*RUWA BIYU...*
*Page 1*
_Python joint_
Ƙayataccen wurin shaƙatawa ne wadda yake haɗa jiga-jigan da suka amsa sunansu a nahiyar ƙasar nan.
Matashiyar budurwa na hango wacce a ƙalla ba zata haura shekara ashirin da biyar zuwa da bakwai ba. Sanye take da doguwar rigar abaya ta sake gyalen ba tare da ta naɗa shi a kanta ba, hakan ne ya bani daman hango gashin da ke kwance a kanta, wanda ya sha man gashi da gani ba sai an faɗa ba. Fuskarta ɗaure yake idan ka ganta ba zaka taɓa cewa tana dariya ba, duk da idonta na sanye da baƙin glass Wanda ya hana gano a yanayin da take.
Shishan da ke hannunta, ta kai bakinta ta zuƙa da ƙarfi ta fesar da hayaƙin ba tare da an ɗauki lokaci mai tsawo ba hayaƙi ya turniƙe wajen gabaɗaya har baka iya ganin fuskarta, ga wanda bai saba da hayaƙin nan ba na tabbatar ba zai iya zama a kusa da ita ba, amma ita ko a jikinta zuƙar Allah tsine uwar mai ƙarya take wa hayaƙin, tana fesarwa hannunta ɗaya kuma tana danna wayarta ƙirar Samsung.
Ƙaran buga teburin da ke gabanta ne ya sa ta ɗago a wulaƙance dan ganin wani mai ƙarfin halin ne zai zo har wajen da take ya yi mata haka. Tsawon rayuwarta da take zuwa python ta huta ba'a taba dosan wajen da take ba sai yau, ganin gender ta ne ba wani gardi ba yasa ta cigaba da abun da take yi ba tare a ta ɗago ba.
"Excuse me Please! Can i seat?" ta jeho mata tambaya. Ganin ko zata shekara tana tsaye ba kulata Anaconda zata yi ba ne yasa ta sake samun ƙarfin guiwa, da mamakinta sai ta ji ta amsa mata.
"Why not" ta faɗa ba tare da ta sake kallonta ba.Kujerar dake ajiye a gefe ta jawo ta zauna, shiru tayi na ƴan mintuna saboda tunanin ta yanda zata fara.
"Ba tayi ne?" Ta sake jeho ma Anaconda tambaya.
Miƙa mata shishan tayi still bata sake magana ba.
"Am just kidding you ba sha zan yi ba. Dama wata magana ce da Ni idan kin bani dama".
"Ok go ahead ina jin ki".
"Aiki nake so ki mun, saboda a labarin ki da aka bani na tabbatar ke ce kaɗai wacce zaki iya mun abun da nake so ba tare da an samu matsala ba..."
"Hey! Hey!! Wait.." ta katse ta da sauri.
"Kuma aka ce miki ni zaki nema? Tabbas wanda ya faɗa miki haka ya yaudare ki saboda haka excuse me".
Tashi tayi ta tattare wayoyinta da wallet din ta cikin sauri ta bar wajen saboda ita kanta bata yarda da kanta ba, ta yaya za'a yi ta yarda da wacce ta gani a cikin daren nan, ta yiwu ma wani setup din aka haɗa mata wanda zai sa ta rufta ba tare da ta kawo hakan a lissafinta ba. Tana shiga motarta ta bawa motar wuta.
Nadiya da ke zaune kuwa wani irin smile ɗin jindaɗi ta sake saboda ta yarda yanda aka faɗa mata nan ta zo saboda gabaɗaya abun da aka faɗa mata akan Anaconda ta gan shi. Dama an ce mata muddin ta yarda ta deal din at once to ba ita bace an saɓa lamba, da sauri ta tashi tana mai jin annashuwa a ranta ta tabbatar burinta ya kusa cika tunda har ta ga Anaconda a wannan karon bayan dogon lokacin da ta ɗeba tana nemanta ido rufe ba tare da ta samu daman ganinta ko da sau ɗaya bane. A haka ta shiga motarta ita ma ta tafi tana jin ranta tamkar yau take sallah.
Tuƙi take tamkar zata tashi sama, sai da ta tabbatar tayi nesa da Python ta samu waje tayi parking a gefen hanya wayarta ta ɗauko tayi dialing wani number sai ga *BESTIE* ya bayyana cikin manya harrufa ringing daya biyu aka ɗauka.
"Hello bestie kina ina?"
Scorpion da ke kwance ta ga kiran aminiyarta da sauri ta tashi saboda ganin dare ya yi tunda ta kira ta a daidai wannan lokacin ta san ba lafiya ba dole akwai wani muhimmin abun.
Tashi tayi ta gyara kwanciyarta tace "Ina gida bestie me ya faru?"
"Ki zo gidana yanzu dan Allah akwai maganar da zamu yi yanzun nan.
Duba time Scorpion tayi ta ga har pass eleven. Sheik na nan ta tabbatar har wasu daga cikin masu ɗaukan karatu a ajensa basu riga sun tafi ba.
Tashi tayi ta ɗauki jalbab ɗinta ta zura duk da sleeping dress ne iya gwuiwa a jikinta.
Waya kawai ta ɗauka da key ɗin motarta ta fita.
Gefe da wajen da tayi parking ɗin motarta kaɗan sheik ke karatu har ta wuce ta ji ya kirata cak ta tsaya.
"A'isha ina zaki ke a cikin daren nan?"
"Abba fitan gaggawa ne ya kamani na san ba zan daɗe ba duk runtsi zuwa 1 zan dawo".
Maganar da ta faɗa ba sabon magana bane a wajen sa har ma da wanda suke daukar karatun saboda babu wanda bai san abin da A'isha take yi ba a bayyane ganin ƴar iska suke yi mata wacce ta gagari kowa. Idan ma har ba wanda ya sani ba ko za'a shekara ana faɗa maka ƴar sheik ce ba zaka taba yarda ba. Saboda zaren ba kalan yadin ba ne.
Girgiza kai kawai Sheik ya yi yace "Allah ya shirya", daga hakan bai kuma cewa komai ba ya cigaba da karatunsa duk da acikin zuciyarsa yana jin haushi mummunar halin da A'isha take yi a matsayinsa na malami wanda mutane suke ganin mutuncin sa amma ace ƴar sa ta mace ta fi ƙarfinsa kuma ba yanda ya iya, duk yanda ya so ya ɗauki hakan a matsayin jarabawa ya kasa, wani lokacin abun yana ci masa rai.
Motarta ta shiga ta bashi wuta mai gadi na ganin haka ya buɗe da sauri.
#Anaconda
#scorpion
#er sheik_FARIDA MUSA (SWEERY)_
_FARIDA MAFARA (RED)_Babyn Mahma🤍❤️
YOU ARE READING
RUWA BIYU
RandomRUWA BIYU Rayuwa wasu Matasa guda biyu dasuka Aminta da Juna wanda suka maida kansu Ruwa biyu, ka siya daya kasamu daya kuauta!