GIDAN ƊAN LITI PAGE 3

39 4 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/CrMx3WgRaeUGK1ekcnIlty

*HANWA! Ƙungiya ce da ta barranta kanta da marubutan batsa, masu yin lahani ga tarbiyyar ƴaƴan Hausawa, wannan ƙungiya ta HANWA ta ƙudiri aniyar samar da ingantattu kuma tsaftatattun littattafai da za su zama abun karantawa a cikin al'umma. Muna fatan Allah ya kawo mana ƙarshen marubuta masu ɓata tarbiyya da koya ba mummunar ɗabi'a ta cikin rubunsu, waɗanda ke  ɓatawa marubuta littattafan Hausa suna a idon jama'a.*

HANTSI WRITERS ASSOCIATION
(HANWA)








*GIDAN ƊAN LITI*







RUBUTAWA: HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH)




*PAGE 3:*



Wata iriyar kwalliya suka tsara wadda duk wanda ya kalle su sai ya qara, dan kuwa daga Mommy har Billy suna da kyawun sura sai kuma suka ƙara da wanka ga wayewa da iya gayu,duk wanda ya kalle su bai san daga wanne gari suke ba zai iya rantsuwa da su ɗin ba 'yan asalin qauyen Ba mugu bane zuwa suka yi daga birni.

Tafe suke suna rausaya kamar wasu furanni a lambu, sai latsa waya suke yi suna hotuna a Snapchat tare da videos, a haka suka isa gidan Sarki, da sallama suka shiga gidan kamar gidan iyayen su, su na shiga suka yi arba da uwar gidan Sarkin mai suna Iya Laminde wadda ta na ganin su ta washe baki tare da fad'in,

"Ah ah ahhhh kanawan dabo ne yau a gidan namu? Lale maraba da 'ya ta, jiya na gama zancen ki a gidan nan da Umman yara, na ce 'ya ta ta shekara ɗaya da watanni ban sanya ta a idanu na ba,ashe ki na tafe yau"

"Iyyy Innah Laminde ina nan tafe yau,kin kira 'yar halal sai gata ta bayyana a gaban ki, Ina yini Innata? Ya gida ya iyali ya Baba Sarki da fatan ya na nan lafiya bai sake cin daɗi ya taso da ciwon sugar ɗin nashi ba ko? Na zo masa da magani ai daga birni ya zo ya sha ko Allah ya sa a dace"

D'aki Iya Laminde ta wuce su Billisious na bin ta a baya, su na shiga sai na ga ashe parlour ne wawakeke mai ɗauke da kayan more rayuwa kala-kala kamar ba a qauye ba, gefe kuma ga wata qofa nan da za ta Sada ka da asalin bedroom ɗin mamallakiyar d'akin, waje suka samu suka zube a cikin kujerun dake zagaye da tsakar palourn, Billy ta sanya hannu a cikin jakar ta ta d'akko maganin masu ciwon sugar da ta siyo wa Sarki wanda yake mijin yayar mahaifiyar ta k'wali ɗaya ta miqa wa Iya Laminde,

"Allah dai ya yi miki albarka Billyn Lamindedeee, ki na taya ni kula da ɗan tsohon miji na baki ko gajiya, yanzu dai fata na Allah ya sa ya sha maganin nan, saboda kin ga Abdussaboor ma da ya kawo masa daga can Abujar qin sha ya yi, wai a bar shi da tafasar shi da cabbage da garahunin sa ya fi gane musu,"

"Ohhh Baba Sarki da gargajiya 5&6 ne ai, Allah ya sa to ya sha wannan ɗin dan ya na da kyau, Hajiyar da nake wa aiki da shi take amfani,kuma ya karɓe ta sosai"

"To Ameen dai, ya qanwata kin ɗauke min hankali ban ko tambaye ta ba, ina fatan dai ta na nan lafiya da sauran 'yan uwan naki?"

"Ahhh alhamdulillahi ta na nan lafiya tace ma a gaishe ki sosai, kowa ma na lafiya qlou,Innah Laminde yaushe Yah Abdul zai dawo gida zai jima kuwa?"

"Ai be jima da komawa ba kun yi sab'ani, kin san injiniya a Koda yaushe ana bukatar shi a kusa musamman a irin kamfanin da yake aiki shi yasa ya na zuwa kwanan shi biyu ya koma"

Jiki a sanyaye Billy ta ce,

"Ayyaaa ! ba rabon mu gana wannan karon ma,Allah ya kaimu wani lokacin in da rai ai da rabo,ya kamata dai a bani sabuwar lambar wayar shi dan watarana muna shiga Abuja da uwar d'aki na idan na yi mata rakiya ita da mijin ta, kin ga idan na je ba sai na nemi ɗan uwana mu gaisa ba nima?"

"Hummmm Allah ya sa ya ɗauki wayar taki kar ki zo ki na min k'orafi irin na wancan karon,"

"Ameen dai, kin san shi ɗin ɗan ra'ayi ne,"

GIDAN ƊAN LITIWhere stories live. Discover now