ISTANBUL, TURKEY
K'arfe biyu na rana suka isa garin instanbul da ke k'asar Turkiyya. Hotel d'in Four Seasons Hotel da ke Teyfikhane Sok lamba ta d'aya, Sultanahmet a nan cikin Instanbul suka sauka.
Sunci abinci sannan duk suka nemi Hutu don sauke gajiyan hanya. Ranar dai basu je ko'ina ba, an taru ana hira cikin farinciki da annashuwa. Mukhtar se mamakin Safiyyah yake don gaba d'aya ta aje IZZAA da ji da kai da take tak'ama dashi ta baje se hira takeyi.
Washegari wajajen k'arfe goma family bus d'in otal din ya dauke su zuwa ganin gari. Masallacin. Sultan Ahmad ko Blue Mosque suka fara zuwa. Blue Mosque masallaci ne da aka ginata tsakanin shekara 1609 ko 1616. Haraban masallacin cike yake da furanni sannan doguwan cilin din da masallacin kedashi anyi shi da wani irin tile (blue tiles) da Zane kala kala Wanda hakan ya k'ara ma masallacin kyau.
Duk sun yaba da Kya masallacin. Suna jinjina ma shugabanin k'asar don ba karamin kokari sukeyi wajen gyara.Daga nan suka zarce Hagia Sophia Wanda asalinsa chochi ne kamin daga baya aka mayardashi masallaci yanzu kuma ta zama gidan tarihi (museum).
Sun dawo a gajiye wanka sukai suka had'u a babban falon suna hira. Mukhtar ya shigo rik'e da chocolate a hannu. Mik'a ma Safiyyah, tana mik'a ma yaranta biyu-biyu ta tattara ta aje, sune ma suka had'u da sauran yaran suka raba. Mamaki ya cika d'aukacin mutanen da suke zaune. Amma ba Wanda yace mata uffan.
Kwanansu goma a Istanbul sunje wajajen bud'e ido kamarsi Topkapi Palace, suleymaniye mosque, Dolmabahce palace, Basilica Cistern da ke ba mutanen garin Istanbul ruwa tun k'arni na goma sha shida sannan sunje Istanbul Archaeological Museum da Galata Tower da sauransu. Sun karu da ilimi sannan sun yaba sosai da kokarin gwamnatin k'asar wajen inganta wajajen nan. Fadi suke "inaama inaama Nigeria zata gyaru haka".
Ana gobe zasu baro suka shiga Grand Bazaar, yana daga cikin manyan kasuwannin duniya da suke killace (indoor marketplace ). Akwai shaguna dubu biyar acikin ginin. Kasuwan da aka Gina tun 1461 akan samu tsofaffin sulalla da wasu ababen tarihi a kasuwan.
Kud'in da Safiyyah ta kashe ya so firgita Aisha. Ta siye abubuwa har na hauka, tana mai barin chanjin wa masu shago. Duk siyayyan daga na 'ya'yanta sai na mamanta babu Wanda ta k'ara ma siyayya.
Aisha kuwa ta siya ma iyayenta da 'yan uwan duk da kud'inta be kai na Safiyyah ba. Sun shiga shago kayan maza, nan Aisha ta kwasar ma ALA, mahaifinsu da yayyinsu maza. Ganin Safiyyah bata d'auki komi yasa tace
"Twin sis ki daukan ma Mukhtar wannan zai Masa kyau""Ta6 ke fa da sauranki, banga shegen da zan kashe ma kudi ba, ya bani kuma in kashe Masa"
"Wa'izubillah! Safiyyah mijinki da Aljannarki ke karkashin kafarsa kike fad'a ma haka, ni kam zan daukar Masa."
"Hmmmn ke kika sani ni tsakanina da miji babu rangwami"
"Ai dama akwai maganar da zamuyi se mun isa Nigeria. Abin har bacci yake hanani"
"Ai na fad'a miki kece wai 'Yar biyayya. Kwanaki fa tura min jakar yayarsa Gida yayi ta kaima Yaya Khalid check, don nace mata jaka ya kalli idona ya kira mummy jaka"
"Ke Safiyyah, shi Mukhtar d'in. Please ki dena ja ma iyayenmu zagi, kuma ki dinga hakuri".Tsaki Safiyyah tayi ta barta Tsaye, Ashe duk abinda akeyi Goggo na la6e, mamaki ya cika ta Ashe fad'in da Maryam tayi na cewa Aisha tafi hankali ba k'arya bane.
Sun sauka a filin jirgin Murtala da ke legas daganan suka sauka sokoto. Motocin gidan sun jirasu a filin jirgin sultan Abubakar sannan suka dauko hanyar Gusau.
Sun dawo suna masu godiya ga Allah da ya dawo dasu lafiya.sun huta sannan kowa ya koma gidansa ana Alhinin rabuwa da juna.Ko da Safiyyah ta shiga dakin Aysha ta iske tana mammatsa ma Al'amin d'inta kafafu. Dariya tayi cikin shakiyanci tace
"Ni de ranar da zaka gwada ma kanwata halin maza da kaina zan halbe ka"