GUGUWA BIYU

24 1 0
                                    

GUGUWA BIYU

Aysha D Fulani

BABI NA ƊAYA

            Maɓudi

     بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

A YAYIN DA WASU KE WALWALA, A LOKACIN NE MU KUMA MU KE BIN LUNGU DA SAKO, KWARARO-KWARARO DOMIN NEMAN ABIN SAKAWA A BAKIN SALATI.
WASU SU BAMU DOMIN ALLAH CIKE DA TAUSAYAWA, WASU KUMA SU BAMU SUNA MITA, HANTARA, KYARA TARE DA TSANGWAMA, KAI HAR DA MASU ALLAH WADAI DAMU MA.

KALMOMIN "ALLAZI WAHIDI, A TAIMAKA!". Su ne kalaman da ke tashi a cikkn dandazon al'ummar da ke cuɗanya tare da kaiwa da komowa wajen hada-hadar kasuwanci. Dubannin mutane da cikin kasuwar Ceceniya da ke kan titin Ahmadu Bello a cikin garin Kaduna.

Kalmar "Wahidi" ita ce ke fita daga bakunan yaran da ke riƙe da robobinsu na bara, waɗanda suka kasance ƙanana mabambanta da shekarunsu ke tsakankanin bakwai zuwa goma sha biyar. Ta ɗaya ɓangaren kuma sahun manya ne da za mu iya cewa iyayensu ne haɗe da tsofaffi, wasu daga ciki masu naƙasa wato guragu, makafi, kutare da dai sauransu.
Ta ɗaya ɓangaren kuma daga inda almajiran suke, wasu ne zaune cikin shigar manyan suturu tare da Rawani, alamun da ke nuni da yanayin sarauta kenan daga cikinsu ko ba a sheda maka hakan ba.
         "Ka taimaka mun don Allah!".
   Itace kalmar matshiryar budurwa take faɗi cikin gujin kuka, tsaki yaja ya ciro Naira hamsin ya miƙa mata yana mita. Da mai mutum zaiji daku almajirai da ku ke toshe mana kan  hanyoyinmu ko kuma da tsadar rayuwa, kai  wannan wacce irin masifah ce haka, ya Allah ka kawo mana sauki."
   Yana tuƙi cikin chuɗewar mutane yake mita kan mashin ɗinsa ta roba-roba.
Naira Hamsin din da ya miƙata tai saurin sunkayawa ta ɗauka, jikinta sai bari yake da gudu ta miƙe ta nufi wurin wani mai rogo da kuli. A galabaice ta miƙa mai kudin tana fadin "Don Allah ka taimaka mun da na hamsin". Kada kai gefe ya yi ya amsa kudi ya zobo mata a takarda ya mika mata. Da sauri ta amsa don ji take kamar ƴan hanjinta zasu fito don yunwa ta riga da tagama cinta, hannunta mai mugun datti ta sanya cikin sauri ta dauka ta kai baki.  Karar ciɗar da garin ya saki ne ya sake an karar da mutane halin da garin yake ciki wanda a kowani lokaci ruwa zai  iya sauka, ɗaraɗaran idanuwanta tazubama sararin samaniya bayan ta kai rogon cikin bakinta, sai tauna take da kyar don cikinta wani irin juyawa yake tamkar mai shirin naƙuda.
     Guguwar data taso ce ta hana ta karasa tantance halin da take ciki, batai wata wata ba ta sheƙa a guje cikin wata rufah don samun mafaka kafin ruwan ya sakko.
Gefe guda tai makanta wurin zama tana cigaba da cusa ma cikinta rogon data siya.  Tako ina isake ke tashi cikin ƙankanin lokaci ruwa yafara sauka, rogon dake hannunta shine na karshe cikin karamin bakinta ta cillashi tana shafa cikinta dake ƙugi. Miƙewa tai ta tara hannayenta biyu a bakin wani yagaggen kwano wanda yagaji da duniya, sai zub da ruwa yake, hannu ta saka takai hannunta wurin cikin zuciya tana fadin. Ya Ubangiji Allah ka dube ni a wannan halin da nake ciki, Allah ka sake tsareni da tsarewar ka, Ubangiji wannan ruwa da zansha Allah kasa yai mun maganin wannan ciwon da cikina yake mun, ya Allah kafi kowa sanin halinda na tsinci kaina a ciki Allah ka dube ni  don tsarkin mulkinka. Hannu biyu ta dinga tarawa tana kaiwa bakinta a duk sanda hannunta ya cika, a haka har ta koshi, gyatsar da babu yadda zatai tayi domin kuwa cikinta yai sama alamun yana neman wani abincin.
