GUGUWA BIYU

9 1 0
                                    

GUGUWA BIYU*

*Aysha D Fulani*


*BABI NA HUDU*

              
          
     بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

   A jiyar zuciya Hajiya Fadelah ta sauke ta sa hannu ta goge kwallar data zubo mata saboda tausayin Aysha, karya kwana tai tana fadin "Hakika ko wani bawa da irin tasa kaddarar ke kuma irin taki kenan, Ubangiji Allah ya bayyana miki a halinki, amma ina kyautata zaton cewa ba hakanan ƴan uwanki suka yadda ke ba hakika akwai babban lamarin dake faruwa sai dai muyi ta rokon Allah ya nuna mana lokacin da komai zai bayyana, yanzu zamuje gidanan zan baki ɗaki mai dauke  da ɓandaki kuma in sha Allah zan saka ki makaranta kuma zanyi iya kar yina in riƙe ki tsakani da Allah don Allah kema ki riƙe alkawari kuma ni mijina ba mazauni bane duk sanda ya dawo zan zayyane mai komai a kanki ko kuma kafin yazo ma, abin da nake so komai zaki tarar a gidana tsakanin ki da shi ido don Allah.
"Babu komai in sha Allah zan kiyaye duk abin da ki ka cemun."

Bakin wani katafaren gida ta faka motarta cikin anguwar da kana gani kasan ta masu ƙasa ce wato masu hannu da shuni, Anguwar Rimi a bakin get ɗin gidan ta sai ta hancin motar ta, ta  dannan hon, a guje mai gadi ya sheko ya bude get din gidan wanda fitilu suka haske ta ko'ina, shiga cikin babban gidan sukai wanda yaji adon furanni masu kyau da daukar ido.
Kashe motar Hajiya Fadilah tai ta sauka daga ciki, itama Aysha ta sauko ta bi bayan ta duk inda ta saka kafa nan take saka tata, ɗan mukuli ta saka ta buɗe kofar falo, kutsa kai tai bakinta dauke da addu'a.
     Sakin baki Aysha tai lokacin da tai tozali da kyakkyawan falon wanda ya more kayan alatu masu kyau da ɗaukar ido.
Ganin Hajiya Fadilah ta buɗe wata kofah yasa Aysha chakarewa a wurin don a tunaninta ɗakinta ne, hakan nema yasa ta ja da baya ta nemi wuri ta zauna.
"Kinga nan shine ɗakin naki wannan kuma bayi ne". Hajiya Fadilah ke fadi a lokacin tana kokarin waigowa ganin babu kowa ya sa ta saki karamin tsaki ta sake fitowa. Hango Aysha tai zaune ta saki baki sai kallon ƙwayeyen wutar falo take tana dariya, Murmushi mai sauti Hajiya Fadilah tayi ganin yadda Aysha ke kallon ƙwayeyen wutar tamkar taga wani zinari.
     "Taso Hajiya kizo in nuna miki ɗakin naki kinga lokacin sallah na gabatowa".
         A kunya ce ta mike ta biyo bayanta cike da mamaki take kallon ɗakin wai nata ne wannan duk ita ka dai,lumshe ido tai tana ma Allah godiya da yai mata chanji cikin lokaci da babu zato balle tsanmmani. Zubewa tai a kasa ta riƙo kafar Hajiya tana zazzago godiya, girgiza kai Hajiya tai tana fadin "Taso kiga bayi kiyi alwalah bari naje ɗakina na dauko miki wata riga kafin gobe muje in miki siyayyar kayan sawa".
Miƙewa tai ta leka ban ɗakin  tana kallon yadda Hajiya ke nuna mata komai na baɗan ɗaki, bayan fitar Hajiya Aysha ta daga ido tana sake kallon ko'ina godiya tai ma Ubangiji da ya azurta da haduwa da mata mai matukar kirki haka.  Mike tai ta dauro alwalah ta dauko sallaya ta gabatar da sallar isha'i , abincin da Hajiya ta ajiye mata ta dauka, shinkafah ce da miya sai gefe kuma soyayyen naman kaza guda biyu manya sai ruwan gora da lemon gora.
Tun kan ta kai baka yawunta ke tsinkewa ta hadiye miyau yafi sau miliyan, miƙe tai da sauri ta sake wanko hannunta ta soma cin abincin hannu baka hannu kwarya. Sai da taga ta shafe kwanon abincin tas sannan tai gyatsa ta kora da ruwa mai sanyi wanda ya sanyaya mata zuciya.
