GIDAN ƊAN LITI PAGE 10

34 6 0
                                    

HANTSI WRITERS ASSOCIATION (HANWA)











GIDAN ƊAN LITI









PAGE 10:









"Mommy ki natsu ki kalli dai-dai inda zaki ajiye ƙafar ki kawai kar ki kalli sama, ke yanzu a haka zaki waye ki na tsoron bene fisabillahi? Meye a cikin hawa bene sai kace wata wadda zata taka girgije?"

Cikin rawar murya da jiki Mommy ta qanqame hannayen Billy gabaki d'ayan su ta ce,

"Ba zaki gane ba ne billy ji nake yi kamar ana waina ni,riqe ni kar ki sake ni, ni da za ku taimake ni ko a d'akin mai gadin gidan nan ku ajiye ni bana son wannan d'akin da sai na yi cinikin rayuwa ta na hau shi"

A haka suna surutu har suka sauka Mommy bata san ma an sauka ba, ganin ta sauka lafiya ne ya sanya ta sakin wata ajiyar zuciya mai qarfin gaske sannan ta fashe da dariyar farin ciki ta ce,

"Ashe ma ba wani wahala,"

"To dama in ba dan ke ba ma meye a hawa bene dan Allah? Yanzu dole ne mu koma ki sake gwadawa,saboda bana so ki hasala Hajiya ta gaji da shirmen ki ta yi maki korar kare, gidan nan ya ajiye 'yammata iri na da irin ki sun fi goma wasu sun samu nasara a irin rayuwar da muke yi har sun jawo wasu a jiki suma sun zama wasu, wasu kuma wauta da rashin rabo da qauyanci irin naki yasa ba aje ko ina da su ba aka rabu rayuwar su ta yi munin da ta fi ta kare, dan haka ki maida hankali ki zama k'wararriya akan abinda ki ke yi ta haka ne zaki yi ta samun ci gaba har ki jawo wasu kema kamar yanda na jawo ki ni kuma Hajiyata ta jawo ni wannan harkar"

(Ci gaban mai haqon rijiya kenan)

Duk abinda Billy ke faɗa yana shigewa cikin kan mommy kuma ta gamsu da bayanan ta dan haka cikin rawar jiki ta kama qarfen benen ta sake gwada hawa, idanun ta na zubar da hawayen tsoro bakin ta ɗauke da kiraye kirayen sunayen duk wanda take ganin zai zo ya kawo mata agaji a wannan yanayi da take ciki,dan kuwa hatta da sunan Ameerah sai da ta kirawo a wannan yanayin, takaicin ta kuwa kamar ya kashe Billy, gajiya tayi da tsayuwa ta samu kujera ta zauna ta fakaici idanun Mommy ta kunna camera ta na yi mata video amma ta boye fuskar ta,ta na gamawa kuwa ta yi posting a account ɗin ta na TikTok, dama ta rasa content ɗin da zata yi creating ta yi posting a ranar,nan da nan kuwa mutane suka hau gani ana yin comments kala-kala da likes, ta na nan zaune sai sheqa dariya take yi har Mommy ta yi sakkowa ta qarshe, a wannan lokacin kuwa ta na jin ta wasai ba wata fargaba balle tashin hankali dan kuwa ta gano hawan benen ba wani kayan gabas bane ba, tana sakkowa kuwa tace da Billy,

"Ashe ma ba wani wahala hawa da saukar,da fari na tsorata ne kawai,yanzu kuwa ina jin ko wanda yafi wannan laulayawa ma ina iya hawan shi"

"Good muje ko?"

Makullin mota Billy ta zara guda ɗaya a inda suke ajiye makullayen motocin gidan suka buɗe qofa suka fita harabar gidan cike da yanga,wajen motar da za su hau suka nufa Mommy na biye tana kallon ikon Allah,bata gama tsinkewa da lamarin Billy ba sai da taga ta shiga motar ta kunna ta da kan ta sannan ta buɗe wa Mommy gefen direba ta yi mata izinin shiga, a rikice Mommy ta kalli Billy da ke toshe idanun ta da wani baqin gilashi ga kid'a na tashi cikin hauragiyar yaren mutanen kudu, da qarfi Mommy ta d'aga murya tace,

"Billy yaushe ki ka iya mota? Billy lamarin ki na nema ya fi qarfi na fa? Kar kai na ya kunce"

Wani shu'umin murmushi Billy ta saki sannan ta ce,

"Dan Allah ki shigo kina b'ata mana lokaci, akwai abubuwan da baki sani ba da yawa game da ni,amma a hankali lokaci zai bayyana maki su,fata na ki rage wannan qauyancin da kike yi dan zai jawo maki raini a gaba a irin wannan duniyar tamu,ina fatan kin gane?"

GIDAN ƊAN LITIWhere stories live. Discover now