RUWA BIYU! 3

5 0 0
                                    

*RUWA BIYU...*

Na

_FARIDA MUSA (SWEERY)_
DA
_FARIDA MAFARA (RED)_

*Page 3*

A zafafe ya juyo ganin Sheik ne riƙe da hannun yasa jikinsa yin sanyi. Bai kai ga sake wani yunƙuri ba sheik ya fara magana.
"Har kullum ina faɗa maka kana tausasa zuciyarka akan A'isha baka ga ko mu da muka haifeta muna yi mata uzuri ba? To kai ma ya zama dole kana yi mata! Ke kuma ki shiga ciki".

Tunda ya fara magana magajin sheik bai ce komai ba, yana gani A'isha ta wuce ciki babu halin ya yi mata shegen dukan da ya yi niyya.

Tana shiga ɗaki ta faɗa gado, a cikin mintuna biyu bacci ya yi awon gaba da ita, saboda bata da wani damuwar da zai dame ta balle ya hanata bacci.

Washegari  tun da wuri Virus ya gama bincikensa. A tracing Kiran wayar da ya yi ne ya san cewa Alhaji Naira zai je wani Mall sayayya, sanar da Anaconda komai ya yi kafin ita ma ta sanar da Scorpion saboda ta zama cikin shiri a wajen suke so su fara ɗana masa tarko.

4:15 daidai tayi wa Scorpion a harabar Mall ɗin tare da Virus suka je amma ya tsaya a mota bai fito ba.

Itama zama tayi a cikin motar har sai da ta hango Alhajin ta cikin glass ɗin mota, Yana sauƙowa a lifter ta fito cikin shigar ta na kamala kaman yadda ta saba.

Giftawar ta kaɗai ya gani ya ji ta tsaya masa a rai duk da bai taɓa jin haka akan ko wacce mace ba, wannan ne dalilin da yasa ya ji ba zai iya haƙura ta wuce ba tare da ya ƙulla wani alaƙa da ita ba, ita ce irin macen da ya daɗe yana nema, mace mai kamun kai wacce zai yi komai da ita ba tare da wani ya sani ba, a ganin farko ya gane ya samu duk abun da yake so a wajenta.

"Audu ka bi wannan matar da ta wuce yanzu ka bata complementary card ɗina kace ta Kira ni". Miƙa masa katin ya yi. Da sauri ya fita ya bi bayan Scorpion.

"Ranki shi daɗe" bata yi mamakin jin maganar ba saboda tasan tabbas Alhajin nan zai bi ta, ba lallai ya iya tsallake irin kallon da tayi masa ba.

Cak ta tsaya ba tare da ta juya ba, ta gabanta ya juyo ya ce "dama boss ne yace na kawo miki card ɗin sa wai ki kira shi a kwai maganar da zaku yi da shi, kuma mai muhimmanci ne".
Yanayin yanda ya yi maganar ne zai gwada maka yana girmama ogan nasa sosai.

Karbar card ɗin kawai tayi bata ce masa komai ba ta cigaba da tafiyarta.

Jiki a sanyaye ya dawo "Boss ta karɓa fa amma bata ce komai ba".

Murmushin nasara Alhaji Naira ya yi yace "karka damu tunda ta karɓa na tabbatar zata kira, ja mota mu tafi".

A cikin kwana biyu shaƙuwa ce sosai ta shiga tsakanin Alhaji da Scorpion, a halin yanzu sosai yake bukatar keɓewa da ita na sirri. Wannan ne dalilin da yasa ya buƙace su haɗu a hotel.

Kai tsaye Scorpion ta karɓi buƙatarshi a ranar suka yanke lokacin da zasu haɗu da kuma time.

Shilfa suite babban hotel ne da duk wanda ya san shi yasan mashahuran masu kuɗi ne suke zama a wajen saboda majority ɗin su suna da ɗaki basa da wani matsala kai tsaye zasu je ba tare da wani damuwa ba.

Karfe huɗu zasu haɗu amma tun biyu Virus yake ciki saboda Scorpion ba zata taɓa shiga wajen ba har sai ya tabbatar da babu wani matsala dan gudun samun akasi basa taɓa bari lissafi ya ƙwabe musu.

"Zaki iya zuwa na gama duk abun da zan yi the place is safe" shine saƙon da ya tura mata. A ɓangaren ta dama ta gama shirinta shi kaɗai take jira.

Ko da ta shiga hotel ɗin sai da ta tsaya a reception ta tambayi room 302 suka kwatanta mata kafin ta shiga.

Tana zuwa bakin kofar ta fara knocking izinin shiga ya bata, ta shige ciki kai tsaye zaune ta same shi a bakin gado yana danna system hakan ne ya bata damar cire niƙab ɗinta ta ajiye a gefe kafin ta cire jalbab ɗin.

