DAYA

13.6K 470 24
                                    

A tafe suke suna zambada sauri, kasancewar lokacin sallar magriba daya gabato, gashi ita aikin dake jiranta a gidansu yafi karfin lokacin datake dashi a kowace rana. Kara jan hannun kawar tata tayi domin su tsallaka titi, dan kuwa masallacin unguwar har sun fara kiraye kirayen sallar magrib.

"Wai Zeenah kinata jana, bakiga yan kilisa suna dawowa ba? Ko so kike su bugemu kuma su buge banza?" Fadar Zainab cikin murya mai sanyi da kuma rawa rawa. Kasantuwar yau alhamis, iyalan sarki da abokansu sukan fita kilisa duk ranar, sannan kuma a wannan lokacin suka saba dawowa-kuma kowa yasan halin dan sarki wanda yake zama gidan a yanzu, bawai ya cika mutunci bane, tsaf zai takesu da doki ya kara gaba.

Togewa tayi waje daya, tana galla ma kawar tata harara, wacce take cike da takaici. Ita wani sa'in har haushin saukin hali irin na Zainab take, komai nata shiru shiru ga hakurin tsiya, itama tanada hakuri amma fa ba irin na Zainab ba, mutum sai kace babu zuciya kirjinshi!

"Kinga Zainab ni ban shirya jin wannan wa'azin naki ba. Ta yaya zasu bugemu ne wai? Wallahi da kau anyi ruwan bala'i!" Cike da masifa Zeenah ke magana tanata harare harare.

"A kofar gidan sarkin zaki fada da dan gidan? Zeenah ni halinki yana bani tsoro wallahi. Wai ke baki taba hakuri da rayuwa?" Zainab ta kara tambaya, dan zuwa yanzu dawakuna sun fara zarya bakin titin daze sadaka da gidan sarkin Katsina.

"Kinga har sun dawo ko? Da tun dazu muka wuce ai da maganar batakai tsawon haka ba. Dan Allah ki taho mutafi, keni uniform din islamiyyar ma takura mani yake," Zeenah ce ke magana tana kara kallon zumbuleliyar hijabin jikinta. Musabaqa zasuyi ta Al-qur'ani mai girma, hakan yasa ko ranar Alhamis da juma'a suke zuwa domin kara tabbacin haddar tasu tana nan kuma komai yaji babu gargada.

Hannunta taja cike da masifa amma Zainab ta toge "Zeenah ji dawakunan sunfi na dazu yawa! Ki tsaya su wuce mana dan Allah!" Zainab ta furta da yar murua me karfi, wanda zata nuna alamun taji tsoron ganin dawakan.

Kallon gefen titin tayi sai taga tawagar abokan dan sarki na uku ne, shine ya dawo hutu wannan satin, dan yayyunshi biyu sunyi aure suna zama kasar waje, dama shine yake zuwa akai akai. Hararar mutanen tayi ta kalli Zainab, "Ke na rantse da Allah bazan jira wadannan yan rainin wayon ba, Zainab kalli yadda suke tafiya kamar basu san taka kasa, suma dawakan hada iskanci ai_yau aka fara tafiya dasu? Abu taku daya daya."

"To nidai ki tsaya kiyi hakuri su ida wucewa, kar kija muyi kwanan asibiti," Zainab ta furta, amma Zeenah sakar mata hannu ma tayi ta kara kallon sashin dawakan, dan kuwa wasu har sun fara shiga gidan sarkin. "Zaki wuce ko bazaki wuce ba? Kinsan dai inada abun yi." Ganin kamar Zainab zata bata mata lokaci yasa ta figi Alqur'aninta daga hannun Zainab din ta durfafi titin nan, kowa yana harkar zuwa masallaci, ita kadai ce tsakiyar titin nan, dan kuwa har masu motoci suna jiran dawakan su ida shigewa kafin su kama gabansu.

Wani burki taja jin hajijiyar doki da gurnaninshi a gabanta, kiris ya rage bai bankadeta ba, dan sai gurnani yake yana san kamu hijab din tata-danma yadda ake juya dokin ya nuna tabbas na saman dokin yasan hannunshi. Dafe kai tayi ta dora Qur'aninta sama, dan akwaita da tsoron irin halittun nan, kawai fuska take ta nuna bata damu ba.

"Ke malama baki ganin kowa ya tsaya sai mun wuce, sai ke zakakka me kafar sauri shine zaki wani wuto ko? Idan aka takeki an banza wallahi!" Daya daga cikin na gefen wanda dokinshi yake saitin kanta yayi magana.

Zeenah bataji ta kyale, bakayi da ita ba balle kayi da ita, duk tsoron dokin nan dake kura mata ido bai hanata dagowa cike da masifa ta galla mashi harara ba "To sannu dan gidan ayi jikan nasaba, kaine me baki yen yen yen, shi wanda ya kusan bugenin baida bakin magana ne sai kai? Ko kurma ne?" Daga idon da zatayi, idanuwanta suka sauka kan na wani saurayi, wanda ya kafeta da idanu, daga ganin fuskarshi kaga alamun bacin rai.

Abokin data zaga ne ya rike baki cikin mamaki, dama akwai mata marasa tsoro haka? Tana gaban gidan sarki take fadan irin wannan magana akan danshi? Lallai yarinya. "Ke baki da hankali ko? Idan wannan ya so sai ya badda ke da danginku kaf daga Katsina, kuma wallahi ta zauna. Sakarya kawai!"

