*RUWA BIYU...*
Na
_FARIDA MUSA (SWEERY)_
DA
_FARIDA MAFARA (RED)_*Page 2*
A 360 ta hau kan titi ta sake kiɗa a motar ta ƙure volume, ta rufe tinted glass ɗin motar.
Buɗe gaban motar tayi ta ciro sigari ta kunna, sosai take zuƙar sigarin cikin ƙwarewa tana bin waƙar gwanja na War! tana rawa da kanta hannunta ɗaya kuma tana tuƙi da shi.
A haka ta isa har gidan Anaconder horn biyu ta yi mai gadi ya buɗe mata gate ɗin, rage glass ɗin motar tayi.
Mai gadi na ganin ta ya washe bakinsa cikin farin ciki ya fara yi mata magana tun kafin tayi masa kaman yanda ko yaro yasan mai yi masa duk wasu halayyar Scorpion da ke bayyane hakan bai hanata girmama wanda ya girme ta ba gami da yi musu ihsani tana da mugun wayo ta iya zama da kowa duk wanda zata zauna da shi ba zata taɓa bari ya faɗi aibunta ba ko da kuwa ƙwaya ɗaya ne.
"Barka da dare Hajiya" ya faɗa fuskarsa a sake.
"Barka dai baba ya aiki?"
"Alhamdulillah" gaban motarta ta buɗe ta ciro kuɗi masu yawa ta bashi tace ya sha ruwa ba ta jira jin godiyar da yake yi mata ba ta ja motarta zuwa cikin gidan gefe da motar Anaconda tayi parking ta fito, sai a lokacin ta wurgar da guntun sigarin da ta gama sha ta saka kafarta ta take shi sannan ta ciro turare ta fesa a jikinta, ta kuma feshe motar da shi. Lemon mint da Bata rabuwa da shi a koyaushe ta ɗauko guda ɗaya ta buɗe kana ta jefa shi a bakinta.
Kai tsaye bedroom ɗin Anaconda ta shiga zaune ta same ta tana sheƙar cocaine tamkar zararriya haka ta dawo idanuwanta duk sun ƙanƙance.
Jin an turo ƙofar ne yasa ta ɗauko da idanuwanta ta suka canja launi ta kalli scorpion, wani lallausar murmushi ta sake mata . Cire jalbab ɗin da ke jikinta tayi ta wurga akan gadon ɗakin.
Waje ta nema kusa da ita ta zauna, ido cikin ido suka kalli juna ba tare da kowa yace ƙala ba. Scorpion ce ta katse shirun da yin magana.
"Bestie lafiya kuwa? You look so worry what's going on?"
"Akwai matsala ta" faɗa mata kai tsaye.
"Go ahead am all ears".
"Boss ya kira ni ya shaida mun akwai wani mutumin da yake so ya kawo mana tsaiko a cikin lamarin kasuwanci wanda ya dawo dole mu san yanda zamu yi mu kawar da shi na ɗan Lokaci".
Wani irin dariya scorpion ta sake ta ce "kash! Bestie na ɗauka ma wani babban issue ne wanda zamu sha wuya ne ko wani deal mai ƙarfi international, akan ɗan wannan abun ne zaki damu kanki?"
"Kin sani duk mutumin da zai shahara a irin business ɗin mu dole yana da mugun wayo ba ƙaramin wuya samu sha ba kafin mu kamo wuyanshi".
"Kin manta ne? Tsuntsu mai wayo ai ta wuya ake kama shi saboda haka sai mu tsara komai yadda ya dace, ina Virus yake?"
"Kin san shi da shegen bacci yanzu haka bacci yake yi".
"Aikuwa bacci bai kama shi ba kira shi yanzu ya zo. amma kafin nan Boss ya turo miki da address ɗin mutumin da numbern sa?".
"Yeah ya turo" ta faɗa, a daidai lokacin da take kiran numbern virus.
Har kiran ya katse bai ɗauka ba, sake kira tayi a karo na biyu ringing biyu ya ɗauka cikin magagin bacci.
"Ka zo ɗakina yanzu" tana faɗa ta ajiye wayar.
Ba a fi minti biyu ba kuwa Virus ya bayyana a ɗakin.
Daga shi sai gajeren wando da singilet, ko ɗar babu wacce ta ji a cikin su, already sun saba zama da shi a kowani yanayi yadda kasan mace haka suka ɗauke shi, gabaɗayansu akwai yarda da juna da kuma fahimtar juna a tsakaninsu, sun ɗauki kansu ne uwa ɗaya uba ɗaya.
