9

349 31 4
                                    

Dakyar ya samu Yusrah ta biyoshi dayan dakin dake can cikin part dinshi wanda babu kawayenta da yan uwanta a ciki. Sai kumburi take tana daure mashi fuska wai ta dizga ta gaban abokanshi. Dan saida yama daya daga cikin kawayenta magana kafin suka lallabata ta biyoshi. Yana rufe kofar dakin ya juyo yaga ta tsaya da hannayenta saman kirjinta sai daure fuska take.

"Haba mana Babe, wai ba na baki hakuri ba dan Allah?" Ya furta cikin sigar lallashi yana karasowa inda take tsaye. Hannyenshi duka biyun yasa ya janyota zuwa jikinshi yana kwantar da kanshi saman kafadarta. "Babe kiyi hakuri mana, kinji?" ya furta da muryar rada can cikin kunnenta.

Duk kuwa da cewar Yusrah fushi takeyi dashi sosai, hakan bai hana ta dan lafe jikinshi ba jin yanda ya rungumeta da kuma yanda yake mata magana can kasa kasa cikin kunnuwanta. Bata fuska tayi tana harararshi. "Ai wallahi ka bani mamaki sosai. Na fada maka Sam is my bestfriend and shine ka ciwa friend dinshi mutunci ko? A kan yar aiki? Har kana mishi ihu ya fita daga cikin gidanku. You didn't just embarass Alex, Babe, ni ka kunyatar wallahi."

Kara matsota yayi zuwa jikinshi ya dan sumbaci kefen wuyanta da yake a bude, wanda yin hakan saida yasa Yusrah ta dan runtse idanunta tana shakar daddadan kamshin da yake fita daga jikinshi. "Ba wai dan saboda me aiki nayi hakan ba. Mu fa musulmai ne, Babe. Kuma ga mutane dayawa and kowa ya rike waya yana daukar abunda ke faruwa. So kike aje social media ana magana ace muna molesting househelps dinmu? It will be very bad kema kin sani, ko?" Cikin rada yake mata maganar ganin yanda take kara narkewa a cikin jikinshi.

Shiru tayi bata kulashi ba shi kuwa sai kara lallabata yakeyi dan soyayya sosai yake yiwa Yusrah. Duk kuwa da cewar bawai shi yanta tun farko yaji yana santa ba, Maama da Mummy wadda ta kasance mahaifiyarta sune suka hadasu. Daga farko bai dauka zaiso Yusrah amma haka kawai daga baya ya tsinci kanshi cikin matsananciyar kaunarta. Wasu abubuwan da yake mata shi kanshi mamakinsu yakeyi.

Juyowa tayi tana kallonshi cikin ido da wani kalar murmushi alamar ta hakura. "Bazan hakura ba har sai ka yarda muna zuwa Abuja zamuyi hosting dinsu for either lunch or dinner. Sam yace man zai danyi touring around the country sai nan da two weeks zai koma US."

Har a ranshi baiso ba. Dan shi bai tashi da tarbiyar wai mace kuma matar aure ace tana abota da wani katon ba. Kuma katon ma kafiri. Amma yanzu da yake lallashinta yakeso yayi kuma da yayi tunanin idan Sam din ya koma US yaushe zai kara dawowa? Sai ya daga mata kai yana murmushi ita kuma ta sarkafo hannayenta ta wuyanshi tana dan janyo fuskarshi zuwa gareta.

"Thanks for being my wife," Khalil ya furta a hankali yana dora bakinshi saman nata tare da lumshe ido saboda wata kalar natsuwa data saukar mashi a lokaci daya.

Basuji karar shigowar mutum ba saidai sukaji karar faduwar abu. Basu rude ba wai sun raba jiki dan kuwa sunsan ba haramun suka aikata ba. Hannayen Ysurah suna kan kafadunshi suka juya a tare suna kallon Batul dake rawar jiki wajen tattara abincin data zubar a kasa sanadiyar ganinsu da tayi a cikin wannan yanayin.

Cikin wani kalar yanayi na fushi Yusrah ta karasa har gaban Batul dake duke tana tattara abincin da hannunta duk kuwa da cewar yana da zafi gashi yana kona mata hannu amma ta kasa dakowa ta kallesu.

"Me hakan ke nufi, malama? Ko kuwa abunda ya faru dazu yasa kike tunanin kema kin kai da har zaki fadowa mutuwa yanda kikeso ba tare da sallama ko kwankwasa kofa ba?!" Yusrah ta furta a murya cike da masifa dan ita Allah ya sani tun ganin data mata na farko kawai taji ta tsani Batul tsana kuma mai tsanani bama tare da tasan dalili ba. Abunda ya faru dazu kawai ya kara wutar abun ne.

"Kuyi hakuri. Nakai abinci sauran dakunan ne akace nazo nan na kawo akwai mutane. Banyi tunanin kune ciki ba..." Ta karasa maganar tana yarfe hannu dan ta debo wajen miyar gashi zafi rau har ya dan so ya kona ta.

K'abila...Where stories live. Discover now