kuma yadda murmushin da suke yi yake kokarin wanke gajiyar da ya debo a yau din, sai a kusan karshe ya tadda matar da ya kira ya sake yi mata alamar  ta tsaya sannan ya karasa sallamar sauran gabadaya.

Darajar Su!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora