IZZAAA....
Na Safiyyah Ummu Abdoul
1.
GUSAU
Garin Gusau ta samu asali ne kusan shekaru 37,000 da suka shud'e, ta bunk'asa zuwa birni bayan zuwan titin dogo (railway) daga zaria a shekarar 1927.
Mutanen garin sun kasance hausawa da fulani wanda suke rayuwa ta hanyar noman gyad'a da auduga tare da sarrafa su ta hanyoyin gargajiya har zuwa shekarar 1960 inda aka sa ma musu masana'artar tace mangyad'a da sarrafa auduga.
Birnin Gusau na tsakanin titin dogo daga Kaura Namoda zuwa Zaria da kuma babban titin Talatan Mafara zuwa Funtua.
Tana da Hakimin sarkin katsinan gusau kafin zuwan gwamna Ahmad sani yarima da ya maida shi sarki mai sanda.
A binciken shekara ta 2006 garin gusau na da fad'in kilomit 3,364, sannan ta kunshi mutane kimanin dubu 383, da dari 162.
Ana samun zinari da lu'ulu'u a wasu sassan jihar.
Akwai makarantu, asibitoci da masanaantu a garin.
Tudun wada babban unguwa ce da ta amshi sunarta a garin gusau. Akwai manyan masu kudi da d'an matsakaita har ma da talakawa a unguwar.
Gidan Alh Saifuddeen na tsakiyan tudun wada ne a birnin Gusau. Gida ne mai hawan bene biyu wanda da gani babu tambaya an san mamallakinsa attajiri ne saboda daga zubin gidan an San Naira tai aiki a ginin.
Alh Saifuddeen haifaffan garin Gusau ne yayi aiki da gwamnatin jiha har ya kai matakin permanent sectary kafin yayi retire ya shiga siyasa. Yana da mata biyu Haj. Hadiza wacce se da ta share shekaru 12 sannan Allah ya bata haihuwar danta Khalid bayan wasu shekaru takwas ta haifi Safiyyah.
Matarsa ta biyu Haj. Maryam mutuniyar jihar Niger ce, tana da yara bakwai Yusuf ne babba sannan Nuruddeen, Aisha wacce take Sa'ar Khalid, Farida, Fadila, Aisha Sa'ar safiyyah sai auta Umar.
Ba laifi akwai wanzuwar zaman lafiya a gidan Alh Saifuddeen don mafi yawan yaran a d'akin Haj. Hadiza da suke kira Momi suke tashi.
Duk ya aurar da yaransa mata saura Safiyyah da Aisha da suke Al-hikma university da ke jihar kwara.
Safiyyah da Aisha sun kasance tamkar aminan juna don samun wanda zai ji cikinsu se an wahala. Sau da dama sukan kashe su birne tsakaninsu ba tare da waninsu ya san anyi ba.GUSAU 2003....
Cikin ikon Allah Alh Saifuddeen ya ci za6en takaran sanata yankin zamfara ta tsakiya. Hakan yayi daidai da kammala karatunsu Safiyyah sai zuwa bautan k'asa.
Ba tare da 6ata lokaci ba yasa akai musu hanyar da zasuyi bautan k'asarsu a zamfara. Hakan kuwa akayi don ko da sunayensu ya fito duk zamfara aka tura su. Safiyyah da ta karanci kimiyar gwaje gwaje (micro biology) aka tura ta asibitin FMC, yayin da Aisha aka tura ta gidan talabijin na kasa.
Sati biyu da fara aikin Aisha wani maaikacin rediyon muryan Amurka ya kawo musu ziyara kasancewarsa d'an asalin jihar Zamfara kuma d'an masarautan gusau.
Tun haduwansu ya fad'a tarkon sonta haka yai ta bibiyarta da kira ta wasiku tun da ya sami lambarta.
Al'àmin siraj haifaffen garin Gusau ne, ya taso hannun kishiyar uwa bayan rasuwan mahaifiyarsa. Ya taso cikin halin zak'i da mad'aci don sau da yawa takan masa mugunta se ya maida wasa, hakan yasa ta gaji ta bari.
Ya sami aiki da muryan Amurka (VOA) bayan kammala bautan kasa. Baya da burin da ya wuce ya taimaka ma marikiyarsa duk da kasancewarta bata rasa ba.
