*MATAN ZAMANI*
*NA*
*SHAMSIYYA MANGA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*
*BISSIMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
*BOOK1*
*Page 1*
_____________________________________Hawaye ne masu zafi suka shiga kwaranyowa ta kumatunta, wani irin zafi take ji hade da raɗaɗi yana tasowa daga ƙasan ranta. Kodayake hakan ba sabon abu ba ne kusan ya zamar mata jiki a duk lokacin da take zaune ita kaɗai ba ta da wani aiki da ya wuce ta ɗauki hoton Sambo ta kafe shi da ido tana kuka tana jin ina ma ta zama silar tseratar da rayuwar Sambo daga rugujewa amma ina! Ƙaddarar Ubangiji ba ta canza wa yadda ya tsara ta haka take kasancewa.
Ya daɗe a tsaye a bakin ƙofar tangamemen falon na su yana ƙare mata kallo, tausayin ta yake ji ganin irin halin da ta shiga ga shi babu ta yadda za a yi a dawo da hannun agogo baya da tunin ya murza ya dawo da shi ko dan wanzuwar farincikin Shareefa, Allah ya sani wani irin so yake yi wa Shareefa marar misaltuwa to amma kash baƙon al'amarin da ya gifta shi ya zama shamaki ko ya ce katanga wajen katangesu daga samun cikar burinsa.
A hankali ya taka har ya isa inda take zaune sannan ya sa hannu ya karɓi hoton Sambo da yake hannunta, jajayen idanuwanta ta ɗago ta kafe shi da su ba tare da ta ce komai ba har zuwa sannan kuma hawaye ba su daina kwaranyo wa daga cikin idanuwanta ba.
"Ki shirya Dr Abbas ya dawo za mu je ya ganki, kuma kin san yau ne date line ɗin da aka ba mu na follow up ɗin ki"
Abin da kawai ya iya ce mata ke nan kafin ya juya ya fice.
Da ƙyar ta iya tashi sannan ta nufi ɗakinta kasancewar ta yi wanka hijab kawai ta sanya sannan ta ɗauki wayarta ta fice. A kallo ɗaya idan ka mata za ka ce lafiyyaya ce babu abin da yake damunta sai dai mai ɗaki shi kaɗai ya san inda yake masa yoyo kamar yadda Allah kaɗai ya san karatun kurma.A harabar gidan ta tarar da Mansur tsaye yana jiranta ba ta mishi magana ba sai buɗe motar da ta yi kawai ta shige sannan suka fice daga cikin gidan.
*Wasu shekaru baya kaɗan* *Daura Katsina state*
Gida ne Babba mai haɗe da manyan sashuna daban-daban wanda za mu iya ƙiran gidan da gidan gandu, duba da yanayin irin gini da tsarin gidan domin a ƙalla akwai sashuna kusan guda ashirin a cikin gidan, hakan ne ma ya sa mutanen unguwar suke yi wa gidan laƙabi da *GIDAN YAWA* ko *LUNGUN YUYUYU* . Ginin gidan ba ginin zamani ba ne ƙofa ɗaya gare shi gidan sai dai a ciki akwai ƙofofi mabanbanta sannan akwai waɗanda aka ƙawata su da ginin zamani duba da cewar a cikin yaran gidan akwai wayyayu. Mazauna gidan sun kasance gabaɗayansu zuri'a guda ne domin kuwa asali ma ƴaƴan mutum ɗaya ne.
Wannan gidan shi ne gidan Malam Babba mai goro, shi ne asalin sunan mai gidan wanda ya kasance sana'ar goro ita ce sana'ar shi hakan ya sanya rabi da kwatar ƴaƴan shi suka gajeshi inda suma suke sana'ar goron. Yaran Malam Babba mai goro guda arba'in da uku cif, guda ashirin da bakwai sune waɗanda iyayen su su ke gidan, sauran yaran kuma duk ya rabu da iyayen su kasancewar shi mai auri saki. Matan shi guda huɗu ne cif a yanzu haka ma. Matar shi ta farko sunanta Baba Uwani wadda suke ƙira da Baba, yaranta guda Tara a cikin gidan huɗu mata biyar maza, Ƙasim shine Babba sai mai bi mishi Lukuman,sai na ukun Rasheed,sai Lawan,sai Mansur. Sai matan su ne; Aina'u, Shukriyya,Mardiyya, sai kuma Shareefa ita ce autar su. Sai Adda Zara wadda suke cewa Adda ita ce matar shi ta biyu ita kuma tana da yara Bakwai Uku duka maza,Khalil,Babangida, Murtala, sai mata huɗu, Balkisu,Shamsiyya,Lubabatu,Hafiza. Sai matar shi ta Uku mai suna Hansai ita kuma yaranta guda biyar duka Maza Jabir,Habibu, Isyaku,Aliyu,Sadi kuma har yanzu tana haihuwa yanzu haka ma ciki gareta, sai ta huɗu mai ƴaƴa Uku duka mata Zulai,Huwaila, A'ishah. wadda ita ce amarya sunanta Zuwaira suna ƙiranta da Baba Zuwai.