7

132 7 0
                                    

A haka na ci gaba da kula Mustapha, ba da sanin iyaye na ba! Idan ya zo niamey shi ke tsara yanda za mu hadu; ni kuma sai na biye masa da yake na makance a kan shi!
A lokacin abba ya gyara min takardu na, na tafiya Maroc (Morroco) dan ci gaba da karatu na, amma na nuna masa sam ba na son nayi nesa da su, gaskiyar maganar ita ce ba na so nayi nisa da Mustapha! Da abba ya ga na matsa sai ya ce min "to Yussyuss tun da haka ki ka zaba, ba matsala, ni kan kai na na fi son na gan ki kusa da mu a matsayin ki na ya mace; sai dai karatun kasar nan, na ga sai a hankali, ko da yaushe cikin grève (strick) a ke" nayi murmushi na ce "papa na, in sha Allah komai zai tafi daidai kuma na ga an bude wata sabuwar makaranta mai suna ESCAE, na ji an ce su ba su biye ma yan université (university) cikin grève din su", ya amince; mama kuwa ba ta da abun cewa tunda abba ya riga ya yanke hukunci, amma ita da son samu ne, na tafi Maroc din, ko nayi nisa da Mustapha!!

-----------         *******        ------------

A kwana a tashi ba wuya, na yi rentré (fara karatu) a ESCAE, tare da yardar mahaifi na. A can na hadu da Safiya, ta girme ni da shekara 1, ta na yanda ta ke so da rayuwar ta, ita ce wanan boite de nuit (club) da dai sauran su, sabanin ni! Ta nuna ta na son kawance da ni, tun ina gudun ta har dai mu ka saba, mu ka shaku. A ko da yaushe mu na tare a gida ko makaranta. Wata rana Mustapha ya zo Niamey, na ce wa Safiya ta zo ta raka ni masabkin sa mu gaishe shi. Mu na tafe a motar ta mu na fira sai ta ce min "Yusra ina fatan dai kinyi tanadin abincin da za ki kai wa Mustapha" nayi murmushi na ce ma ta "Safbaby na kai masa abinci sai ka ce miji na" tayi dariya ta ce "ban gane ba; ai nan da lokaci kadan in Allah ya yarda sai shafa fatiyah" na amsa da "Allah Ya sa, Ya karkato hankalin su mama su amince da shi" sai ta ce min, a daidai lokacin da tayi garé(parking) din motar ta bakin makaranta "ni kam Yusra da za ki yarda, da na kai ki gurin wani malami na, aikin sa kamar yankan wuka ne" na ce ma ta "haba dai qawata?? Shi ne sai yanzu za ki fada min, s'il te plaît (please) da mun kare wanan cours din mu je" ta amsa da "to" mu ka sauka mota mu ka nufi cikin makaranta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 01, 2017 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SA'AR RAYUWATAWhere stories live. Discover now