Chapter three

633 55 2
                                    

     
    
     Rayuwansu se ya kasance kowa na cin gashin kanshi, wani sa'in sai suyi  sati biyu basa magana, kowannensu na jin haushin d'an uwansa.
    Ana cikin haka Safiyyah ta samu cikin, Murnar da yayi ba'a magana don burinsa kenan. Ya kula da ita sosai duk da rashin d'ar da yai ta samu wajenta. Har cikin ya kai watan haihuwa, bai 6ata lokaci ba ya fitar da ita zuwa kasar Japan achan ta haihu.
    Kwata kwata bai ji tausayin kud'i ba haka nan ya kashe mata su. Anyi suna yarinya ta tashi da suna Aisha ana ce mata Humaira.
    Humaira na da wata uku aka maida Mukhtar aiki a Qatar. Suka tattara suka koma. Rayuwarsu dai ba abinda ya chanza zani. Anan Safiyyah ta had'u da Yasmeen suka k'ulla amintaka.
    "Kar ki yarda ki d'aga Masa kafa, kinsan maza basu da tabbas" karatn da Yasmin ke koyar da Safiyyah kenan. Nan ta k'ara sakin jiki wajen mulkinsa.

    "Sweet please tea zansha ki taimake ni dashi" fad'in Mukhtar suna zaune suna kallo.

     "Sweet ba ka kunyar sa mutum aiki fa, ga kitchen chan ka had'o." Ta fad'i tana k'ara maida hankali a kallo.
      Nazifi abokinsa da ke zaune ji yayi da ma bata wajen. Yana mamakin bakin  halin Safiyyah.

     "Gaskiya ka karo aure kafin ka sami mutuwan 6arin jiki don bak'in ciki"
     "Ya na k'are da Safiyah da zaka d'aura min aiki ko  bakin ciki kake so ya kassara in..

      Yau kwana Tara kenan babu Wanda ya sa d'an uwansa a ido tsakanin Mukhtar da Safiyyah. Kwance yake yana tuna abinda ya had'a su.
   Dawowa yayi a gajiye, ga yunwa na damunsa, lokacin ya rasa me ke Masa dad'i yayi. Shigowa yayi da Sallama a bakinsa amma ko wajibin bata sauke ba balle ta ce da shi "Sannu da zuwa",  
    Zama yayi tare da fad'in "Wash na gaji, sweet taimaka min da abinci". 
    Wani kallo ta watso shi dashi tare da Jan tsaki. Ransa ya 6aci sosai Amma ya dake.
    "Please my sweet, ki taimake ni yunwa nake ji kuma na gaji da yawa".
     
     "Ka dai San ba baiwa kasa kud'i ka siya ba ko, toh ka jira ranar da ka siyo baiwa se kazo ka ce ta kawo maka  abinci. Mtswwww..." Ta shige d'aki.
       Bak'inciki ya sa ya ji shi a k'oshe. Tashi yayi ya je gidan abokinsa da ke bayansu, tarbon da ya samu daga matar abokin yasa yayi tunanin anya dagaske matar tayi karatu har PhD. Yaci yayi kat sannan suka zauna hira da abokin nasa. Be 6oye Masa komi ba dangane da matsalarsu, shekaransu bakwai kenan da aure yaransu biyu kenan amma kullum jiya iyau.

   "Hakuri zaka k'ara sannan ka dage da mata addua. Ka dena cewa don tana da ilimin zamani ne, ni in ka barni zance mata masu ilimin boko da islamiyya sunfi tattalin miji, kaga ko ba komi akwai dabaru da wayewa a tattare dasu.
    Safiyyah nata ba rashin ilimi bane ko rashin tarbiyya, matsalarta IZZAA da girman kai da banzan halin nan da wasu mata suka d'auka na daidaita matsayin maza da mata (gender equality) Wanda Sam ba halin musulunci bane. Sun manta musulunci yafi kowace addini sauke ma mata hakkinsu da darajasu.
    Kayi hakuri aboki na, ka jawo ta jikinka, ba kashe kudi kawai mata ke buk'ata ba, suna son a basu kulawa kuma a darajasu, ka gwanda saukar da naka girman don a zauna lafiya"...
   Tsam yana kaiwa nan ya dawo daga duniyar tunani. Tashi yayi ya je d'akinta. Kwance ya same ta, gadon ya hau tare da rungumota..
    "My sweet my Queen" ya fad'a mata cikin rad'a. 
     "Am so sorry, ki yafe min, na san ban kyauta ba, kiyi hakuri mu dawo da farincikinmu, yanzu ki fad'i abinda kike so ayi miki"
     Rungumo sa tayi tana sumbutar sa don ita kanta tasan tayi kewarsa.
    "Jari zaka kara ma yaya,  miliyan biyar zaka bashi"
    "An gama my Queen, Ala ma nake son ba kudi ya karasa gidan rediyon sa (media house) kinga tunda na sami kudi ban ta6a masa abin dubu dari ba ai da kunya".

   "Wani Ala? Ba dai mijin Aisha ba, wallahi kar ma ka fara, ai akace maka wannan 'yan uba ne, nesa nesa yafi". Ta fad'i tana d'aure fuska.
   
