MATAN ZAMANI 002

2 0 0
                                    

*MATAN ZAMANI*
     
        *NA*

*SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA GA YAYANA ABDALLAH HASSAN YARIMA*.

*BOOK 1*

        *02*
_____________________________________

"Ah Babe ya ka tashi za ka tafi ba ka ce komai ba?".

Kallonta Shaheed yayi sannan ya ce.

"To mai kike so na ce?".

"Babe Ina so so nake ka sayamun kaga auren Lubabatu daman ya zo to kuma kasan kaf gidan mu dai nice nayi Sa'a na auri miji mai dukiya to kaga ai ya kamata a ce na fita daban daga cikin ƴanuwana ko ba komai suma zasu gane akwai bambanci".

"Wai kina nufin sarƙar miliyan ɗayan zan siya miki ko kina nufin material ɗin dubu ɗari biyar ɗin zan siyamiki?".

Shaheed ya faɗa yana Zaro ido waje alamar mamaki.

"To meye a ciki Babe abun da nasan cewa ka fi ƙarfin shi kam ai ba zan ji shayi ba wajen cewa ka siyamin tunda nasan ko fiye da hakane zaka siya".

Shukriyya ta faɗa tana wani fari da ido tare da cuno baki gaba alamar shagwaɓa.

"Tabbas ina tsammanin ƙwaƙwalwarki ta samu damuwa to bari ki ji bana ƙarya don a soni don haka ban miki wannan ƙaryar ba, idan za ki ɗauki kayan ki na cikin akwati ki ɗinka gwanda tun wuri ma ki ɗinka dan nikam ba wani kaya da zan sake siyamiki".

Yana kaiwa nan a maganar shi ya shige cikin ɗaki ya bar Shukriyya sake da baki.

"Kan uban can mai Shaheed yake nufi? Daga yin aure ko shekara ba a rufa ba har ya fara nuna gazawarsa wajen biya mini buƙatuna na yau da kullum. To na rantse da Allah ba zata saɓu ba bindiga a ruwa ko ka so ko ka ƙi sai ka siyi kayan nan in ba haka ba kuwa zaka sha mamaki dan na rantse sai kasan ka auro ƴar GIDAN YAWA".

Tashi tayi da sauri ta bi bayanshi tare da shiga ɗakin da ya shiga ɗin haɗe da banko ƙofar.

"Shaheed mai kake nufi? Ya za a yi na ce ina son abu kuma ka ce ba zaka yi ba alhalin kana da kuɗin yi, bayan haka ma auren ƙanwata za a yi uwa ɗaya uba ɗaya idan har baka mun ba gidan uban wa zan je ya min?".

Ta ƙarashe maganar tana sakin wani huci kamar wadda ta yi gudun tsere.

"Fice mun daga ɗaki".

Ya faɗa yana nuna mata ƙofar ficewa daga cikin ɗakin lokaci guda ya haɗe rai.

Duk da cewa ta ɗan tsorata da yanayin nashi hakan bai sa ta ji zuciyarta ta karaya ba ko ta nuna mishi cewar ta tsorata dan wallahi ta ƙudurta a ranta cewar a daren nan ba zata bar ɗakin ba har sai ya amince zai bata kuɗin kayan.

"Na rantse da wanda ya halliceni ba zan fita ba har sai ka amince zaka ban kuɗin kayan nan idan kuwa ba haka ba wallahi daga ni har kai ba mai rintsawa a cikin gidan nan tunda ni zaka nunawa tijara".

Ta ƙarashe maganar tana riƙe kunkumi.

"Shukriyya ki fita ki bar cikin ɗakin nan tun muna ganin juna da mutunci tun kafin kuma ki ƙarasa kaini bango domin kuwa za ki sa na miki abin da ba ki yi zato ba".

"Na faɗa bazan fita ba, kai a tunaninka har akwai wani abu da za ka mini wanda ban yi zato ba, ai kuma ka gama shayar da ni mamaki wallahi Shahed kar nake kallonka, babu wani sabon abu kuma da ya rage".

Tasowa yayi gadan-gadan ya nufo ta ita kuwa ko gizau bata yiba domin zuciyarta ta gama ƙeƙashewa ba alamar tsoro a cikinta.

Shikuwa Shaheed yana isowa inda take ya finciketa da ƙarfi yayi hanyar fita daga cikin ɗakin da ita duk da irin tirjewar da take hakan bai sanyashi ya dakata da fitar da ita daga cikin ɗakin ba.

MATAN ZAMANIWhere stories live. Discover now