BABI NA DAYA

2.7K 128 24
                                    

16 PM] ‪+234 706 884 4606‬: *MAI GASKIYA.....*1

©MAMAN HANEEP

EDITOR:SANA S MATAZU
2017

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI!

***

Hannu ta sanya da nufin tsaida dalleliyar motar data kunno kai a dai-dai wannan lokacin, ba b'ata lokaci had'adiyar motar tayi parking a bakin hanya wacce ta d'auki hankalin y'an mata guda hud'u da suke tsaye.

Cikin salon yanga da iyayi irinna wasu 'yan matan na yanzu ta dube su tare da ce wa," muje to ya tsaya",  gajeriyar cikin su mai sanye da doguwar riga har k'asa ta d'an ja da baya tana ce wa dasu," to kuje kawai saina taho zanjira A dai-dai ta sahu",

Cikin ya tsine fuska wacce ta tsayar da motar ta ce" Haba Maimuna kedai kullum a kazo tafiya sai kin raba mana tafiya bayan duk guri d'aya zamu?"
Murmushi tayi kana ta ce" kuje kawai Ramlatu kinsan bana hawa lift sau nawa zan fad'a muku?"

"kun fa tsayar da mutum kun kuma tsaya kuna surutu in bazaku shiga ba nizanje na shiga kud'in mota na ya huta ace ke kullum sai an samu matsala da ke?", cewar Maryam,

Alamun haushi ya bayyana a fuskar Ramlat don haka a tak'aice ta ce" Mu shiga gaba d'aya ko kawai a hak'ura mu jira ADDS din",

"hmm ni kuma bazan hak'ura ba kinga Kubra zomuje mu shiga kyale Ramlat da Maimuna",

Nan taja hannun kubra suka isa gaban motar ya bud'e suka shige bayan sun gaidashi,

Mugun tsaki Ramlatu taja, Maimuna da ke gefen ta ta ce" Uhmm ko wani zaki tare Ramlatu naga kamar kinji haushi na", " ni banji haushin kiba kawai dai bana son rana ne kuma bana son  mutafi mubar ki ke kad'ai tsaye a nan",

"Allah sarki Aminiya ta duk da mun banbanta wajen ra'ayi inanan daram cikin ranki Ramlatu nasan su Kubra bazasu iya cin galabar rabamu ba duk da taku tafi zuwa d'aya da su","Yanzu me yakawo wannan maganar memcy?Burin ki dai kullum mutafi Sch a ADDS bayan rana tagama gasamu, nasan yanzu su Maryam sun jima da isa makaran ta koma sun kusa kaiwa tunda yau ba new site zamuyi lacture ba",

Sunan tsaye tana ta mita har suka samu A dai-dai ta sahu ya kwashe su Maimuna dai hak'uri take bawa Aminiyar ta ta har suka isa Makaran ta.

A dawowa ma rasa abin hawa sukai don haka wannan karon Ramlatu bata biyewa Maimuna ba, suka tsayar da lift suka shige yayin da suka bar Maimuna tsaye wacce ta soma kiran k'anin ta Yahya a waya yazo ya d'auke ta akan mashir.

Gaban ta ne ya yanke ya fad'i das! a sakamakon had'a idon da sukai da yayan ta Abubakar a yayin da take sauka daga had'addiyar motar da ta kawo ta har k'ofar gida,
Cikin yak'e ta shiga d'agawa su Maryam hannu wanda da anyi gaba kad'an suma zai ajye su kasancewar su duk a unguwa d'aya suke...

Ko sallama batai ba ta afka d'akin Maman ta a tsorace don ganin Abubakar ya biyo bayan ta tasan dai ko bai dake ta ba tasha masifa akan ya kamata  dumu-dumu da laifin daya hanata tun farkon shigar ta jami'a.

Cikin rashin sa'a bata tadda Mama a d'akin ba  Mama na wanka a bayi balle ma ta hana Abubakar dukan ta, aikwa yana shigowa ya zare belt ya shiga lafta mata tana ihu tanai masa Allah ya isa,
Mama da ke wanka sai jiyo ihu tayi a yayin da ta ke ce wa" Kaga ka dena duka na babu ruwan ka dani inka kuma duka na Allah ya isa",

Ba shiri ta watsa ruwan ta futo a gurguje ta tadda Abubakar na dukan Ramlatu kamar Allah ya Aikoshi, nan tashiga tsakiya ta rik'e belt d'in tana fad'in" Haba Abbakar meye hakan wai me tayi maka haka?"

"kinsan kwa yarinyar nan bata dena hawa motar mutane ba? Yanzu akan ido na aka ajye ta ita dasu Maryama "

Nan Mama ta saki salati da tafa hannu ta juyo kan Ramlatu ta rufe ta da fad'a" Yanzu ke kam bazaki samawa kanki lafiya kiji fad'an da kullum sai anyi miki ba? Ace kedai kunnan ki bazaiji maganar da zaa fad'a miki ba?,

Cikin sheshek'ar kuka ta ce"nifa Mama karya yayimin bawata lift da mukai saurayin Kubra ne ya ganmu ya rage mana hanya shine wai yace lift mukai don kawai ya dake ni hankalin sa ya kwanta kuma wallahi ban yafe ba",

duka ta kaiwa bakin ta ta kuma ci gaba dayi mata fad'a bayan na hawa motar mutane harda mugun rainin da ta yiwa Abubakar,
Shi kuwa haushi da takaici ne ya isheshi duk ransa ya b'aci Allah ya isan data dingai masa a k'arshe ma ya ce" kyale ta Mama yau Mohd zaizo ai in yazo duk zan gaya masa abinda kikeyi tunda kinfi jin maganar sa ni daga yau bazan kuma hanaki shiga lift ba in kikaje Dan yan kan kai ya Kwashe ku ai bawani kukai wa asara ba",

Cikin k'unk'uni ta mik'e tana fad'in" oho dai mutum in banda munafin ci babu abinda ya iya ai in baka had'ani da Yaya Mohd baka cika munafiki ba".

tashige d'aki tana hararar sa, "Allah ya shirye ki Ramlatu" Cewar Mama.

****

to da Yaya Mohd yazo ma sata yayi a gaba yayi mata Fad'a hadeda nasiha a karshe dai tassshi yai mata Alkawarin zai siya mata mota in Allah ya buda masa, bai bar garin kano ba saida ya tabbatar ya ajye musu dukkan abin da suke buk'ata ya bawa Ramlatu kud'i wanda zqta dinga hawa mota da sauran bukatu na dan Makatan ta dubu d'aya ya bar mata a hannun ta ya bawa Mama sauran dubun tara ta ajye mata kafin yakuma zuwa, kasancewar yana aiki a katsina ne matar sa da yaran sa guda uku duk suna can..

***

safiya suke cikin rangaji kai daka gansu kasan sungaji mutuk'a, har sun kusa kaiwa bakin get ta hango shi durk'ushe gaban wata bishiya yana haki had'eda tari, nan ta ce dasu" Maimuna kunga wani bawan Allah kuyi gaba nasame ku a bakin get taimaka masa zanyi",
"ok shikenan kiyi sauri dan Allah kinga ana rana yau jumaa kar muita jiran ki".

Cikin sauri tazo gaban sa fuskar ta d'auke da Alamu na tausayi, ta ce" Sannu Baba me kake bukata?",  bakin sa ta kalla da yake motsi a hankali yana furta ruwa," ruwah ruwah".

da sauri ta duba gabas kudu da arewa aikwa idon ta yayi Arba da wasu samari guda biyu acan nesa da su, hannu d'aya daga cikin su d'auke da ruwan gora, don haka gudu-gudu ta nufi gurin....


ku biyo ni
[11/3, 4:16 PM]

MAI GASKIYAWhere stories live. Discover now