*MATAN ZAMANI*
*NA*
*SHAMSIYYA MANGA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*
*BOOK 1*
*Page 03*
______________________________Nan fa Zainab ta cigaba da magana ta inda take shiga ba ta nan take fita ba baƙaƙen maganganu kuwa haka ta dinga ruwan su ba tare da ta ware kowa a cikin gidan ba.
"Ke dalla Malama kin ishi mutane, wa ya damu dake? Wa ya damu da kayan ki? Da har zai ɗauka to wallahi tun wuri ki je ki nemi wanda ya ɗaukar miki kaya a waje amma ba a cikin gidan nan ba dan na lura idan ba a taka miki burki ba rashin kunyar taki kan kowa zai iya hawa a cikin gidan nan".
Baba Uwani ta daka mata tsawa tana galla mata harara.
"Baba ni fa a cikin gidan nan aka ɗaukar min kaya sannan duk wani abu da kika ga ina yi da hujja nake yinsa, dan haka ai ita wadda ta ɗauki kayan ta sani kuma ta san da ita nake to wallahi tun wuri tun kafin na tonawa mata asiri ta yi gaggawar zuwa ta mayar min da kayana".
Zainab ta ƙarashe maganar tana ƙara turo ɗaurin kwali gaba irin ba mutuncin nan.
"To ke da kinsan wanda ya ɗaukar miki kaya amma shi ne za ki tsaya kina mana kumfar baki a cikin gidan ai sai ki nemi koma waye ku yita ta ƙare".
Cewar Baba Zuwai tana janyo ruwa a cikin rijiya.
Ita kuwa Hansai kaɗa kai kawai ta yi ta nufi hanyar ɗakinta domin kuwa ita ko a cikin matan gidan ma ita ce ba ta fiya magana ba sannan ba ta fiya shiga sha'anin kowa ba tana da kama kanta sosai sai dai kuma idan mutum ya taɓata to bata da daɗi fa.
Tun da Zainab ta fara magana Hafsa ta dinga jin zuciyarta tana wani irin matsanancin bugu duk da cewa ta san ba ita ta ɗaukarwa Zainab kaya ba amma haka kawai ta ji ta tsargu da kanta duba da irin kallon da Zainab ɗin take watsa mata mai cike da tuhuma.
"Ni fa bana son tozarta mutum ne shi ya sa nake so cikin salama a fito mini da kayana tun maƙwafta ma ba su ji mu ba"
"Ke Zainab dakata wai mai kike nufi ne? Na ga sai wani kallona kike kina maganganu kin san dai wallahi ban gaji sata a gidanmu ba don haka ba zan fara a kan ki ba to ki kama kan ki can ki je ki nemi wanda ya ɗaukar miki kaya"
Hafsa ta faɗa tana ƙarasa shanya kayan da ta gama ɗaurayewa.
"Ni dai ai ban ambaci suna ba amma daman shi marar gaskiya ko a ruwa sai ya yi gumi kuma shi abin da yake cikin duhu ai ba kowa ya fiye ganinsa ba sai an haska, don haka ai ba zai ya bi ɗan kuturu ba har sai an ga ya girma da yatsunsa"
"E lallai biri ya yi kama da mutum to kawai Zainab fito fili ki ce ni kike zargi na daukar miki kaya"
Har Zainab ta buɗe baki za ta ce wani abu sai Hafsa ta katseta.
"Zainab ki shiga ɗakina ki duba idan kin ga kayanki ki ɗauka idan kuma har ba ki samu kayan ki ba 'yan gidan nan ku zama shaidu na rantse da Allah sai na rufe Zainab a ɗaki na ci mai cin uwarta wallahi"
"A'a duk abin bai kai haka ba, ku bari a samu masalaha mana"
"Baba Uwani barta ta je ta duba kayanta ai ba za a tabbatar da gaskiyar mutum ba sai an duba an gani ba"
Zainab ta faɗa tana bin bayan Hafsa da ta nufi ƙofarta.
Suma sauran matan gidan biyo bayansu suka yi aka zo bakin ƙofar Hafsa aka yi cirko cirko.
Kai tsaye Zainab tana shiga ɗakin Hafsa ta fara bincika kayanta duk inda ta san za ta ga kayanta ta duba amma ko mai kalar kayanta ba ta gani ba, juyawa ta yi da niyyar barin ɗakin ai da mugun gudu Hafsa ta sha gabanta tana cewa.