chapter 2

8.5K 708 21
                                    

The Messenger of Allah (blessings of Allah be upon him and his family) has said: “The superiority of the Qur’an over the rest of words, is like the superiority of Allah over His creations.”

40votes
Yeeey
♥♥♥♥♥♥

Gidane na jar  kasa mai dauke da dakuna biyu da makewayi(toilet),sai dan madai'daicin tsakar gida mai dauke da ran'dar ruwa ta ka'sa da kuma murhu na girki guda biyu.

Da sallama siddiqa ta shigo cikin gidan a gajiyenta,inna dake zaune a gaban murhu duk hayaki turnuke wurin ya rufe mata ido tace,ah ah yar inna har kin shigo sannunki..

  Siddiqa ta rube a kasa tana fadin,wayyo Allah na gaskiya inna yau sai kin min ga'shi kafar nan da ruwan zafi..
  Inna dake kokarin tura itace a cikin murhu tace,kedai wallahI anyi ragguwar tsiya,nan da hayin gadan kike korafi?duka tafiyar nawa take?

   Siddiqa tadan turo baki,wallahi inna kullum sai na makara,gashi nayi ta shan duka kamar wata jaka..
  Inna ta mike tazo gabanta,nasan kina kokari yar inna,nima bana son kina irin wannan wahalar kinji,kici gaba da hakuri lokaci ne..
  Siddiqa ta kura wa innar ta ido,toh wai inna ina babana ne wai shi?

   Innar ta mike rai a bace tace,maza tashi kije kiyi wanka kizo kici abincinki taliyar fulace wadda kike so,kum na riga na hada kokon dare da zaki fita dashi..
   Siddiqa ta mike a sanyaye,har yanzu ta kasa gane mai yasa innarta take fushi kullum idan ta anbaci mahaifinta,ko ba komai ai ya dace tasan ko mahaifinta yana raye ne ko kuwa ya mutu,kuma ina yan uwansa suke?.

Karfe 7 na yamma ta dauki bokitin kokonta ta fita dashi,tafe suke ita da zuwaira dan itama ummanta na daura mata doya da kwai na siyarwa..

    Siddiqa gaba daya tunanin wannan saurayi ya cika kwakwal'warta,batasan mai yasa idan ta gansa take jin wani irin farinciki da faduwar gaba ba,kodan kyawunsa ne da yayi yawa oho!,zuwaira ta buga mata dundu biyu masu kyau a baya,tayi firfigit tana kallon ta,zuwaira taja tsaki,shegiya tunanin mai kikeyi ne wai?tun dazun fa wadan'cen samarin ke faman kiran ki amma hankalinki baya nan gaba daya..
   Siddiqa tace,yi hakuri muje banji bane,kuma wallahi kada ki sake min dundu haka.
 
Sunkai babban titi na cikin garin,kamar daga sama siddiqa ta hango wani da kayan NYC can wajen usman mai tsire..
   Ta kalli zuwaira dake kokarin tsallake titin,kiyi gaba kawai gani nan zuwa,ta koma can kusa da wajen ta ajiye bokitin kokon ta ta kura ido tana jira taga waye zai juyo,addu'a kawai takeyi ,Allah yasa wannan kyakkyawan ne.

     Horn kawai mai adaidaita tahu yake ta kwarara mata amma inaa.. hankalinta na can wata duniyar,ribas yake yi kuma ya tabbata zai mata lalata da kayan talar ta idan bata gusa daga wajen ba,ganin ta masa banza sai kawai ya share yaci gaba da ribas dinsa gadan gadan..

    Kafin ta ankara har ya ture mata bokitin kokon ta,a firgice ta mike hankali a tashe,tana kokarin yayyafa masa bala'I da sai ka biyani yaja napep dinsa da speed ya wuce abunsa yana jan tsaki..

    Hankalinta a tashe ta shiga kwashe robobinta tana fadin,yau na shiga uku Allah ya isa wannan mai napep din baya da imani yaje shi da Allah..
    Tana cikin kwashe kayanta zuwaira ta karaso wajen,ta kallI siddiqa da mamaki sosai tace,ya akayi haka ta ?

   Siddiqa hawaye sun cika ido tace,wallahi tallahi bazan taba yarda ba,ai na gane napep din nasa,dauda ne sai naje har gidan su dan bazata sabo bane,yanzu dan kudin mashin din goben ma bazan samu ba..

   Zuwaira ta na taimaka mata da daura bokitin a kai tace,kema dai siddiqa kin cika sabolanci wallahi,hankalinki yana ina har dauda ya ture miki bokitin kokon naki?
   Ai fa a take ta tuna da abunda take kallo,tayi saurin juyawa tana kallon wurin mai tsiren,wayam ba kowa a wajen,tadan matse bakinta bataji dadi ba wallahi..