Gefe ta koma ta zuba ma titin kyakkyawan idon, cikin zuci take saƙa ko mintina biyar ba'ayi ba da ya cike da al'ummar Annabi amma yanzu kowa ya kama kanshi sakamakon sakowar ruwan sama.
     Lumshe ido tai tana jin bacci bacci na neman ɗibarta, jingina tai da bango sosai ta yadda zata ji ɗadin baccin.
    Bacci tai sosai don dama a gajiye take, jin ana shafah mata jiki yasa ta zabure a rikice ta kwallara wani irin kara, rintse ido tai ganin an haske mata ido da wata fitila mai mugun haske, a tsorace tai baya tana jan jikinta waigawa tai cikin sauri tana son sanin inda take.
   Jikinta ne ya fara kyarma ganinta cikin ɗaki saman kanta kuma kattin maza ne har guda uku dukkansu sanye da gajeren wando.
     Addu'a neman tsari ta shiga yi cikin zuciyarta tana ja da baya ganin suna tunkaro ta suna babbaka dariya mai cike da nuni da kya yi kya gama ya sa ta kara tsurewa tana fusgo numfashinta a wahalce, tai baya jin ta jingina da bangone ya sa zuciyarta harbawa da sauri da sauri.
    Kanƙame jikinta tai cike da tsoronsu ta shiga basu hakuri.
    Tsawar da taji an buga mata ne ya  hantar cikinta saurin kaɗawa, rintse ido tai ta sake ƙankame jikinta, hannu ya kai ya fisgota da ƙarfi cikin ƙaraji yake fadin.
     "Dan ubanki kina son jikin naki ki ke bajewa atiti kina bacci, na rantse yau sai na miki ciki sau goma kuma kinga waɗanan duk sai mun haɗu mun yageki  tare dasu duk mu uku zamu haye ki, dama irinku muke nema idan na ƙara jin kin yi koda gyaran murya ne sai na miki abin da ko numfashi bazaki ƙara yi ba a gidan duniya.
    Wani wahalallen miyau ta haɗiya zuba musu ido tai tana hasaso ta inda zata kwaci kanta jin an fige mata ɗankwalinta yasa tai saurin ruƙukume kanta tana sake ambaton Allah.
    Jikin bango ta sake manna jikinta tana sake kare ma ɗakin kallo cikin sa'a ta hango wani karfe nesa da'ita babu ta yanda zata iya daukowa.
    Babban cikinsu ne ya yo kanta ya jawota ya cillata kan yar yaloluwar katifar wandonshi ya soma zamewa ya rage daga shi sai dan ciki, sauranma kwabe nasu suka yo suka nofo kanta ganin bilhakki nema suke su rabadata da mutuncinta ya sa ta kwalla ƙara da iyakar karfinta, saukar marin da taji ne ya sata saurin dafe ƙuncinta.
    A zafafa ya kwabe wandonshi yai zigidir ya cakumo wuyanta tattaro miyon bakinta tai ta tofah mai, wani marin ta sake ji ya da sauri ya cakumeta yana kokarin rabata da kayanta.
    Wani irin wahallalen numfashi take ja idanuwanta sunyi jazir, jikinta sai kyarma yake ganin ƙuriyar ainun sauran ma sun tube haihuwar uwarsu yasa tafara kai mashi duka, baki takai ta gantsara mai cizo a hannun shi ai ko a gigice ya sake ta, karfe dake gefenta ta dauka ta raɗa mai akan Hajiya babba ba tai wata-wata ba ta sake kwala ma ɗayan shima ɗayan yana juyowa ta sauke mai tsabar azaba suke sume a gurin, a gurguje ta dauke ɗankwalinta da hijab ɗinta kudi ta gani kusa da hijab ɗinta ta dauke ta cire sakatar dakin ta fito da sauri tana saka hijabinta.
    Gugu-gudu take gudun kadda su fito su sake kamata, kallan yanayin wurin tai take ta fahimci layin da take, da sauri ta bar cikin layin tai hanyar da zata sadata da masallaci tana zuwa taga har an idar sallar isha'i.
      Jan jikinta tai ta karasa bakin famfo ta saka baki tana zuƙar zuwan da ta kunna da hannunta, wa irin tsawa taji daga bayanta wacce ta saka ta suman tsaye, kyarma jikinta ya soma yi, jin an sake daka mata wata tsawar yasa ta juyo babu shiri.

Comment fisabillilahi

GUGUWA BIYU Where stories live. Discover now