1.

416 16 5
                                    

Juma'a 15-06-2012

A daidai lokacin da na iso wurin feu tricolore din Maurice Delens; police ya daga hanun sa, alamun da ke nunawa mu tsaya dan mu bar wadanda ke gefen mu su wuce; nayi tsaki tareda daidaita tabarau di na na Gucci; sauri na ke na isa gida, dan na samu na huta kuma na duba e-mail din da tuteur de memoire di na ya turo min domin kuwa saura mana kwana goma kaccal mu ba da memoire din, an sa mana delai de rigueur, na kara tsaki, ina da na sanin rashin fara rubuta memoire din da wuri, sai ga shi yanzu lokacin ajewa ya na kara matsowa; stresse di na na karuwa.

Isa ta gida ke da wuya; na ajiye kayan da ke hannu na; na nufi salle de bain (bathroom) dan yin wanka. Bayan na ida shiryawa, na isa falo, na ji shigowar mama; daya ke yau juma'a karfe daya su ke dawowa daga aiki. Na tarar da ita ta na waya da abba, nayi murmushi, Allah sarki mahaifa na, shekara 25 kenan da auren su, amma har yanzu so da kulawar da su keyi wa juna sabo ya ke zama, kullum addu'a ta ba ta wuce Allah ya ban miji mai irin hallayar mahaifi na ba.

Bayan sun ida magana ta mika min waya na gaishe shi, ya amsa ya na ce min "Yussyuss ya memoire din ki na ta kokartawa ko" na ce "eh abba, le 25 ne ma delais din, ka saka ni cikin addua abba" ya yi dariya tare da cewa "Yussyuss (haka ya ke kira na tun ina yar karama) a ko da yaushe ki na cikin addu'a ta ma fille; Allah ya ba da saa"
"Ameen abba; nagode sosai. Vous nous manquez enormement (we miss you so much)" na ce masa a daidai lokacin da idanu na su ka cika da hawaye; ina kewar mahaifi na ko na ce, mu na kewar sa, mu dukan mu; yau watan sa uku kenan rabon sa da NIAMEY; ya na Etats Unis, ya tafi karo ilimi,
Ya ce min "je viens à la fin du mois in sha Allah, calme toi( zan zo karshen watan nan in sha Allah, kar ki damu" da alamu ya gane ina so na fara kuka; dan na saba; a duk lokacin da mu kayi waya sai nayi kuka kafin in yi racroché (kashe waya); na shaku da mahaifi na, il est comme mon meilleur ami (ya zamanto kamar best friend di na); har mama ke cewa "Yusrah ke fa ba enfant unique  ba ce, in ki na wasu abubuwa sai ki manta da kina da yan uwa" shi ko sai dai yayi murmushi ya na ce wa "kyale ta Yussyuss". Mun kusa minti goma muna magana da shi kafin mu yi sallama; ya kara ba ni courage a kan karatu na da kuma mémoire
din da na ke rubutawa.

SA'AR RAYUWATAWhere stories live. Discover now