Chapter one

384 23 2
                                    

ZULAIKA ce ta fito da Gudu tana fadin mama dan Allah ki siyo mun farin belt na mata, mama ta kalli zulaika tace kin cika rigima murmushi zulaika tayi tace kiyi hakuri bazan Kara ba, mama ko kallon ta batayi ba tace naji... Zulaika ta shige cikin gida tana tsalle tsalle. Hajiya aisha da abokiyar zaman ta suka wuce kasuwa.
Labarin zulaika da mahaifanta..
Zulaika yar shekara 15 ce Wanda suke zama a garin abuja (gwarinpa) mahaifin ta Alhaji Ameen hussein Yana aiki ne a SEC (security and exchange commission) matan sa biyu Hajiya Aisha(mahaifiyar zulaika) da hajiya Fatima(aunty) su biyar ne wurin mahifinsu. Hajiya aisha tana da yara biyu Yaya sadiq se autansu zulaika itakuma Haj. Fatima yara ta uku, Abdul jalal, Muhammad da Idris. Ita Kadai ce mace wurin mahaifinta, Hakan yasa Alhaji hussein Yana rikon yaran yan uwansa Alhaji zubair da baba faruq, maryam da Amina... Alhaji hussein mutumin kirki ne Wanda kowa ke alfahari da shi agida da waje.. Haifaffen dan Zaria ne Anan ya hadu da mahaifiyar zulaika har Allah yasa sukayi aure... ***
A dai -dai karfe 6:00pm hajiya aisha(mama) suka dawo kasuwa zulaika na jin hon din mota ta fito da Gudu tace sannnunku da dawowa suka amsa da yawwa bata kara fadin komai ba, sai ta koma inda mama take a shagwa6e tace mama kin siyo mun? Mama tace ban sani ba yaya sadiq ya kalli zulaika yace katuwa dake har yanzu baza ki bar shagwaban nan ba ta turo baki bata ce masa komi ba... Mama ta ciro belt din ta mika mata cikin farin ciki ta rungume ta tace thanks mum! Ta dauki Wasu kaya ta shiga dasu ciki...
Zulaika yarinya ce mai hankali, Wankan tarwada ita ba fara ba kuma ba baka bace, Idanunta manya gasu farare gashin kanta Dana ido kuma tabarkalla.. Tsayin ta average ne... To cut it short zulaika yarinya ce kyakkyawa, mai ilimi da tausayi, saboda Duk Wanda zai zauna da ita ko na second daya se yayi burin kara kasancewa da ita duk inda taje ana yabawa da halayenta sosai.

Chapter 2 loading....

ZULAIKA(A hausa story💖) Where stories live. Discover now