MATAN ZAMANI 004

6 1 0
                                    

*MATAN ZAMANI*

            *NA*

*SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*Bissimillahir Rahmani Rahim*

*BOOK 1*

*Page 04*
____________________________________
         
      *Police station*

A office ɗin DPO su Shareefa suka yada zango sai aikawa juna harara suke tsakanin su da su Lantee gayu.

Bayan duk sun nemi waje sun gama daidaituwa ne DPO ya dube su ɗaya bayan ɗaya ya fara magana.

"To da farko dai na saurari bayanai daga kowane ɓangare inda kuma dama haka dokar mu take matuƙar aka kawo mana mutane biyu masu laifi ko sun yi faɗa ko sun yi sata ko dai wani abu,to abu na farko da muke fara yi shine mu saurari bayani daga bakin kowanne daga cikin su wanda muke ƙiran shi Statement kafin mu yanke hukunci. To daga bayanin da muka saurara mun gano cewa wadda ake ƙara itace mai laifi saboda ta taka taje har gida ta yiwa yaro duka wanda hakan ya janyo ta mishi lahani. Dan haka a bisa adalci irin na hukuma da farko ƴan uwan Shareefa zaku biya ƴan uwan Mubarak watau shi yaron da aka ji wa ciwo adadin kuɗaɗen da suka kashe wajen siya mishi maganganuwa. Sannan hukuma zata yi kokarin ganin ta shiga tsakanin ku domin ko gaba ba ma fatan irin haka ta sake faruwa a tsakanin ku. Bayan haka Shareefa zaki bawa ƴan uwan Mubarak haƙuri bisa abun da k...".

"Kaga Malam DPO kake ko wa? Don Allah ka tafi kai tsaye kan abin da kake son cewa na gaji da sauraron dogon bayanin nan,dan haka sanar dani abun da kake so ayi a dunƙule".

DPO ɗin ya tsinkayi Muryar Shareefa kamar dirar aradu a tsakar kan shi. Cike da mamaki ya ke bin ta da kallo domin kuwa har ga Allah shi lamarin yarinyar mamaki ya fara ba shi rashin tsoron ta ya daina ba shi mamaki sai tsoro ma da ya fara ba shi anya kuwa wannan yarinyar ita kaɗai ce ba aljanu a kan ta.

"Ke marar kunya ki iya bakin ki ko yanzu na ladabtar da ke".

Cewar wani kurtun ɗan sanda yana muzurai.

Ko kallo bai ishi Shareefa ba balle ta ba shi amsa.

Malam Babba ne ya dubi mahaifiyar su Lantee gayu yace.

"Talatu nawa ne kuɗin da ku ka kashe ɗin?".

"Naira dubu goma ne ba yawa".

Talatu ta faɗa tana ƙara cokaro ɗaurin ɗan kwali gaban goshi irin na ƴan duniyar nan ga cingom kuma a bakin ta.

"Dubu goma sai ka ce abin sata! to na rantse da Allah dubu ɗaya ita zan iya bayarwa idan kunga dama ku karɓa idan kunga dama kar ku karɓa".

Malam Babba mai goro ya faɗa tare da zaro wata cukurkuɗaɗiyyar naira dubu a aljihun shi sannan ya ajiye wa Talatu a gaban ta.

Wani ƙundumemen ashar Talatu ta maka sannan ta buga teburin gaban DPO tare da buga rantsuwar cewar wallahi ba zata karɓi dubu ɗaya ba, hauka ake yi.

Nan fa shima Malam Babba mai goro ya rantse cewar shima ba zai ƙara ko sisi ba.

Kan ka ce kwabo musu ya ƙara ɓarkewa a tsakanin su kowa ya dage akan abun da yake faɗa.

Duk yadda DPO ya so ya sasanta su lamarin ya faskara domin kuwa yana ganin abin kamar wasa sai ga shi abin yana so ya fi ƙarfin shi. Da ƙyar Lawan ya ce zai ƙara dubu ɗaya idan sun ga dama su ƙarɓa idan sunga dama su bar kuɗin. Haka DPO yana ji yana gani ya shiga bawa Talatu da su Lantee gayu haƙuri lura da yayi cewar su Malam Babba mai goro da gaske suke.

Ita kuwa Talatu cewa tayi zata karɓa amma wallahi su kwana da sanin cewa ko kallon banza ƴan gidan su Shareefa suka sake yiwa yaranta to wallahi kotu ce zata shiga tsakanin su.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 24 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAN ZAMANIWhere stories live. Discover now