GIDAN ƊAN LITI PAGE 21

60 5 2
                                    

GIDAN ƊAN LITI





HANTSI WRITERS ASSOCIATION
(HANWA)



RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH






PAGE 21:


"Billy na shiga uku Number bawan Allahn nan bata tafiya, ita kan ta 'yar iskar yarinyar ta kashe wayar ta ba a samun ta, daga taje ta yi weekend shikenan sai ta b'ata shiru kamar an aiki bawa garin su?"

Murmushi Billy ta yi cikin ran ta tana fatan ace wani mugun abun ne ma ya samu Mommy kar ta dawo, dan tinda take harkar nan babu wanda ya taɓa bada million uku nan take akan ta balle wuri na gugar wuri har millon biyar se dai a ba wa sauran yaran da suka yi zama tare, kafin ta haɗa million biyar sai ta sha yawo wajen qatti da mata,duk qarya take zubawa mommy dama akan samun kuɗin da take yi dan ta aminta da harkar sosai, se gashi ya tabbata ta shiga da qafar dama bugu ɗaya ta samu million biyar zuwait, cikin yaqe tace,

"Hajiyata don't stress yourself out akan wannan lamarin, ke fa ki ka faɗa min bama kamfanin ki na gyaran jiki kika kirawo aka yi mata gyara ba, kamfanin uwar Daba ki ka kirawo, matar da a kullum itace madubin ki kamar yanda kike madubi na, kin kuwa san ta sha gyara dole Alhajin ya riqe ta,"

"Kuma da wannan ma fa, to amma me yasa ba za su bar waya a kunne ba idan an kira a same su? "

"Kar ki damu, yanzu se ki fara quraje a fuska ki b'ata skin ɗin ki,"

Wata qara me cike da yanga Hajiya K'waisa ta saki sannan ya hau shafa fuskar shi ya na wani karairaya yace,

"Hakane kuma fa, bari na kwantar da hankali na shi ɗan bariki duk inda yaje dole gida zai dawo tinda shi ya sa kan shi a harkar,amma kuwa duk sanda mutumin nan ya dawo da ita se na ɗauke duk wani nauyin shi da nake ji na cinye masa guntun mutuncin shi da ya rage a ido na, sannan kuma dole ya qara kuɗi akan wanda ya bayar dan ba qaramar mace na aika masa ba, yarinya full option double engine? Ke baki ga yanda ta haɗu bane Billy na san da kin ganta sai aljanun kan ki sun tashi kin ja yarinyar mutane d'aki, hahaiiiii ragassss, zo zo na nuna miki hotunan da sa a yi mata ba tare da ta ma sani ba,"

Nan take wani irin qunci ya qara kama Billy, da dikkan alamu dai Mommy na neman kwace mata fada a wajen K'waisa,in kuwa haka ne lallai mommy ta zama 'yar yankan baya, kwana nawa ta yi da tafiyar har ta samu wajen zama a gun Hajiya K'waisa? Jiki babu k'wari ta matsa kusa da Hajiyan shi kuwa ya hau nuna mata hotunan Mommy har waɗanda aka yi mata tana cikin kwamin wanka ba tare da ta sani ba, da shi Hajiyan ke so ta yi amfani wajen yaudaro babban ɗan siyasan da take so ta haɗa ta da shi, wajen kuwa da ake shafa mata mai a jikin ta babu kaya video ta sa aka yi mata, wani yawu Billy ta had'iya dan ganin yanda Mommy ta kere ta a komai da komai,nan take zufa ta fara karyo mata na wani mixed emotions da take ji game da videon, hassada, baqin ciki, kwad'ayi da so da qaunar kasancewa da mommy, sannan uwa uba k'yashi da jin dama ita ce ke da jiki irin na mommyn.

Kallon ta Hajiya K'waisa tayi taga yanda Billy ta gigice, dariyar mugunta ya saki har da buga qafa sannan ya daki kafad'ar Billy yace,

"Wani kaya sai amale, ramin kura kuwa sai 'ya'yanta, wannan ita ake kira da cib'iri nannagi babban kaya,ba abinda zan ce miki sai godiya,kar kuma ki damu babu mai k'wace matsayin ki a waje na har abada, ke fa 'yar amana ta ce,kin manta faɗi tashin da muka yi tare? Kin manta irin taimakon da kema kika bani a rayuwa? Ai ba zan taɓa juya miki baya ba,kar ki ji komai wai mace ta mari mijin ta, tace kar ka ji komai duk a cikin so ne,"

Nan da nan Billy ta ji zuciyar ta ta wanke da kaso mafi tsoka daga baqin cikin dake addabar zuciyar ta, sannan ta wani bangaren ta cika fal da mamakin yanda aka yi wannan karon Hajiyar ta gano yanda take hassada da Mommy, kafad'ar ta ta ji an dafa Hajiya K'waisa tace,

GIDAN ƊAN LITIWhere stories live. Discover now