Al'amin bai koma ba sai da aka tsaida lokacin aurensa da Aysha.
Ya nuna bajinta wajen gyara mata gidan da kuma lehe. Ya sakarmata kud'i don yasan aikin nashi ."Kin ganki kuwa twin sis, fatabarakallu Ahsanil khaliqeen" fadin safiyyah tana d'aukan Aisha hotuna.
Shiri sukeyi don halartar kamun Aishan da zaayi a gidan yayarsu Aisha da ke mortgage anan cikin garin gusau. Kaya kusan d'aya suka sa nan take kamanninsu da ake fad'i ya kara bayyana.
"Wallahi kin fini kyau twin sis, inama auren mu biyu akeyi yau" Aisha ta maida martani tana mai murmusawa.
Bayan sun kammala shiri, angwaye suka zo da motoci aka kwashe su zuwa mortgage. Ango da amarya suka kasance a bayan mota yayin da Safiyyah ke zaune a gaba se wanda yake tuk'a su.
Anyi kamu cikin armashi inda safiyyah ta bayyana a matsayin babban kawar amarya kuma 'yar uwarta ta bada tak'aitaccen tarihin amarya sannan ta rufe da musu fatan alkhairi tare da ma daukacin mahalarta bikin addu'an komawa gida lafiya.
Ranar asabar aka d'aura auren Aisha da Al'amin, wallimah akayi bayan daurin aure sannan aka cigaba da hidimomin biki har zuwa dare inda aka kai ta gidansu Al'amin a Gada biyu.
*********
"Twin sis bazaki zo bane wai, yau watanmu daya da aure sau daya kika lek'o mu". Fadin Aisha bayan Safiyyah ta amsa kiran da tayi mata.
"Wallahi ina da niyyar zuwa yau don har mafarkinki nayi. Am so sorry pls dear"
"Kar ma kizo din. Visana ya fita ina sa ran sati mai zuwa zan tafi. Don Allah ki fito yanzu"
"Kalli karfe nawa yanzu A'ilo bakwai saura fa. Ina nan zuwa de karfe tara inshaAllah"
"Yeeeeh se kinzo" ta fada tana mai kashe wayar.
"Safiyyah zata zo dear, me zan shirya mata ne?" Ta karasa tana mai tsalle. Kallo mijinta ya bita dashi, in zaa tsare shi bai ta6a ganin mutum mai zumunci da son 'yan uwansa irin matarsa ba. Komi da ya shafi danginta ke zuwa farko.Karfe tara tayima Safiyyah a gidan 'Yar uwarta. Ihu sukai tare da rungume juna tamkar sun share shekaru batare da had'uwa ba.
"Twin sis lallai Alanki ya iya kiwo kin ganki kuwa" safiyyah ta fad'i tana mai rola kyawun da 'yar uwarta tayi.
Dariya sukai gaba daya sannan suka baje. Abinci Aisha ta dauko musu suna ci suna hira. Chan Safiyyah tace "wai mijinki bacci yake ne bai zo ya gaida yayarsa ba"
"Au ashe fa yaya ce, se naga awanni kika bani. Kai Dady ya iya aiki"
Duka ta kaimata tace "wallahi baki da kunya wato ke kinyi aure ko".
Dariya suka saki gaba d'aya suna masu tafawa. Tare suka shiga kitchen suna hira suna girki har suka kammala. Nan din ma wani sabon hira suka dasa suna kallon hotunan biki suna dariya.
Sallaman da akayi ne ya katse musu hira, Mukhtar ne yayan Al'amin d'an wajen goggo (marikiyarsa).
"Mutan Lagos ne sannu da zuwa". Aisha ta fad'i cikin fara'a.
Sam hankalinsa baya kanta, yana ga safiyyah da ya tsare da kallo. Ita dinma shi take kallo dan ya tafi da imaninta kamar yanda ta tafi da nasa.
Sosa k'eya yayi sa'ilin da safiyyah ta kawar da idonta.
"Amarya ina yini, hankali na ya tafi ga mai kama da ke"
"Kai big brother, twin sisterta ce, Safiyyah, tana bautan kasa a FMC"
"Wow nice one, bara naje na yi ma goggo Albishir autanta yayi mata love at first sight" yana karasawa ya tashi ya shige cikin gida.