TARA

3.5K 228 0
                                    

Koda ya gama warming din abincin tsayawa yayi cikin kitchen din dan ya bata dan lokaci. A tray ya zuba abincin ya nufa dakinta, shi tsoro ma yake kar ta kara suma dan yadda yaga yanayin ta ta galabaita. Yana shiga Zeenah ta futo daga wanka daure da towel, bata lura dashi ba, a hankali take taku dai daya dakyar.

Dauke idanshi yayi daga ganta yaje ya ajiye tray din saman bed side drawer. Direct wajen drawer din kayanta ta nufa, dakyar take taka kafarta tsabar jiri jirin da take gani, danma drip din da aka saka mata ba karamin taimaka mata yayi ba.

Kamar baya so haka ya kalle ta, "Ki saka kayan sai kici abinci. Kinyi sallah ko?" Fuskarshi inda take yake fuskanta amma idanunshi ba ita suke kallo ba.

Juyowa tayi ta kalleshi, da kyar tayi nodding kanta, "Zanyi maghrib da isha'i yanzu. Abincin kuma na koshi." Ta furta a hankali lokacin da take saka doguwar rigar baccin data fiddo. Ita tama manta wai yanayin jikinta ko kuma waye gabanta, burinta bai wuce ta sauke sallolin dake kanta ba ta koma bacci, ji take zata iya kwana biyu a tsaye tana bacci tsabar azabar data sha.

Fita yayi daga dakin baice komai ba, bayajin dadin yanayin da yake ganinta. Sannan kuma wannan sanyin jikin nata bai sa ba dashi ba. Saida ya bata kusan minti talatin kafin Bilal ya dawo cikin dakin, inda ya isketa kwance a jasa inda tayi sallah.

Gabanshi saida ya dan fadi kafin ya karasa inda take, "Ki tashi kici abinci kisha magunguna, Insha Allah gobe da kin farka zakiji karfin jikin ki." Cikin bacci Zeenah taji yana tadata. Dukda haushin shi da kuma jiran warkewarta da take dan ta ci mashi mutunci sai taji dadin nuna damuwar shi da yayi, dan ita tunda yake bata saba wai dan bata lafiya a duba ta ba, ita take kidanta tana rawarta, iyakarta da Mama ido.

A hankalj ta mike tana murza idanu, hannu ya mika mata alamar zai taimaka mata ta mike, babu musu ta mika mashi nata dan kuwa jikinta ko ina ya mutu. Kan gadon ya maida ta ta zauna kafin ta jingina. "Abinci ya fara sanyi, ko nayi miki warming?" Ya tambaya, girgiza kai kawai tayi tana lumshe ido, ita da yasan irin baccin da takeji wallahi da ya fita ya bata waje.

Ganin yanayinta yasa Bilal yasan koda ya aje mata plate din a gabanta ba ci zatayi ba. Debo abincin yayi da spoon kafin yakai bakinta, da mamaki fal cikin idanuwanta haka ta bude baki ta karba. A haka har saida ya tabbatar ta koshi kafin ya ajiye ya ballo magunguna, "Karbi wannan kisha, sai ointments din. Zaki iya shafawa?" Dakyar yake maganar, dan jinshi yake kamar a kaya yake. Amma kuma halin da take ciki ta cancanci ya tsaya duk sarautar shi ya duba ta.

"Bazan sha wani magani ba, zuwa gobe zanji sauki. Bacci nakeji." Da muryar shagwaba take magana, kome ke faruwa dasu yau sabo me wanda kuma basu taba tsanmani ba nan kusa. Haushin shi kasan ranta, kuma masifa takeso ta balbaleshi da ita amma bata da karfin yin magana mai tsawo.

Magungunan yakai bakinta babu musu dole ta karba tasha kafin a hankali ta zame ta kwanta saman cinyoyinshi. Ita bata ma san kan abunda ta kwanta ba, nan take bacci ya dauke ta. Bilal ya kusa minti biyar yana kallon yadda take bacci hankali kwance kamar batayi pillow da cinyar Dan Sarkin katsina ba.

Ointments din ya dauko yana kallo, shi kam wallahi ko hannunta bazai iya tabawa ba. A hankali ya maida kanta saman pillow kafin ya lullube ta da blanket. Ac din dakin ya rage mata kafin ya kashe wuce ya fitar da trays din waje. Yana zuwa daki wanka yayi kafin yaga missed calls din Isma'il.

Kiran shi yayi sai can ta kusa tsinkewa Isma'il ya dauka. "Kai to ya? Jikin nata wai ya yake? Ni baka cemun komai ba dazu." Maganar da Isma'il ya farayi kenan.

Saida Bilal ya girgiza kai tare da shafa sajen fuskarshi kafin yayi magana. "Isma'il gobe da safe zanje gidan yarin. Duk wadanda suka hora ta zansa ayi musu daurin shekara daya da horo mai tsanani. Kasan ruwa kawai suka bata kwana biyun nan? Kai, abun is worse. Zadai muyi magana goben."

"Kaga abunda nake fada maka ko? Wallahi kai aka raina ba Yarinyar can ba. Dan babu halin a hukunta ka shiyasa ake labewa da matarka tayi rashin kunya. To saida safen." Da haka sukayi sallama Bilal ya shiga yayi wanka kafin ya kwanta.

Tun daga ranar Zeenah bata kara ganinshi ba itama kuma bata damu ba. Kamar yadda ya fadi haka yaje ya aikata a gidan yari, bayan Fulani taji labari saidai tayi murmushi kawai batace komai ba. Yaro yana wasa, baisan wuta ba sai ya taka. In bacci darajar aure, dan baiwa kaskantacciya kamar uwarshi har ya isa ya taka maganarta?