Tattara kayan tai ta fito falo anan ta iske Hajiya na zaune itama ta kamallah sallar isha'i, tsugunawa tai har kasa tace "Ina zan kai kayan?".
Dariya tai tace "Ince dai  ko kin koshi da kyau, don naga kamar akwai yunwa a tattare dake, idan  baki koshi ba ki gayamun domin Ni din na dauke ki matsayin ɗiyata ke kuma ki dauke ni matsayin uwa a gare ki, don Allah kema ki dauka hakan".
"Na koshi sosai Hajiya wallahi cikina har yai mun katoto, yanzu inane madafah in ajiye wannan so nake in samu in chaza kayan jikina, naga rigarar da ki ka kawo mun tai kyau Nagode sosai Ubangiji Allah ya bada lada Allah kuma ya linka miki nikin baninki abin da ki kayi mun, Ubangiji ya baki gidan aljanna na gode matuƙa".
"Babu komai Aysha tashi ga madafar chan ki a jiye kwanukan zuwa safiya sai na karasa nuna miki sauran wuraren, Kiyi wanka ki samu ki kwanta don akwai gajiya a tattare dake so nima zan shiga daga ciki, don yau kwatata ban zauna ba sai yanzu  ina so in huta".
"Miƙewa Aysha tai tana fadin Allah ya tashe mu lafiya na gode sosai".
Hanyar kicin ta nufah tana yaba matukar kirkin Hajiya Fadilah a zuciyar ta tambayar kanta take anya kuwa akwai ragowar irin waƴanan mutane a duniya, ba su sanka ba su dauko ka su mai da aka jikinsu lallai a jijina ma Hajiya. Shiga ciki zuciyarta na zayyano mata bayanai iri-iri, baki ta sake gefe ta ajiye zancen da zuciyar ta ke mata a gefe, tana kare ma kicin ɗin da  hasken fitilu ya ƙawatashi, zaman dirshan tayi tana kallon komai na wurin gudun kadda ta taɓa ta lalata wani abun ya sa ta tsayar da hannunta amma baɗon hakan ba da sai ta taɓa komai na wurin don ta samu salamar zuciya da waƴanan kayan masu kama da na aljanna wanda ake basu labari a islamiyya.
Zumbur tai ta miƙe gudun kadda Hajiya taga dadewarta yasa ta ajiye kayan a wurin ta fito ta janyo kofar, ganin babu kowa a babban falo ya sa tai saurin shigewa cikin ɗakin da mugun gudu ta fada kan gadon tana juye tana tsalle.
   "Wayyo Allah na na gode maka bisa wannan ni'ima da kai mun Allah na gode". Juyi take tana abaton Allah tana mai godiya ta kalli nan ta juya ta kalli chan wani irin dadi take ji tamkar ance taga a halinta.
Miƙewa  tai da sauri rigar da aka bata ta dauko da sauri tana kallo, rigah ce mai ruwan madara wacce akai ma ado da duwatsu farare, a jiyewa tai tana yaba kyan rigar da sauri ta shiga bayi sannu a hankali ta dinga bin komai tana bin bayanin da Hajiya tai mata, wanka ta sillo tana ta shafah jikinta don ji tai ko'ina na santsi, gaban madubi ta dire kanta tana kare ma halittar ta kallo, dariya ta saka tana lakato kumatunta mayukan dake wurin ta dinga bi tana karanta sunayensu, guda ɗaya ta dauko ta mutseke jikinta dashi lumshe ido tai jin ƙamshin man na ratsa ko'ina na wurin. Lungu da sako haka tabi jikinta sannan ta sanya ma idonta kwalli, hoda ta dauko zata shafa, ta mayar ta ajiye tana fadin a tsohon darenan wazan ma kwaliyar salan in kwanta Aljannu su dinga kallona, dariya tai ta dauko rigar da aka bata da hijabi ta zubama kayan ido tana kallo, a jiye rigar tayi ta dauki hijab din ta zura tana kallon yadda ya fito da kyawun fuskar ta a ciki. Kan gado ta hau ta kashe filitar ɗakin ta karaton addu'ar bacci ta janyo bargo ta kwanta.

