CIN AMANA KO FANSA PART 1

10.5K 133 3
                                    

[6/29, 14:03] Rukayya Shuaibu: 📓📓📓📓📓📓📓📓
         *CIN AMANA*
                *KO*
             *FANSA*
📓📓📓📓📓📓📓📓
  *(TRUE LIFE STORY )*

Zahra Muhammad Mahmud

® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
       *PML*

*Godiya ga Allah mad'aukakin Sarki, tsira da Aminci sutabbata ga annabinmu Muhammad sallallahu ala'ihi wasallam.*

*Wannan labari ba k'agagge bane yafaru dagaske,duk abinda ke ciki anyine da gaske, suna kawai na wa'inda abun yashafa Nasauya,da d'an abinda ba'a rasaba.baya ga haka babu abinda Nasauya*

Ya Allah, yadda nafara rubuta littafinnan lfy,Allah kasa nagamashi lfy.

*page 1*

Y'anmatane su biyu, y'an kimanin shekara goma sha shida da haihuwa,suka rugo da gudu zuwa Cikin d'akin kakarsu suna ta kiranta,  uniform ne ajikinsu, alamar daga makaranta suke,

"Grany!!! Grany!!!  where are you? we miss you so much,mekika tanadarmana yau."
A zaune suka ganta tana Kallonsu, k'arasawa jikinta sukayi, suka rungumeta,  kowacce tamata kiss a gefen kumatunta.

"Kai ni banason iskancinnan naku, ace gird'a gird'a daku Amman har yanzu baku girmaba,wato abinnaku gaba yakeyi,yau kuma harda sumbatata ko?".

Dariya sukayi suka K'ara rungumeta,Khairat ce tace,

"Haba Grany, danma kinsamu munzo gidanki yau shine harda yimana wulak'anci,ni dama wlh banso zuwa ba,Fatima ce da shegen naci tace muzo gidanki,gashi daga zuwanmu  kinfara halinnaki."sakin Grany tayi takoma gefe tazauna,

Fatima tace, "Wayyo Sis kiyiwa Grany uzuri, bakiga se kallonmu takeyiba, alamun taji dad'in ganinmu, hala taji haushin bamuyi sallama bane, ko Grany?",tawaiga Tana kallon kakar tasu.

Grany dariya tayi sannan taruk'osu dukansu tace ,

"Haba kha'iriyya ta fushi kikeyi danine?, nicefa babbar k'awarki ranar bikinki,"dariyace takwacemusu dukansu,khairat tace,

"Wai,dagwargwajiya kenan Grany ansha gwargwaro ranar aurena,"cigaba sukayi da dariyar.

Ranar wuni sukayi agidan Grany,seda la'asar suka mata sallama suka wuce gida.

Khairat da Fatima sa'annin junane, dan anhaifi Fatima da Sati biyu aka haifi Khairat.

Iyayensu mata ya da k'anwane,haka zalika, Iyayensu maza suma wa da k'anine.

Alhaji Nasir Abubakar shine mahaifin Fatima,suna kiranshi da Abba,mahaifiyarta Mesuna Hajiya Salamatu suna kiranta da Umma.yaran Alhaji Nasir hud'u biyu maza biyu mata,Yaya Jameel shine babba, se Yaya Umar mebimasa,se Fatima, da autarsu Yasmeen.

Alhaji Mukhtar Abubakar shine mahaifin Khairat,suna kiranshi da Daddy, Wanda wa yake agurin Alhaji Nasir,uwa d'aya uba d'aya,
Matarshi d'aya Hajiya Binta,wacce take yaya ga mahaifiyar Fatima, yaransu guda shida,hud'u mata biyu maza,Aunty Fareeda Itace babba ,se Yaya Kamal mebimata,se Aunty Khadija,se Kha'irat, se Fa'eeza,da autansu Yusuf.

Gidan Alhaji Nasir dana Alhaji Mukhtar ahad'e suke sede katanga data rabasu,
Suna zaune da iyalansu agarin Kaduna awata anguwa Mesuna Tudunwada dede layin k'osai kan katagum road,

kansu ahad'e yake haka na iyalansu komai nasu tarene ko kasuwancin suma a tare sukeyi inda suke Saida kayan sawa kama daga na maza zuwa na mata, da yara, komai suna saidarwa a kasuwar checheniya dake Kaduna.

Zumunci ne me k'arfi a tsakaninsu inda ahalin yanzu babban d'an Alhaji Nasir yana auran Y'ar gidan Alhaji Mukhtar Khadija, harda yaransu guda biyu suna zaune a kinkinau dake Kaduna,ita kuma Farida wani ma'aikacin nepa take aure harda yaranta guda uku.

CIN AMANA KO FANSAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن