chapter five

597 35 1
                                    

MATAZU

   Matazu babban gari ne a katsina domin Kamar hukuma ce mai headquarter a garin Matazu. An kafa karamar hukumar a shekara 1991, bayan kafuwar jihar a 1987.
    Tana ta fadin kilomita 503, sannan tana da adadin mutane kimanin. 115,325.
    Akwai ababen more rayuwa da dama a garin matazu, sanaar mutanen garin Noma ne da kiwo.

    Alaranma Sadi, d'alibi ne ga babban malamin Matazu, yanda yake Alaranma haka yake likita a asibitin garin. Yayi karatun likitanci ta hanyar ciyaman dinsu na wannnan zamani.
   Matansa biyu, Wasila wacce take 'yar malam tana da yara biyar. Nasir, Nafiu, Nuratu, Nusaiba, da Auta Nuwaila. 
     Taufiqat itace matarsa ta biyu, 'yar asalin jihar kwara ce, garin Ilorin. Iyayenta malamaine amma a makaranta suka hadu don itama likitarce.

     Gidan Alaranma Sadi gida ne mai cike da tarbiyya, duk da matsanancin kishin da matan keyi. Taufiqat taso Jan yaran duka jikinta amma uwar gida wasila ta kad'a ta raya akan bata San wannan ba.
     "Nusaiba wai ke wata irin 'yar iskan yarinya ce, bana son salon karuwanci in aikeki maimakon ki dawo da wuri kina tafiyan nan naki kamar tsohuwar kilaki.." Wasila bata kai aya ba Taufiqat ta katse ta
    
    "Wosila! Wosila ina guje muka hillar bakin uwa, kina kiran danka da Iranu (Dan iska) wollahi zakayi kuka da idonka
    A ce kullum se na ce ka bari. Woo ka sigaba ranar da Allah ze amsa"

    "Sannu 'yar malamai dad'in abin nima ubana malami ne, ai ba cewa nayi Allah yasa ba. Shegen sanabe. Wuce ciki kema" ta karasa da dakawa Nusaiba tsawa.

   Tabe baki tayi sannan tace "olowu sha nuwa oo"

   Haka rayuwar gidan yake tafiya, wasila kullum da kalan zagin da take kiran yanta da shi, zamanin yayyin daga d'an banza, sakarai se wawa take cewa. Tasowan Nusaiba, tana son kwalliya, zata iya 6ata awa tana Zane fuskarta. Tafiyanta kad'ai abin kallo ne duk da iyakanta aji hudu a sakandare. Nan fa wasila ta tsiro amfani da Kalmar iskanci. Taufiqat kuma bata gajiya da mata nasiha.

    Ana cikin haka Nusaiba ta kammala sakandare har ta sami gurbin karatu a jami'ar Benin city (uniben). Ba tare da shayin komi ba iyayen suka tura ta inda zata zauna gidan  kawunta yayan wasila.
    Ta kammala shekara ta d'aya da ta biyu  cike da Nasarori. A shekaranta na uku ta had'u da Mimi, Mimi 'Yar asalin jihar Edo ce, tashin garin Kano. Kallo d'aya zakayi ma Mimi kayi tunanin arniya ce, shiga take na rashin mutunci.

   Sun saba sosai da Mimi duk da bambamcin hali da suke dashi. Kwatsam wani malaminsu ya nemi tayin soyayyar Nusaiba. Mimi ce ta k'ara mata k'arfin guiwa har ta amince masa.

   Soyayyar Nusaiba da Yasir soyayya ce mai tsafta, har iyaye sun shiga anyi maganar gemu da gemu.

   Wata rana sun fito lectures kenan hadari ya had'u, gashi Mimi da ke da abin hawa bata zo ba, kawai se ta yanke shawaran zuwa ofishin Yasir.
    Ko da ta isa, da sallamarta ta shiga ta iske zai fito, se suka yanke shawaran ya sauke ta gida se ya wuce.
    Basuyi tafiyan Minti uku daga kofar gate din makarantar ruwa ya sauko. Ruwan mai had'e da iska. Da kyar ya iya Jan motar har suka kai layin Evboumwan, a anguwan Etete hanyar sapele. Bai fi su k'ara tafiyan minti goma ba su isa gidan kawunta. Nan shedan yai aikinsa.
    Juya kan motar Yasir yayi zuwa Bestwestern Homeville hotel. Bata iya ce masa uffan ba duk da zuciyarsa na dukan uku uku.
    Bai ce mata komi ba ya shiga ya samo daki ya biya kud'in. Haka ta zama masa rakuma yana janta har cikin d'akin. Anan ya bud'e bakinsa ya ce
   "Nusy please ki taimake ni. Kinsan komi naki mallaki na ne, ki taimake ni  in rage shaawar da nake yawo dashi.  Wallahi ina sonki Nusaiba ki taimaka min" .

"Kyaleshi ance fa da dadi abin kuma ai sonki yake"

   "Kiji tsoron Allah ki rike mutuncinki"

   Abinda zukatanta ke raya mata kenan, tai shiru tana tunani. Hud'ubar mimi ya fad'o mata a rai inda kullum take nuna mata dadin abin da kuma dacewar ta nuna ma Yasir tunda aure zasuyi.

IZZA..Where stories live. Discover now