Chapter 2

212 12 1
                                    

Zul's POV :
Yau Sunday mun kusa komawa makaranta, yaya sadiq  ya karbo mana dinkin uniform dinmu, ya siyan mana new books har na kosa gobe tayi don nayi kewan kawaye na shukura da basma, nayi wanka nayi sallan isha nabi lafiyan gado daman kullum bacci na nakeyi da wuri.. Da sassafe na tashi,  nayi wanka nayi sallah, sannan na sauka Kasa don yin breakfast ganin Mairo(yar aikin su zulaika) bata gama ba naje na gaida mama da aunty na wuce dakin baba don in gaida shi na fito Kenan na hadu da yaya sadiq Nace masa ina kwana? Ya amsa da lafiya qalau,  and kigaya ma sauran  Duk Wanda be shirya ba zan tafi abuna,  nayi dariya Nace Toh yaya.. Na koma Kasa don yin breakfast yaya sadiq ya shiga dakin Baba.
writer:
Dai dai 7;30am suka kai makaranta lokacin Ana assembly principal tayi welcoming dinsu back...Duka daliban cikin farin ciki sukayi hanyar classes dinsu,  zulaika ta shiga ss2. Suna shiga class suka rungume  juna da kawayenta se labari suke har saida malama ta shigo ajin  kowa ya natsu.
Haka ranar ta kare Duka teachers sun shigo, Ana tashi driver dinsu Yazo ya maida su gida.
A kwana a tashi su Zulaika sunyi 7weeks da komawa school don har an fara musu maganan jarabawa.
Yau Friday, yar ajin su Zulaika tayi birthday ko ina an bata,  class din yayi datti sosai,  English teacher dinsu ta shigo tace kowa yayi kwashe  dattin  dake kusa dashi ina kallon zulaika itace farko da ta fara dauke  abubuwan da ke kusa da ita ta kai dust bin, Kowa ma yayi hakan.. Malamar  tace su ci Gaba da tsayuwa saboda 6ata class din da sukayi,  Tana tafiya cikin class din dai-dai kujeran zulaika ta tsaya jimm kadan se ji zulaika tayi an Mare ta, ta gigice cikin tashin hankali don ko tamanta rabon da a taba lafiyan jikinta, Cikin kuka da rudewa ta kalli matan don batason abun da tayi ba. Malamar, cikin masifa  tace me ya hanata picking seat dinta don taga paper kusa da seat din,  Cikin harshen turanci zulaika tace ita ta fara picking,  bata karasa magana ba hawaye ya fara futowa daga idanunta,  kawai fita tayi daga ajin tanata kuka mutane se tambayan ta suke abun da ya faru bata iya magana ba ta je ta wanke fuskarta a waje, malamar ta kusa gamawa Kenan zulaika ta dawo class din ta zauna. Teacher din tazo tana bata hakuri amma zulaika kuka kawai takeyi. A lokacin taji babu Wanda ta tsana irin matannan Ana tashi ta dauki jakarta ranar yaya sadiq Yazo daukan su daga makaranta.

Cikin motan ma kuka take tayi yaya sadiq ya kalle ta yace menene? Ta gaya masa abun da ya faru ransa a bace yace yaushe akafara Duka a school dinku? Da yaransu ne za su iya musu hakane? Kiyi hakuri by Monday zan je school din naku ya shafa kanta yace sorry dear kinji? 😱 daga masa kai kawai tayi ta cigaba da zubar da hawaye, Suna kaiwa gida dakinta ta wuce.  Mama ta kira su dinning  don cin abinci zulaika tace ta koshi.  Nanne suke gaya wa mama Abun da ya faru,  Ran hajiya aisha yayi matukar 6aci tace Muhammad ya dauko mata hijab yanzu zata wuce school din yaya sadiq ya shigo Yana bata hakuri yace hajiya ki Bari monday zanje school din sun tashi yanzu ai,  Nan fa tanata fada don tasan zulaikan ta baza tayi abun da ze saka a dake ta ba. Alhaji hussein Yana dawowa bema sani ba yace a kira masa yar mama, maryam ta ruga da Gudu tace aunty zulaika daddy na kira ta amsa da Naji. Tana zuwa a parlour ta same mahaifinta yaga idanunta sunyi manya kuma sun koma ja, Cikin tashin hankali yace yar mama? Bakida lafiya ne? Nan wani hawayen ya tsinke mata ta fara sabon kuka... Muhammad ya gaya masa abun da ya faru, Hmm ni kaina Alhaji hussein ya bani tsoro Yana ta fada yace kiyi hakuri auta Monday zanje school din naku kinji?  Yaya sadiq yace ka Bari in na aje su zanje inyi musu magana Daddy yace Haba! I'm going there on monday! Its my daughter we are talking about, in kaje me zakace musu?  Yaya sadiq be Kara cewa komi ba.  alhaji hussein yace zo yar mama kinci abinci? Tace a'a ranar tare da babanta suka ci abinci bayannane naga zulaika ta saki jikinta...

Lemme pause here 📌
Anticipate for chapter 3

ZULAIKA(A hausa story💖) Where stories live. Discover now