   Mamaki ya hana sa cewa uffan, duk hidiman da suke musu ita kenan kullum cikin hana shi taimaka musu.
[3/29, 08:41] Ummu Abdoul🤕: Izzaa.... 9

Na Ummu Abdoul

    "Kayi shiru ko kana tunani ne, in ma rok'onka sukai wallahi bazaka bada ba".

    "Kai my Queen, ai tunda kin fad'i ai shikenan. Amma zamu je kasar Turkiyya Hutu mu duk har da Goggo, kinga zamu lek'a wajajen tarihin musulunci".

    "Allah ya. Kaimu jarumin jarumai" t fad'i tana fari da idanu.
  
Ko da ya shiga d'akin Kiran yayarsa Maryam yayi wacce suka fi shiri sannan itace ta kawo shawarar ya ba Al'amin kud'in nan. Ringing biyu ta d'auka
    "A'a mutanen Qatar da daddaren nan, fatan lafiya de"
   
    "Lafiya lau Anty ya su namesake?"

    "Suna nan lafiya, ka tura"

  "Dama dalilin kiran kenan. Nayi ma Safiyyah magana Amma ta nuna bata amince ba"

   "Au sannu kan tace, se kace ka aje matar alfahari, da za'a ce shawaran kwarai ta ba ka"
   Nan de ya kwashe duk abinda ya faru ya gaya mata, shiru tayi na wasu dak'ik'u sannan tace
   "Zan kai ma wanta check dinshi, duk abinda kake kar ka bari gobe ta wuce ba tare da ka aika ma ALA kudin nan ba, yana k'ok'arinsa wajen zumunci da mu duk da wariyan da mafi yawanmu ke nuna Masa, sannan baya jiran mu bashi. Ka dena biye ma su Goggo kayi zumunci da k'aninka"

   "InshaAllahu Anty hakan zaayi" daga nan sukai sallama.

    Washegari karfe takwas ya ma Dr Maryam a gidan sanata Saifuddeen. Direct dakin haj Hadiza mahaifiyarsu Safiyyah ta nufa bayan sun gaggaisa tace
  "Dama wannan ne Mukhtar yace a ba Khalid, Allah sanya Albarka a kasuwancin" ta k'arasa tana mai mik'a mata check din, sannan tayi mata sallama ta tafi. 
    Kasa godiya tayi don wani mak'ak'in bak'in ciki ya taso mata. Don mijin tilon 'yarta zai ba d'anta tilo kyauta se dai ta hannun 'Yar uwarsa. "Wato dai su ke juya min 'ya a gida, ta6" ta fad'i tana mai girgiza kafafu.
   Dr Maryam na fita d'akin takwararta ta shiga, tarban da ta samu yasha bambam da na d'akin Haj Hadiza. Kayan kari ta kawo mata tana mai janta da hira. Anan ne Dr take dan feshe mata halin Safiyyah.
    "Gsky ba halinta bane arowa tayi, amma ki bari zan sa 'yar uwarta tayi mata magana don suna jin maganar junansu. Kuyi ta hakuri kin San halin d'an yau".
   "Allah ya shirye mu duka toh"
   "Ameen don Albarkan annabi" sannan ta tashi ta ciko mata Leda da turaren wuta na d'aki da jiki. Sunyi sallama a mutunce ta rako ta har kofar babban falon gidan sannan ta koma.

     "Safiyyah kice ma Mukhtar Dr ta kawo an gode" Haj Hadiza ta fad'i bayan Safiyyah ta ansa wayar ko gaisawa basuyi ba.

   "Mummy ban gane ba me ta kawo"

    "Kudin da mukayi magana jiya, ta kawo check yanzunnan ta bar d'akin mamanku ko mi ta kai mata oho"
    "Wallahi zaayi rigima,  don zai ba Yaya Khalid Abu se duniya ta sani, yanzu zan je in iske shi kuwa"
    "Ni de ban aike ki rigima da mijinki ba, ai kyauta ce ba ajiya muka bashi ba"

   "Shi yasa zai wulakanta mu mummy?" Ta tanbaya tana mai rusa kuka.

    Se da tayi ma'ishi sannan ta sauka kasa ta same shi yana cin abinci. Janye kwanon tayi ta tsaya Masa aka tamkar zata dake shi.

    "Ke lafiya?" Ya fadi cikin tsawa-tsawa.
   
     "Wace jaka ka aika ta kai ma mummy check?"

    "Au! Na manta kisan jaki kawai ke jin yaren d'an uwansa jaki. Da fatan dusar ta ishe su."

    "Kamburrrrr.... " ta saki wata ashariya

    "Mummy ce jakar don rashin mutunci Mukhtar?"

    "Yoh kin ta6a ganin inda jaka ta kaima mutum sak'o har sukai magana ai se de ma d'an uwanta jaki ko"
    Nan fa ta fara zaginsa, ko amsa mata beyi ba, da taga ya manna mata hauka ne kawai se ta sa kuka. Tsallaketa yayi ya fita ya barta nan.

    Rigiman da se da suka di karfin wata basa magana, se da shi din ya koma ya nemi sulhu Amma ita ko gezau.
 

IZZA..Where stories live. Discover now