Kusan sati kenan har Zeenah ta warke ta murmure, ranar da marece Waziri ya aika aka kirata, nasiha ya mata sosai kuma ya kara mata nuni da yanda ake zaman gidan sarauta dole saida dubura da ladabi koda kuwa na karya ne. Ya umurceta akan duk abunda Fulani ta sakata daga yanzu karta kara kauce ma maganganun ta kuma karta kuskura ta kara maida mata magana. Godiya ta mashi ta koma gida.

Ba'ayi kwana biyu ba da maganar su aka aiko ana kiranta daga bangaren Fulani. Shiryawa tayi tsab taje yau cikin falonta ta iske ga. Zama Zeenah tayi kafin ta gaida ta da kyar, dan ji takeyi kamar ta shaketa ta mutu kowa ma ya huta. Amma idan ta tuno kalaman waziri sai ta danne zuciyarta.

Wani magani Fulani ta miko mata cikin leda. "Na tuntuni Yarima akan matsalar ku sannan yamin bayani akan abunda yake damunshi. Na saka an nemo mashi maganin gargajiya, daga yanzu zuwa wata biyu ina jiran sabon labari daga wajen ki. Wannan maganin a abinci zaki rika saka mashi kullum." Faga ita har Fulani babu wanda ya tado da maganar gidan yari, hakan kuwa ba karamin sausaka ma Zeenah yayi ba wajen danne fushin dake cin ta.

"Nayi magana dashi daga yanzu a wajenki zai rika cin abinci. Baisan da maganin ba dan Yarima baya kaunar magani a rayuwarshi. Ki kula kar ya gane inba haka ba bazai rika ci ba." Tana gama magana Zeenah ta jinjina kai alamar ta gane kafin ta tashi ta koma bangarenta.

Daga ranar kuma kullum ta tashi dafa abinci sai ta saka mashi maganin a nashi, kuma kamar yadda Fulanin ta fada yanzu kullum safe, rana dare a gidanta yake cin abinci. Bata fitowa balle tasan ko tare da Isma'il suke ko akasin hakan.

Tun daren jiya yake jinshi ba daidai ba, wani irin mugun ciwon ciki ne yake neman hallaka rayuwar shi. Shi bai taba irin haka ba, gashi zurfin ciki bazai barshi yaje yaga likita ba ko kuma ya fadama koda Isma'il ne. Yamma tayi lis yana zaune a falo yana kallo yaji cikin ya murda mashi, kamar wasa tun yana kishingide saman kujera ya koma ya rungume ciki, karshe ma kasa ya zauna yana murkususu. Dakinshi ma ya kasa komawa balle.

Duhu duhu yake gani tsabar azabar dake cinshi, kamar daga saman yaji sallamar Isma'il, baisan sadda yake Alhamdulillah cikin ranshi ba. Da hanzari Isma'il ya karasa wajenshu yana tambayar ko lafiya? "Ciki na." Abunda Bilal kawai yake iya fadi kenan.

Taimaka mashi yayi ya koma daki kafin ya kira doctor cikin gaggawa, allurar da zata sawwaka mashi ciwon cikin yayi daga nan Bilal ya samu bacci ya dan daukeshi. Fita sukayi da doctor din inda Isma'il yake tambayar menene matsalar? Shi bai tabajin Bilal yayi complain akan ciwon ciki ba.

Doctor din cewa yayi shikam bazai ce ga abun dayake damun Bilal ba amma ya debi jinishi zaiyi test yanzu daya koma asibiti, koma menene zai kira ya fada masu. A haka sukayi sallama. A nan dakin Bilal Isma'il yayi sallar maghrib dan bayaso ya tashi baiga kowa kusa dashi ba.

Har isha'i kafin Bilal ya farka yana yan kalle kalle, da sannu Isma'il ya taimaka mashi yaje yayi wanka kafin yayi sallolin shi. Bilal ya saba da kulawar Isma'il in bashi da lafiya, dan tunda suka tafi makaranta shine uwarshi da ubanshi. Yana zaune saman sallaya kiran doctor ya shigo, a natse ya fara magana, "Ranka ya dade da fatan kaji sassaucin ciwon?" Um kawai ya iya ce mashi, dan ko bude baki bayaso yayi.

"A binciken da nayi na gano cewar akwai maganin da ake saka maka a abinci wanda shi zai hana jikinka yayi producing kwayoyin haihuwa. To dama maganin kodai ya hana ko kuma ya saka production din sperm cells din yayi yawa, a case dinka gaskia ya kara boosting hormones din dake producing kwayoyin haihuwar ne har suna nema suyi maka yawa a jiki wanda dan dole ko kaso ko baka so ba zaka bukaci iyalinka. Shawarar da zan baka itace..." Dama wayar a speaker take tunda Isma'il ne ya dauka. Datse call din gaba daya yayi ya mike tsaye.

"Ina zakaje kuma Bilal? Waye yake saka maka maganin da bazaka haihu ba?"

"Isma'il kusan wata biyu banacin abinci ko ina inba na wannan yarinyar ba. Wajen ta zani ko ta fadaman wanda ya sakata ko kuma wallahi idan na tashi aikata gidan yari sai tayi shekara ba kwana biyu ba." Yana fadin haka ya fita daga dakin gaba daya. Isma'il bayanshi yabi, amma shi fita yayi daga gidan ya nufi unguwar su. Abun ya daure mashi kai.

A JINI NA TAKEWhere stories live. Discover now