GUGUWA BIYU
Aysha D Fulani
BABI NA UKU
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِAjiyar zuciya ta sauke tana fadin "cikakken sunana shine Aysha don haka naji ana gayamun sai dai abin da ban sani ba shine, ban san wacece Ni ba daga ina nake waye mahaifina, wacece mahaifiyata, su waye ɗangina duk ban sani ba. Abu ɗaya zan iya fadi da rayuwata shine na taso a wani gida cikin wata anguwa mai suna , tun ina karama na taso wurin wata mata mai suna Uwale, a hannunta na taso tun ina karama Ni dai idan a baya aka tambaye Ni zan iya cewa itace uwata wacce tai silar zuwana duniya, sai dai kash ashe duk ba haka bane.
Hakika na taso a wurin Uwale matar na da matuƙar kirki don itace ta raineni tun bayan tsintata da tai a zanin goyo, kin san malam bahaushe yace yaro sai uwarsa. Na taso tabbas tana iya bakin kokarinta wurin kula dani ita da mijinta Uwale na da yara biyar kuma duk mazane sun fara mallakar hankalinsu, hakika Allah ya basu yara, sai dai ba masu jin magana ba ne don babban yaronta yafi kowa rashin ji wallahi tun ina ƙanƙanuwata yake so ya ɓata mun rayuwa hakan yasa na tsane shi, ko hanya banson mu hada Ni dashi, ina da shekara goma ya fara addabar rayuwata idan na fito ya tsareni, haka idan muka hadu cikin gida yai ta cika yana batsewa, idan kuma tsautsayi ya hadani da shi a cikin ɗakin mahaifiyarsa sai nayi kamar zan mai ihu sannan sai kyaleni. Ina girma yana kara nuna mun mugun halinsa hakan yasa hankalina ya sake tashi, a duk sanda na zauna na kanyi kukan da bansan iya adadinsa ba saboda a tunanina idan har shiɗin Yayana ne taya zai dinga mun haka, anane zuciyata tashiga kokonto cewa lallai akwai wani lamari a tsakani don wanda ku ke uwa ɗaya uba ɗaya bazai aikata hakan ba, don hakan jahilcine. Ina da shekara goma sha uku lokacin ina aji biyu na gaba da primary a makarantar gwamnati, inada kokari sosai saboda nike cinye ta ɗaya a jinmu a makarantar muma ta islamiyya nike lashe wannan gurbin. Duk yanda yaronta Ali ya yi dani naki yadda watarana wacce ita ce ranar da ta zama silar rugujewar dukkan farin cikin rayuwata, a duk sanda zan tina da hakan nakanji wata guguwa mai matuƙar karfi ta daki duk wani sansani na faranin ciki na ta ruguza shi, hakika naga tashin hankalin da rai da zuciya sun yi ƙadan wurin hasaso abubuwan da zasu iya riskar bawa a cikin babin rayuwarsa. Hmmmmm ranar Asabar bayan mun taso makaranta ina tafe cikin layin mu, har na karaso gida niƙadai saboda ban cika mu'amula da ƙáwaye ba, ina karaso na iske gidan babu kowa, shiga ɗaki nai na soma cire kayan makaranta, banyi aune ba kawai naji mutum a kaina ihu nafara ina neman zanina in daura amma hakan ya gagara domin ya riga da yaci mun, da karfin Allah na samu na gantsara mai cizo a kunne shine ya gigice yai gefe nikuma na yayimi zanina na fito a guje. Ina kaiwa bakin kyaure gida nai karo da Uwani tana shigowa, a guje nai kanta ina haki tambayata take mai yafaru a galabaice na shiga zayyano mata abubuwan da suke faruwa tundaga lokacin da ya faramun wannan abun.
Riko hannuna tai muka shiga cikin gidan abun mamaki babu kowa, maƙalewa nai kamar gunki don tsabar tsoro da mamakin ina kuma ya yi tambayar da na wurga ma kaina kenan.
"Hmmmm!. itace kalmar da naji daga bakinta Uwani ta saki hannuna tai bayi, kasa shiga ɗakin nai na koma gefe na rakuɓe bata bi takaina ba ta cigaba da aiyukan gabanta Inan zaune har sauran yaran suka dawo daga makaranta. Ganina a gefe ɗaya yasa suka soma tambayar lafiya gyada musu kai nai kawai alamun lafiya, shigowar babban ɗanata yai daidai da dokawar zuciyata wacce ke harbi tamkar zata fito fili.