"Wani number zaka mana tracing muga a yanda yake yanzun nan". Scorpion ta faɗa.
Hamma ya yi bayan ya miƙe ya ce "wai ku duk abin da za'a yi ba za'a yi shi da rana ba sai mutum yana baccinsa ku dame shi wannan wani irin rayuwa ne?".
Ganin Anaconda ta haɗa rai ne yasa ya gane babu wasa a lamarin ta duk yanda suke dole ita ce babba a tafiyar akwai lokacin da bata ɗaukan raini a wajen kowanne daga cikin su idan ta harɗe sun san tabbas ba wasa a lamarinta.
Zaman dirshan ya yi akan study table wanda suka ajiye system din da suke amfani da shin dan irin wannan case din.
Numbern ta karanto masa ya saka a ciki ya fara aiki, cikin jimami ya waigo ya ce "Alhaji Naira! A ina kuka samo shi?"
"Shine wanda Boss ya bamu aiki akan shi" kai tsaye Anaconda ta bashi amsa.
"Am sorry to say gaskiya mutumin nan yana da mugun haɗari dealer ne guda na Cocaine gashi da tsinannen wayo".
"Kana ganin ya fi Anaconda wayo kenan ko me zaka ce? A tunaninka yanzu har akwai wani namijin da ba zan iya da shi ba ne duk wayonsa kuwa? Kai dai ka yi aikin da na sa ka kawai".
Cigaba da haɗa abun da zai haɗa ya yi har sai da ya kammala kafin ya rufe system din ya juyo ya fuskance su.
"Na tracing numbern yanzu haka yana loyalty hotel, sannan na haɗa komai ta yanda zamu na samun information akan duk wayar da zai yi, da duk wani shige da ficen shi".
"Ok abun ma ya zo da sauki yanzu abun da xa'a yi shine na baka 24hours ka tabbatar komai ya kammala ka binciko mun abun da ya fi so, shin yana neman mata ko akasin haka.
Saboda a wannan karon Scorpion ce zata marabce shi ko ba komai ta iya kwanciyar mage mai ɗaukar rai".
"Angama Ma'am, Zan iya tafiya?""Yes You can go sarkin bacci" Scorpion ta faɗa ita ma tana shirin tashi duk da ta duba time karfe biyu na dare.
"Ba dai tafiya zaki yi da tsohon daren nan ba? Ya kamata ki kwana ai".
"A'a bestie zan tafi kin san mu dare shine lokacin mu saboda haka bana ganin dare kuma komai dare bana tsoron na koma gida, a sanka a san cinikinka idan ka bari asan ka daina"...
"Ƴar malam taƙi halin malam! Shegiyar gyaɗa da ƴaƴan kanya wanda ya so ki ya ga bani wanda ya ƙi ki kuwa ya yi asara.."
"Hold on dear" ta katse Anaconda da wannan shegen kirarin da take yi mata.
"Na wuce have a nice dreams" tana sa jalbab ɗin ta ta fita.
Horn mai ƙarfi take ɗannawa saboda alamu ya gama nunawa mai gadi baya kusa da bakin Gate ɗin gidan bata da wani hanyar da zata bi idan ba yin hakan ba.
Ƙaran horn ɗin da ta ringa yi ne ya tayar da wasu daga cikin iyalan gidan da suke bacci.
Mai gadi kuwa already sallah yake yi hakan ne yasa bai buɗe gate ɗin ba, magajin sheik ne ya zo ya buɗe mata gate, a zuciyarsa yana jin haushi da takaicin hali irin na A'isha ace mutum kunnensa kamar kunnen ƙashi gabaɗaya gidan kowa ya bi layi na ƙwarai, idan aka cire ta da ta dauƙi mummunar hali ta yafa wa kanta, wannan shine dalilin da yasa ko magana baya yi da ita, har ran sa yana takaicin ace A'isha ƴar uwarsa ce kuma tsatson sheik.
"Ina kika fito?" Ya tambaye ta bayan ta fito zata shiga cikin gida.
"Yanda ka aike Ni" kai tsaye ta bashi amsa duk da ya girme mata.
Wani irin zafi ya ji a zuciyar sa game da amsar da ta bashi, hakan ne yasa ya ɗaga hannu da niyyar wanka mata mari, bai kai ga samu damar yin hakan ba ya ji an riƙe hannun.
YOU ARE READING
RUWA BIYU
RandomRUWA BIYU Rayuwa wasu Matasa guda biyu dasuka Aminta da Juna wanda suka maida kansu Ruwa biyu, ka siya daya kasamu daya kuauta!