Yana ganin hakan ya tashi domin ya yi welcoming ɗin ta, already Virus ya bincika musu dama Alhaji mai kuɗi mayen mata ne mussaman wanda yake tunanin virgin ce, saboda ya fi buƙatar ya lalata mace da kansa shiyasa ko nawa ne zai iya kashe wa mace muddin zata bashi kanta.

"Welcome! Welcome!! Welcome!! Baby" hugging ɗin ta ya yi fuskarsa cike da murmushi ita ɗin ma hakan take a gefen ta, zata iya yin komai da na miji amma ban da sex Bata taɓa yi ba kuma bata fatan tayi saboda ba layinta ba ne.

"Me zaki ci ayi order?" Ta tsinkayi Muryarsa a sama.

Kawo abinci yana cikin target ɗin saboda ta haka ne kaɗai virus zai samu damar shigowa ɗakin. Bata jin yunwa amma ya zama dole ta ce a kawo.

"Just special chips" ta faɗa a takaice.

Waya ya kira ya sanar musu da abun da zasu kawo masa.

A can gefe ɗaya kuma virus ya hango waiter Wanda zai kai musu abinci hakan ne ya bashi daman haurawa sama da sauri ya tsayar da shi.

Cewa ya yi, ya  ba shi Kayan abincin zai miƙa wa boss.

Da mamaki waitern ke kallonsa saboda a iya sanin shi bai san shi ba.
"Waye kai?" Ya tambaye shi. "Ni yaron Boss ne hasalima ban cika zuwa nan ba shi yasa ba zaka Sanni ba amma yanzu ma dan na ga shiga zan yi shi ya sa na zaɓi na sauƙaƙa maka".

Sake fuska ya yi dan jin abun da Virus ya faɗa masa ba tare da tunanin komai ba ya miƙa masa tray ɗin shi kuma ya juyo dama akwai aiyuka a gaban shi da yawa.

  Yana karɓa ya shiga resting room ɗin su Ya canja kaya yasaka irin na waiters ɗin hotel ɗin. Saboda kar Alhaji mai kuɗi ya gane shi ba ma'aikacin wajen ba ne yasa ya yi haka.

Ya yi ɗakin da suke kai tsaye. Ko da ya yi knocking Scorpion ce ta tambaye wanene jin waiter ne yasa ta ce ya shigo, yana shiga ya tarar da Alhajin yana waya, tsayawa ya yi a gefensa bayan ya ajiye tray ɗin akan ɗan stool ɗin da ke gefe da Alhajin.

Idon Alhajin ya faƙa ya maƙala ƙaramin recorder mai kama da botil ɗin riga a jikin hannun ƙofar ɗakin ta yanda zai ɗaukar masa duk abun da ke faruwa a cikin ɗakin yana gamawa ya yi signa ma Scorpion ta gyrara zamanta gami da sake ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya.

"Lafiya kuwa?" Alhaji ya tambaye shi bayan ya gama wayan.

"E list ɗin Bill ɗin ka na kawo maka" ya bashi amsa. Duk wanda yake zuwa manyan hotels yasan irin hakan yana faruwa.

"Nawa ne kuɗin ku?"
"20k ne". Ciro kudin ya yi ya miƙa masa ya karba ya fita.

"Nayi duk abun da ya kamata nayi saura ya rage na ki, Idan har kin ga da akwai wani matsala ki kirani ko kiyi mun text ina ƙasa ina jiran fitowar ku" wannan shine text ɗin da Virus ya tura ma Scorpion.

Toilet alhaji ya shiga watsa ruwa, a wannan lokacin ne ta yi text wa virus akan ya kawo brief case ɗin da suka zo da shi saboda su samu damar canjawa saboda ya buɗe a gabanta ta gani dollars ne a ciki.

Ko da ya zo sai da ya nemi excuse ta je ta bude daga toilet ɗin Alhaji ya yanko mata magana "waye a wajen?"

"Waiter ne na ce a kawo mun cofee ne" ta bashi amsa gabanta na bugawa saboda gudun kar ya kama su.

"Ok" abun da ya faɗa kenan ya cigaba da wankansa, brief case ɗin Alhajin ta canja ta ajiye masa na su bayan sun setting password din da ya saka ta koma ta zauna tamkar babu abun da ya faru.

Mamaki ne ya kashe ta bayan ya fito daga wanka naked ya tunƙare ta yana kashe ido tamkar tsohon kwarto.

Ba tare da ta ankara ba kawai ta ji sauƙan shi a kanta sosai ya danne ta ya fara kissing ɗin ta.






Babyn Mahma

RUWA BIYU Where stories live. Discover now