2.

186 10 2
                                    

Misalin karfe goma sha daya na dare dai dai na tura wa Mr Maman Sani e-mail, bayan na karanta parties din da ya turo min da correction din da ya kama ta nayi, na ji waya ta tayi sonné (ringing), alamun message ya shigo; cike da mamaki na ke tambayar kai na wa ke min message wanan lokacin. A haka na janyo waya ta tare da bude sakon da ya shigo, ko da na ga sunan na saki dan murmushi, ina cewa ashe ma Zuhra ce,

"Yussy ya kike? Ya karatun? Ya su mama? Ya labarin abba? Dazu na hadu da Yasmin, ta ke ce min ba ki da dama kwanakin nan, dama Zaïd Abdel Hak ne ke son numero din ki"

Nayi murmushi tare da tsaki; duk wadanan tambayoyi lokaci guda; Zuhra ba za ta taba canzawa ba.
"Zuhra zuhra; a cikin tambayoyin ki wacce ki ke so na fara amsawa" na rubuta na tu ra mata

"Mdr; dukan su" ta maido min

"Ok, attends je vais essayer; hahahaha; to lafiya ta lau, karatu kuma alhamdulillah, mama na nan lafiya lau, abba ma haka dazu munyi waya da shi, wallahi ban da damar gaskia, kin ga 25 din nan za mu ajiye memoire. Waye kuma Zaïd? Ya san ni ne? " na mata repondre;

"Yussy ba na son iskanci kin ji ko; ke komai sai kin saka wasa a ciki"

Ina karantawa na mata repondre da "wallahi je suis serieuse; je ne l'ai vraiment pas reconnu"

"Ok tohm, ki na tune da aminin Mohamed, wanda ku kayi course din bikin mu tare?"

"Oh na gane shi wallahi, da ce min ki kayi le gas sympa, ba matsala ki ba shi"

Sai ta ce "ok, amma fa il est serieux, aure ya ke so"

"Kin ji ki fah, kin san yanzu memoire ya aure ni....hhhh"

Ta turo min da emoticone din fushi tare da min fatan asuba ta gari.

Kawar arziki kenan; Zuhra aminiya ta ce, mun shaku sosai da ita, tayi aure shekaru biyu da su ka wuce; kuma Allah ya albarkaci auren su da diya mace mai suna Hanane.

"Je voulais terminer la journée en souhaitant une bonne nuit à une jolie fille. Bonne nuit" nayi tsaki; bayan karanta message din da ya shigo cikin waya ta daga bakuwar lamba, na saba samun message masu kama da haka daga numero din da ban sani ba, wanan ne ya sa na kashe waya ta, na tashi na shiga ban daki; bayan na sa pyjama, na nufi chevet de lit na kashe veilleuse din daki na, nayi addu'ar kwanciya bacci "Bismikal lahumma Amutu wa'ahya", na kwanta.

Asuba ta gari

SA'AR RAYUWATAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt