17 PM] +234 706 884 4606: *MAI GASKIYA...6*
©MAMANHANEEP
EDITOR:SANA S MATAZU
2017
***
A hankali ta soma murza idanu wanta da hannayen ta don dishi-dishi ta ke gani bakin ta na furta Kalmar shahada har idon ta ya bud'e tangara rau, ta shiga dudu ba d'akin da take a cikin sa.,
Nan tai zunbur ta mik'e a tsorace ta dafe k'irji tashiga salati da innalillahi don ganin mutane biyu a zaune kan doguwar kujerar da ke d'akin daga gefen hagu,
Nan take gaban ta ya yanke ya fad'i dass! Ta kuma murza ido ta dube su sai kuma Abin da yafaru ya fad'o mata, tasan dai wani saurayi ya d'auko ta ya rage mata hanya amma ba ta san sanda aka kawo ta cikin gidan ba,
Don haka ta ci gaba da binsu da ido kamar yanda suma su ke kallon ta.,Cikin bin bango ta isa k'ofar d'akin ta shiga k'okarin bud'ewa ta na jijjigata amma gam ta ke a kulle ko motsi k'ofar batayi, da ga bayanta ta ji sun kwashe mata da dariya,
Dukan k'ofar tashiga yi babu k'akkauta wa har ta gaji ta bari don kan ta ta zube a gurin ta na haki.,Ta ke taji wani mugun tsoro da fargaba sun dirar ma ta ta juya ta kuma kallon mutanen da ke cikin d'akin maca ce da namiji kuma sam ba suyi kama da mugayen mutane ba asalima hirar su suke suna juyowa sunai mata dariya ganin lokaci na k'ara ja agogon d'akin ya nuna uku saura kwata yasa ta k'ara tsorata da halin da ta tsinci kan ta,
Don haka ta juya ta fuskan ce su,
Cikin rawar murya da rawar jiki ta had'e hannun ta biyu Alamun rok'o ta shiga ba su hak'uri da ce wa, " Don Allah don Annabi kuyi hak'uri kar ku cutar da ni ku taimake ni na tafi gida hankalin iyayena nasan ya soma tashi zuwa yanzu"
Macen ce ta dube ta ta dube shi ta kwashe da dariya ka na ta ce," karki da mu Baby zaki tafi gida Amma fa ba yanzu ba",
Cikin muryar kuka ta ce ," Don Allah karku cutar da ni ni marainiya ce ina da rangwamen ga ta Baba ya rasu da jimawa don Allah ku kira wanda ya kawoni ya maidani in da ya d'auko ni",
Cikin 'yar dariya irin ta tsoka na matashin saurayin ya taso ya nufo in da ta ke, ya na fad'in, "zaki aure ni?"
Fuskar ta kad'ai ta isa fallasa rud'anin da zuciyar ta tashiga a sanadin tambayar da ya yi mata, nan ta shiga jijjiga kai Alamun A'a ta d'ora da ce wa,"Ni ina da wanda zan aura ni dai don Allah karka cutar da ni",
"to shikenan tun da bazaki aure ni ba bara na ganki na 'yan mintu na sai na maidake gida ko 'yan mata?" Ya d'a ga mata gira ka na ya mik'e tare da ce wa," Teema shigo da ita ciki kawai".
Ko kawa su ka shiga yi ita da Teema kasancewar Ramlatu dirarriyar maca ce kuma k'ak'k'arfa Teema kasa ko da janyo ta tayi sai kokawa su ke Ramlatu ta dage iya K'arfin ta ta angiza ta tafad'i da baya ta Kume sai ji kake k'um!,
ta kwala ma sa kira da ce wa" Akash!",
Ya fito sanye da gajeran wando iya gwuiwa ya na tambayar lafiya? Ya sa hannu ya d'aga ta, haki ta ke sosai don ta ci duka gurin Ramlatu sai da ta zauna ka na ta ce,"Akash bazaka iya da wannan yarinyar ba shawara kawai ka d'auke hankalin ta zai fi ma hankali kwance",
"wannan wacce magana ki ke Teema?, Tsawon awa d'aya ina jiran ta farka don na fi samun nutsuwa sai ki ce na kuma matar da ita?, Gaskiya bazai yuwu ba ni namiji ne in ke kin ka sa bari ki gani".Ko da wasa Ramlat bata fahimci maganar da su ke ba, don ba ta saba jin irin wannan zantukan ba ta dai sha jinin jikin ta ba mutanen kirki ba ne don haka ya na durfafo ta zari wata zungureriyar kwalbar da ta gani zube a gefe ta nunoshi da kwalbar tare da ce wa,"Kana k'ara taku d'aya zan fasa maka kai da wannan!"