Bangaren Baba Halime kuwa tunda sukar bar gidan take murna da kudin da Hajiya ta bata, Mijinta na shigowa ta sanar mai Dubanta ya yi cike da mamaki yace "Halima a wannan zamanin ki ke irin wannan lallai Toh wallahi babu ruwana taya zaki dauki yarinya da baki san  daga inda ta fito ba ki baiwa mata kamar wannan, yanzu idan wani abu ya biyo baya ba. Baki san yarinyar nan ba bakisan su waye iyayenta ba kin dauke ta daga ganinta a tati ki duba yarinya budurwa kamar wannan a kallah zata kai shekara sha biyar amma ace tana yawo a tati a gaskiya bakiyi ma kanki abu mai kyau kuma wallahi ni babu ruwana da duk abin da ya biyo baya".
Sosai hankalin Baba Halime ya tashi da zance mijinta Malam Audu sam batai tunani irin wannan ba ita kawai tsananin tausayin Aysha yasa ta taimaka mata, muskutawa tai gefe tana gyara zama ta dubi mijin nata dubanshi tai da kyau tana soma magana "Kayi hakuri da farko nai kuskure da ban sanar maka ba, amma abun da ya sa nai haka shine sai da na tambayi yarinya tai mun bayanin yadda rayuwar ta taso, wallahi malam duba nai da cewa idan ɗiyata ce ta fada wannan iftilan ya zanyi ka duba kagani batasan uwarta ba bare ubanta bare kuma wani daga cikin ɗanginta in Sha Allah babu wani abu da zai faru da izinin Ubangiji".
"Allah ya sa haka don komai yaje ya dawo wallahi babu hannuna a ciki kin dai ji ko".
Miƙewa ya yi ya shige daki ya barta zaune ta zuba hannu bibbiyu tai tagumi, tunanin yadda rayuwa tai tsada take yanzu idan Aysha ta aikata wani abu wanda ba dai dai ba ya zatayi kenan, hannu ta ɗaga sama ta karanto ma Ubangiji kokenta akan ya hani Aysha da aikata wani abu wanda zai sa ayi Allah wa dai da'ita.
Kirar sallah asuba wanda ya ke dauke sanyi mai sanyaya baccin duk wani bil'adama, juyi take kiran sallah na ratsa kunnenta burinta ta katse baccin datake amma hakan na neman gagararta don tana jin gardin bacci, bakinta dauke da salati ta miƙe na addu'ar tashi daga bacci sannu a hankali ta buɗe ido tana addu'ar kadda Allah yasa wannan kyakkyawan dakin da take gani ya zama mafarki.
Jin kiran sunanta yasa ta zabura ta mike tana fadin "Ganinan na tashi".
Miƙewa tai da sauri ta shiga banɗaki wanke baki tai ta dauro alwalah, sallah ta gabatar ta duba dakin ganin babu Alkur'ani ya sa ta miƙe ta nufi falo, gefen Hajiya ta tsguna ta gaidata, cike da fara'a ta amsa tana tambayar ta ya takwana, tabbatar mata da lafiya ta tai sannan ta tambayeta Alkur'ani domin ta samu tai karatu.
Dariya Hajiya tai ta nuna mata ma'ajiyar kur'anai  "Gasu chan ki dauka ki a jiye a dakin ki, duk sanda zakiyi karatu sai kiyi anfani dashi idan kin kamallah ki same ni a madafah domin in nuna muki yadda abubuwa suke".
Godiya tai ta miƙe ta nufi inda kur'anen suke ta dauki kwaya ɗaya, ta koma daki karatu tai sosai sannan ta rufe ta ajiye, miƙe tai ta shiga bayi tai wanka sannan ta dawo ta shirya cikin kaya da Hajiya ta bata jiya gaban madubi ta koma ta shafah fauda sama'sama sannan ta daura kwalli a kwayar idonta da man baki, fes ta fito, kitson kanta ta kallah taga ko tsagar ba'a gani kauda kai gefe tai alamun ya bata kyama. Jiyowa tai ta sake kallonta a madubin daura dankwalin tai da niyyar tana gama aikin gidan zata zo ta warware kanta ta wanke da man wankin gashin data gani a cikin bayi.
Fitowa tai ta nufi madafah a tsaye ta tarar da Hajiya ta wanke kayan ciki na rago, cikin kankanin lokaci Hajiya ta nuna mata yadda ake anfani da na'urorin wurin, farfesu suka shirya sai soyayyen dankali da kwai da ruwan shayi.
Suna kamlawa ta fito makeken hoton dake jikin bango ta zuba ma ido, namijine ƙyakyyawa tagefensa kuma mace mai matukar kama dashi, dafah shi tai suna murmushi aka ɗauki hoton, shagala tai da kallonsu don sun matukar birgeta jin an dafata tai firgigi.


Comment fisabillilahi

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 01 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GUGUWA BIYU Where stories live. Discover now