Dishi-dishi ya fara gani, juyawa yai ya shiga mota, figarta yayi kaman ana tashin yak'i, Allah kad'ai ya kaishi gidan Nusaiba lafiya.
Bugun da yake ma kofar yasa ta tsorata, a hankali ta lek'o ta gefen labulen. Ganin mukhtar yasa tayi saurin bude k'ofa. Taro shi tayi har ya zauna, ta d'ebo masa ruwan sanyi ta bashi yasha, zufan da yakeyi yasa ta fara masa firfita. Numfarfashi yakeyi Wanda ya k'ara bata tsoro.
Wayarsa ta d'auka ta lalubo lambar likitansa, ta kira tai masa kwatancen inda suke, ko da ya iso gwajin hawan jini yai masa ya tsorata da yaga 160/70. Tsare sa yayi da ido anan ya hango karkacewan da bakinsa yayi. Wawan jijjiga yai masa kafin ya saki kuka.
Dr Mas'ud abokinsa ne tun suna yara, Mukhtar yai masa hanyar zama likitan kamfaninsu.
Kukan da Dr keyi ya k'ara tsorata Nusaiba,
"Dr me ya same shi? Pls talk to me" abinda tayi kok'arin fad'i kenan."Mu tafi asibiti" ya fad'i yana cicci6anshi.
Cikin mintoci suka isa asibitin, sashin gaggawa (emergency) aka kaishi nan likitoci sukayi kokarin daidaita numfashinsa. Al'amin Dr ya kira, bayan sun gaisa dashi yace
"Autan goggo fa ba lafiya, amma abin ya zo da sauki, bugun zuciya ne (heart attack) da chunkushewar kwakwalwa (stroke), anyi sa'a bai sami mutuwan 6arin jiki gaba daya ba amma an sami kad'an (partial paralysis). Bincike ya nuna damuwa da bakin ciki ya jawo masa don jininsa ma yayi bala'in hawa.
Alhamdulillah an shawo daidaiton numfashinsa yanzu haka yana barci.""Matarsa fa, dafatan baka fad'a mata ba, kasan mata da rud'u"
"Eh toh gaskiya bata kusa, don ma Nusaiba ce ta kira ni, tace sun rabu lafiya ya dawo mata a rud'e, ita dai bata san mai ya faru ba, am suspecting his wife Ala, (ina zargin matarsa fa Ala)"
"Hmmmn kasan ance wasu matan sunfi ciwon kanjamau zama bala'.
Yanzu de zan taho anjima inshaAllah, yanayin jikin zai sa mu fad'i ma goggo ko muyi shiru"Nan sukai Sallama, Al'amin ya kira Dr Maryam ya fad'a mata abinda ke faruwa. Nan suka shirya, jirgin k'arfe shida suka biyo zuwa lagos.
Sun iske bai farka ba, sai Nusaiba da ta fige kamar wacce ta jima tana jinya, wayarsa da makullin motarsa na hannunta, zaune take a d'akin da zai Sada ta da inda yake tana lek'ansa ta gilashin k'ofar.
Jikin Dr Maryam ta fada ta saki kuka mai tsuma rai.
"Anty zan rasa Yaya na, mutuwa zanyi nima" kamar wasa se ta tafi suuuuuuu numfashinta na neman daukewa.Nan itama aka dauketa don ceton rayuwarta. Dr maryam ce ta kwashe wayoyinsu da suka fad'i da makullin motar Mukhtar da na gidan Nusy.
Mamaki ne ya cika Al'amin da ita Dr Maryam don kuwa wannan firgici da kuma kasancewarta a wajen sun san da wani abu a kasa. Amma halin fa suke ciki ya hana musu magana.Motar Mukhtar suka shiga basu tsaya ko'ina ba sai gidanshi.
A falo suka iske ta da yara suna cin pizza, ko amsa sallamarsu batayi ba. Ganin har da Dr Maryam yasa ta shiga hankalinta har ta gaida ta.
"Tafiya zamuyi aka rusa tashin jirginmu shiyasa kika ganmu ba notice, Auta na nan kuwa?" Dr maryam ta fadi bayan sun gaisa.
"Anty ai Auta se muyi sati uku bai kwana gidan nan ba, shine d'azu ya ce in je ayi min gwajin ciwon da ake kamuwa ta hanyar jima'i wai bai da lafiya. Ni kuma nace yaje chan ya k'arata da kanjaman da ya kwaso ma kansa don nayi HIV test kuma lfy ta lau" ta fad'i cikin izza da burgewa."Kanjamau fa kika ce safiyya? Ina kika kai bokonki? STDs d'aya ne kawai da zaki ce haka tunda lafiyanki k'alau muje kiyi jinyar mijinki an kwantar dashi a asibiti."
"Anty wallahi ba inda zani, ni na sa shi neman mata. Allah jikanshi da Rahma don karshen mazina..." Marin da taji an d'auke ta dashi yasa tayi shiru. Al'amin ne bata dawo daga duniyar mamaki ba yasaketa wani marin ya kara mata.