ko gezau baiba ya zo har gaban ta ta kuwa mako masa ya tare da hannu kwalbar ta fashe ta yanke shi a hannun nan jini ya b'alle, ya sa hannu ya kwad'a mata mari ta zube a k'as! Ya had'a hannayen ta guri d'aya ya rik'e da hannun sa d'aya ya shiga jan ta a hakan.,
ihu tashiga yi ta na dagewa ta na k'okarin kwace wa amma ina k'ashin ba d'aya ba ne, a k'ofar d'akinne ta dage ta kwace hannu d'aya ta na kwala ihu ta na kiran wacce ya kira da Teema" wayyo Allah na Teema kizo ki kwace ni karki bari ya cutar da ni nifa maca ce 'yar uwarki ki taimake ni don Allah",
Hannu ta ke mik'awa Teema sai taji kamar ta kama hannun yarinyar amma ta kasa har ya shiga d'akin da ita ya maida k'ofar ya rufe...,
Tunda ya shiga da yarinyar ta kasa tsaye ta kasa zaune ihun ta ya d'aga hankalin ta haka nan taji bata kyautawa yarinyar ba, ta na nan tsaye ta na zarya a falon ta na jiyo ihun ta to babu yanda zatai tasan halin Akash duk yarinyar da ta shiga hannun sa baya saurara mata babu Abin da za ta iyai mata,
Ta na wannan nazarin ta ji ta kwalla k'ara sai kuma ta ji shuru,A zabure ta nufi k'ofar d'akin ta shiga bubbuga masa,"haba Akash wai ya haka ne karfa ka kashe y'ar mutane mu shiga uku ka kyale ta haka!"
Ya na bud'e k'ofar ta fad'a d'akin idon ta akan yarinyar da ke kwance tamkar matacciya da Alama suma ta yi, kayan jikin ta duk sun ya ge da Alamu ta k'arfin tsiya ya farke su.,
Bata tab'ajin tausayi irin wanda taji yanzu ya tsirga mata ba,hawayen da ya d'isa saman kuncin ta ya sa ta k'ara yardar wa kanta taji tausayin yarinyar.,
Hannu ta sa ta share hawayen ta ta nai masa wani mugun kallo tare da ce wa"ka kyauta Akash! Ka kyauta!, "ji yanda kayiwa yar mutane kana da imani kuwa Akasha?"Cikin mamaki ya shiga duban ta,"Teema wacce magana kike ne sai ka ce yau aka fara?".
"nidai ba wannan ba bani mukullin mota na kaita Asibiti",
tab'e baki yayi ka na ya ce," gashi nan ki kaita gurin Dr na ya dubamin ita kuma ki tabbatar kin dawo min da ita nan don ba yau zan sallame ta ba sai jibi ko ma gata",
cikin masifa ta watso masa kallo" ban gane ba",
"hmm zaki ganene in kikai kuskure kin jin Abun da nace miki, ni yanzu tafiya zanyi Dady ya kirani d'azu kiran gaggawa ya ce kome nake na ajye na tafi katsina a yau ya na son ga nina don haka kwana zanyi acan bazai yuwu na dawo yau ba sai gobe ki kula karki sake a samu matsala",Ajiyar zuciya tayi,"hmmm shikenan kawai zan kula da ita amma don Allah ka dawo goben",
Nan ya shirya a gurguje yabar gidan kan ya tafi ma saida ya k'ara jaddada mata ce wa,"ki kula ina sonta",jijjiga kai tayi kawai, ya na futa ta shiga band'aki tayi wanka ta sanya wa Ramlatu doguwar rigar ta wacce ta d'ora a saman kayan da Akasha ya yayyaga mata, ta futa ta nemi taimakon mai gadin gidan suka sata a mota ,
sai da tayi tafiya mai nisa sosai ta kusa shiga rijiyar zaki sannan ta tsayar da motar ta koma baya ta bud'e murfin ta turo Ramlatu a hankali don karta fad'i har saida ta ga ta dira sannan ta futo ita ma ta gyara ma ta kwanciyar ta sai ta ta in da mutane zasuyi saurin ganin ta ka na ta koma mota ta harba kan titi tayi tafiyar ta...***
Tarrr! Ta sauke idon ta a kansa ta k'are masa kallo dogo ne bak'i mai saje, ta ke surar wancen ta dawo mata shima dogo ne mai saje amma shi wancen fari ne sakamakon wannan da ya kasance bak'i....
"Sannu Ramlatu ya jikin naki?Allah ya sawake ya kiyaye gaba"
Har zuwa yanzu kallon sa ta ke takasa sarrafa bakin ta balle ta tanka masa.kubiyo ni
[11/
YOU ARE READING
MAI GASKIYA
Short StoryMai gaskiya labarin wani matashin saurayine namijin duniya wanda yayi jahadi akan Ramlat, wacce ta kasance yarinya marajin magana mai mummunar ɗabu arnan tayin lift wanda yayi sanadiyar tarwatsa rayuwar ta.