Sai da innarta ta mare ta dan haushi,dama gashi dan geron dama daukar shi tayi ba'shi,gashi kuma sun rasa kokon gaba daya sai naira dari kacal data dawo dashi.
      Kwanciya siddiqa tayi akan yar kafifarta,innar na gefe tana gyara waken suya wanda zatayi awara dashi gobe da safe,ahankali tace,kiyi hakuri inna dan Allah kinji..
   Innar tayi mata banza,siddiqa ta runtse ido,tasan halin innarta idan tayi fushi,zata bari sai gobe ta sake bata hakuri.

"Washe gari.
tafe suke ita da zuwaira sai buka sauri sukeyi tamkar zasu tashi sama..
   Siddiqa ta kalli zuwaira,yanzu dan Allah zuwaira sabida tsabar ma'ko irin naki damu hau mashin da kudin naki gwara munsha wannan wahalar nan..?

  Zuwaira ta watsa mata harara,na fada miki siddiqa kudin nan tarin su nakeyi,kindai san halin da gidan namu yake ciki ko?.
    Tabe baki kawai siddiqa tayi ganin har sun kai bakin gate din makaranta.
     Tun kafin su shiga gaban su ke faduwa,malam ahmad ne da senior rabi a wajen sun tara dalibai yan makara.

Sai kuzo ai kubi layi kuma sarakan makara,malam ahmad ya fada yana yiwa su siddiqa nuni da karkashin bishiya inda dalibai da yawa suke a tsaye.
     Senior rabi itace labour prefect dinsu kuma muguwa ce sosai dan gaba daya makarantar tsoron ta akeyi.
     Ta kalli siddiqa da zuwaira,wai ku ya zanyi da ku ne huh! Kullum har na gaji da ganin ku cikin yan makara...
  Malam ahmad yace,ai daga yau zasu daina dan ubansu,maza ku rage tsawon ku a can,yayi musu nuni da tsakiyar rana..
  Da saurin su suka karasa.
  Har aka kammala asambili suna nan a wajen,can idonta ya hango yan nysc dinnan,ta kura musu ido su uku ne banda macen,kallon saurayin nan kawai takeyi har suka wuce..

"Break time nayi ta kwashi litattafansu na maths tayi staffroom dan kaiwa malam garba kamar yadda ya umarceta.
    Tun kafin ta shiga ta jiyo tashin turanci daga ciki,ta saki murmushi dan ta tabbatar wadan nan coppers din na ciki,hakanan ta tsinci kanta cikin farin ciki sosai.
   
Jabir ne ya zauna akan desk din adyan yana fadin,oh my gosh wallahi garinnan sauro har na bala'I,neelam tayi hamma tana fadin, I didn't get much sleep jiya,from one band to another kunnena har ya gaji da saurara  mosquitos sucks alot ..
     Daniel ya kwashe da dariya,you guys should stop complaining,idan wani yaji zai iya zaton ku din bada ga north din bane..
    Adyan yadan dago daga marking din classwork din da yakeyi,yana kallon su yace, why do you guys like talking to much huh !
Gaba daya suka kallosa,yasa hannunsa yana sosa kunnensa,my ears are hurting..
    Jabir ya kai hannu wurin kunnen adyan yana fadin,hey hey guy,anya kuwa ba wankan da kayi ta yi bane jiya da daddare..
   Adyan ya kwashe daga rikon da jabir yayi masa yana yatsina fuska,dai dai lokacin siddiqa ta rangada sallama ta shigo staff room din.
Neelam ta kalla tana fadin,malama ina kwana?
  Ta amsa a sake tana sake kallon siddiqa kamar taso ta gane yarinyar,can tace yes,the dirty student..

    Tana kusanso desk din malam garba gabanta na faduwa,sakamakon neighbours ne da wannan saurayin mai kyau..
    A takaice tace,good morning sirs,Daniel ne kawai ya amsa mata dan jabir da adyan hankalinsu baya wajen ta ma gaba daya,sai teasing adyan jabir din yakeyi,amma yayi masa banza tamkar bada shi yakeyi ba.

Malam garba ne ya daka wa siddiqa tsawa,kee!
Firgita tayi sosai dan sai a lokacin ta lura da ta'asar da tayi,gaba daya bata lura da kafar malam garba ba tayi tuntube littafan suka rube daga daya a kasa..
    Dan ubanki ina hankalinki yake! Ta shiga kwashe books din tana fadin,am sorry sir..
    Jabir ya juyo yana kallonsu,malam garba ya mike yana daukar bulalarsa,ke wace irin makauniya ce zaki taka ni haka,siddiqa ta rage tsawo tana rokon gafara,amma Inaa malam garba ba imani ya shiga kai mataa duka..
   Neelam runtse ido ma tayi,tana mamakin yadda ake dukan dalibai haka a arewa..
   Jabir ya mike yana fadin,malam garba kayi mata afuwa mana..
    Siddiqa ta saki ihun azaba,adyan earpiece kawai ya saka ya kishingida ya runtse idonsa,mutum ne shi da baya son hayaniya da shiga harkar da bata shafe saba..

Please
Vote
N
Comments

Instagram @ dija_bature

Boyayyar soyayyaDove le storie prendono vita. Scoprilo ora