Kwalamai kira tai ya karaso inda take zaune ya tsaya, a banzace ta dubi inda nake tana fadin "Uban mai kai ma yarinyar chan". Inda nake ya kalla yana fadin "Meko zan mata bayan nima shigowata gidan kenan".
Zayyano mai abin da nagaya mata tashiga yi ai take yafara zagina, ban tsure da maganarsa ba, sai da naji yana fadin "Ai tsintaciyayyar mage bata mage taya idan ta dauke ni a matsayin ɗan uwa zata dinga bina da wannan mugun alkaba'ii, Ni wallahi shiyasa sanda ki ka tsintota naso ki kaita gidan sarki ba ki barta a nan gidaba, ke ɗan ubanki a ina na ganki har nake miki wannan abun munafukar Allah ta'alah wallahi yau sai kibar gidanan ki koma chan ki ne mi iyayenki wa yasani ma ko ɗiyar sheguce aka wurgar a cikin bola".
A ɗuke nake a ƙasa banda luguɗen bugu babu abin da zuciyata keyi, gaba ɗaya kwakwalwata ta chushe wuri ɗaya, maganganusa sun juyamun karamar kwakwalwata, hawayen dake aikin zuba a kasa na saka hannuna na gobe, gyara zaman zanin jikina nayi na miki tsaye jiri na ɗibata, tafiya nake tamkar zan fadi don har yanzu kalmar wama ya asani ma ko ɗiyar shegece ita ke mun yawo adodon kunnena , bugun zuciyata naji yana sake hauhawa tana shiga ta kowani lungu da sako.
A kasa na zube na riko ƙafafuwa Uwale ina gujin kuka nake fadin" Hakika Ni baiwace mai yadda da kaddarar Allah, kadda ki duba ƙanƙantar shekaruna kiyi hakuri ki gayamun gaskiyar abin da yake fadi tabbatacce ne ko kuma ƙage yake mun don Allah".
Saukar kalmomin ta naji tana fadin "Tabbas tsintoki nai cikin bola, bayan nadawo daga anguwa ina tafiya na dinga jin kukan jariri, kasa hakuri nai na nufi inda sautin ke fitowa anan na cikaro dake a cikin kayan jariri masu kyawu da abun ɗauka tsugunawa nai nadauke ki, ina ɗago ki naga damin kudi tare da farar takarda an rubuta* _Duk wanda ya tsinci ta don Allah ya dauki kudinan ya siya mata madara daganan har ta isa yaye daga nan kuma kaima ka daura da naka taimakon don samun lada a taimaka a sanya mata suna Aysha_*. Ai a guje na dauke ki nayo gida ina murna, wannan gidan da kiga ni a cikin shi muke haya a da kenan lokacin dana tsintoki, ina zuwa gida na nuna ma mijina ai murna a gunmu kamar ranar sallah da muka zauna muka kirga kudinan Naira miliyan hadda rabi, bayan mun kamallah na dubu mijima Malam Hashimu, nace mai malam kaga kudinan mu dau miliyan mu sai gida saboda kaga an saka gidanan a kasuwa kuma idan mun tashi bamu da matsuguni, wannan kudi daga Allah ne sauran abin da ya rage sai mu siyaa mata madarar muyi chefene da gyaran gidanan domim murufah ma kanmu asiri, duk wanda ya tambaye Ni ɗiyar waye zance daga gida aka kawomin mahaifiyarta Allah ya amshi abinsa wurin haihuwa kaga babu wanda ya sani bakinmu alaikum. Da murmushi malam ya kalleni yana samun albarka, cikin kwana biyu akai ciniki aka gama abin da muka siya gida dubu ɗari takwas aka siya miki madara da saura kuma muka gyara ko'ina, kafin kice me unguwar mu ta dauka da masu gutsiri motsa kowa da abin da yake cewa da yawa mamaki suke taya muka iya siyan gidanan lokaci guda wai dare ɗaya Allah ya yi Bature.
Ranar da ki ka kwan bakwai Malam ya amshi kudi ya siyo miki rago madaidaici ya yanka miki, aka saka miki suna Aysha na ciga da rainon ki.
Wannan shine iya abin da ya biyo baya, yanzu duk irin hallacin da mukai miki shine zaki ɗinga bin yarona da sharri wallahi kinyi asara kuma na gode da sakkayar da ki kaimun Ni nasan ba halin yarona ba kenan kije ke da Allah kai kuma wuce kaban wuri kar in sake jin bakin ka".
Tunda Uwale ta fara magana hawayen idona suka ƙafe, sai da takai aya, sannan na dago na dubi inda take muryata na rawa na soma magana.
"Kiyi hakuri don Allah domin kece uwata don ke nataso na sani a duniyata hakika bansan dacewa ni din ɗiyar tsintuwace ba mara gata da galihu, wacce uwa da uban suka gwammaci yin nisa da'ita akan su hakura su zauna dani, Kiyi hakuri da abinda na fadi in sha Allah hakan bata sake faruwa ba ki yafe mun domin Allah."
Ganin taki kulani yasa na miƙe ina tangaɗi na isa cikin ɗakinmu zama nai akan yaloluwar katifar dake ɗakin, anan naji wani sabon kuka ya kufce mun mai ratsa zuciyar mai sauraro, kuka nai har sai da naji kaina kamar zai tsage sannan na rarrashe zuciyata, duniyar tunani na fada ina tambayar kai na wani zunubi na aikata wa Uwata ko Ubana ko a halina suka raboni da su, shin ko dai Ni din shegiya ce, toh idan ni din shegiya ce zasu saka wannan uban kudi a cikin zanin goyona. Tambaya babu wacce ban ma kaina ba a karshe sai inga banda amsatar kuma ban da wanda zai bani amsa, haka na rarrashi zuciyata na miƙe na shiga bayi alwala na dauro nazo na zube gaban Ubangiji ina kai kukana akan kar ya kashe ni ba tare da na hadu da zuri'a taba.
Tunda ga ranar da mukai abunan Uwale ta chanzamun idan na gaidata sai taga dama take amsawa, abinci idan nazo karba ɗan ƙadan zata bani a wannan lokacin ta fara nuna mun bambanci na gane cewa lallai Ni din ɗiyar tsintuwace, rayuwa ta sauya komai yai mun zafi, ga jarabar ɗanta wanda ya saka ni gaba sai dai idan bamu hadu ba amma sai ya nemi afka mun da taimakon Ubangiji nake tserewa daga wurin shi.
Anyi abun nan da sati biyu watarana Uwale ta sake fita ina tsaka da wanka kawai naga yaron nata ya afkonmin cikin bayi salati nafara tare da neman taimako gurin Ubangiji Allah. Cikin hukuncin Ubangiji idona yai kan wani katako ɗan madaidaici, yana yowa kaina na zille na dauki katakon na buga mai aiko take jini ya ɓalle a goshin shi a guje na fito ya biyo ni, ina dab da shigewa ɗaki naji faduwar mutum a kasa ina waiwayo naga shine ya fadi hankalina yai ƙololuwar tashi duk tunanina ya mutu. A gaggauce na hada kayana na kwaso kudina naira dubu biyar danake tarawa, na tsallake shine na fito. Kasa bi ta cikin gari nai saboda kadda a zargeni sai ta bayan gari nabi na hau mota, nace ma mai mota ya kawo ni cikin gari tofah shine nayo anan nake bara nake cin abinci, idan dare ya yi kuma in shiga Masallaci in kwanta tun mai gadi na hanani har ya hakura, lura da natsuwa ta yasa ya barni don yaga ban kula maza bare inje inda suke. Baba Halime tai matukar kokari akaina don ita ke jana a jiki har muka saba nake mata aikace-aikace kuma tana ban abinci wanda zai isheni, na nuna mata ina son aikatau wanda za' a dinga bani abinci da wurin kwanciya tare da sanya Ni a makaranta koda islamiyya ne, na tashi da niyyar sallah sai ga Baba Halime ta sanar dani zuwanki, kinji iya kar abin da zan iya gaya miki dan gane da rayuwata".Comment fisabillilahi
YOU ARE READING
GUGUWA BIYU
RomanceMaɓudi بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ A YAYIN DA WASU KE WALWALA, A LOKACIN NE MU KUMA MU KE BIN LUNGU DA SAKO, KWARARO-KWARARO DOMIN NEMAN ABIN SAKAWA A BAKIN SALATI. WASU SU BAMU DOMIN ALLAH CIKE DA TAUSAYAWA, WASU KUMA SU BAMU SUNA...