Wata shewa Zeenah ta saki, tama manta da wani zancen gida ko kasancewarsu tsakiyar titi. "To masu bakin magana, idan ni sakara ce dan nayi magana kan abunda yake gaskia, kai kuma ace maka hotiho ko? Wanda yake dan kaleren masu uba, andaiji kunya wallahi. Kuma bari kaji, ba daga Katsina kadai zai fiddamu ba, ai bai isa ba tunda muna iya zuwa kano mu zauna, ya fiddamu daga kasar gaba daya in yaso, kaga ko anan sai mu koma Niger, anyi ba'ayi ba dai." Bala'i take sosai tana galla masu harara, ita ta tsani iskancin ya'yan masu kudi, ai ba gani sukayi tazo tana rokonsu ba balle suce zasuyi mata iskanci ko? Yara sai dan banzan rashin sanin darajar dan adam.

Yunkuruwa yayi zai sauko daga dokin amma shi yariman ya hanashi "Isma'il karka sauka mana." Abunda ya furta kenan cike da dauriya, dan maganar bawai saukin fitowa takeyi daga bakinshi ba.

Wanda aka kira da Isma'il ne ya kalleshi cike da tsananin mamaki, dan kuwa suna iya awa biyu zaune baice masu kala ba, amma yau kan wannan yar maganar ya tanka, lallai yarinyar nan ta kaishi makura.

"Amma Aahil kana ganin yarinyar nan sai kawai a kyaleta? Zan iya kiran dogarai su tafi da ita fa." Bai ida rufe baki ba ta yanko mashi maganar da saida yaji kamar ya sheketa.

"San a sani gaida uwar miji a kasuwa, ai basai ka fito fili ka furta cewar zaka iya kiran dogori ba, daga ganinku saman halittun Allah sannan kuna niyar shiga gidan sarki ai ya nuna akwai sarautar ko bawan Allah? Dama kabar masu abun a jini sunyi magana, dukda koshi yaman ba kyale shi zanyi ba!" Tana kaiwa nan taji an dafata, juyowar da zatayi cike da masifa sai taga Zainab ce a rude tana girgiza mata kai, fizge hannunta tayi tana hararar su baki daya.

"Zainab ni iskanci ne ban cika so ba. Naga titin ai ba nasu bane ko? Dan zaka tsallaka sai kuma ace baka isa ba sai dawakai da na samansu sun wuce? Wallahi basu isa ba, kuma da an bugeni na rantse ba yadda zan ba!" A karo na biyu idanunsu ya hadu dana Aahil, harara ta banka mashi kafin taja hannun kawarta suka wuce, tare da buga uban tsaki.

Isma'il ne ya kalli Aahil yace "Muje Aahil, in kere na yawo zabo na yawo wataran zasu hade, amma yarinyar nan bazata mana iskanci tasha lallai ba." Ko kallan inda yake baiyi ba kawai ya kada linzaminshi suka karasa gidan sarkin, dan zuwa yanzu har mutane sun taru suna kallon me bakin data tsaya tana maidama Yarima magana, bama susan ba dashi akayi fadan ba.

Tunda suka baro bakin titin Zeenah ke masifa har suka karaso kofar gidansu, dama makwabta ne ga gida ga gida. "Zeenah dan Allah ki rika daukar komai da sauki mana, ni banga abun masifa a can ba, karki jawo ma kanki wani bala'in fiye da wanda kike ciki fah." Hannuwan Zainab saman kafadun Zeenah take magana cike da tausasawa.

"Zainab sun dauka mulki shine komai, amma wallahi they're wrong. Ni ba kowa bace, amma kuma insha Allah ba'ayi mahalukin dazai man iskanci in kyale shi ba, ke kofa sarkin da kanshi!" A tare suka fashe da dariya, dan ita Zainab wani sa'in halin Zeenah har mamaki yake bata.

So dayawa mutane suna mata maganar yadda take hakuri da halinta, amma ita bataga aibu a halayyar Zeenah ba. Yarinya ce mai kirki da sanin ya kamata, abu daya ne bata dauka; raini. To fa duk yadda kuke da ita, kuma duk kankancin rainin daka mata saita balbale ka tas!

"Kinada halin dariya, Zeenah. Bari inje inyi sallah sai in shigo in tayaki aiki muci abinci ki karbar mani haddata kinji? Karfa inzo kice ke baki yarda ba labari zamuyi," Zainab ta kara jaddawa, dan tasan halin Zeenah sarai. Ga kwakwalwa gareta, sai yasa inba a islamiyya ba bata cika wani karatu ba sosai, Allah ya bata.

Saida tayi yar dariya kafin ta kalli Zainab, "Eh to, kinsan dai yau kawar taki tayi jarumta dayawa, bai zama lallai in iya bude Qur'ani ba dan kar zuciyata tayi sanyi azo mana sammaci Zeenah ta rasa bakin kare kanta. Na duba dai in gani!" Dukan da Zainab ta kawo mata ne ta goce tana dariya.

"Zeenah kin bani wallahi, wato tsabar masifa na cinki bakisan kiyi karatun Qur'ani bala'in ya tafi ko? Allahu yahdiki. Nasan Mama nacan na jira, kije ko tana bukatar wani abu, saina shigo." A hankali Zainab ta dan rungumeta kafin sukama juna murmushi, wanda hakan ya kasance al'adarsu, basu iya rabuwa sai anyi labari kofar gida sannan su rungumi juna da murmushi.

"To Zee din Zee, sai kinzo." Daga haka suka kara dariya kafin ko wacce ta shige gidansu, amma idanu masu kala da zaiba da kalar sararin samaniya na yawo cikin kwayar idan Zeenah Kabir Muhammad.

A JINI NA TAKEWhere stories live. Discover now