HUDU

3.5K 241 8
                                    

Nan da nan hankalin dogarawan dake gadin fada yayo kansu, nema suke su fara dukanta ita kuma ta fara ihu tana fadin wajen Babanta yazo. Hayaniyar da sukeyi ita ta janyo hankalin mutanen fada har sarki ya aika da a shigo da duk wanda suke hayaniyar. Shigar dasu ciki akayi, ganin Bilal da kuma Isma'il ga Zeenah yasa hankalin Baba yakai kololuwa wajen tashi, yasan rashin kunya ta musu.

Mai martaba kuwa mamaki yake anya da Bilal ake hayaniyar nan? Dan yasan halin Bilal sarai sai ka saka mashi hannu a baki yayi awanni baima san ka saka ba. Dukansu saman guiwowinsu suka zube. Waziri, wanda ya kasance shine mahaifin Isma'il ya fara tambayarsu abunda ya faru. Isma'il ne yazo zaiyi magana Zeenah tayi saurin katseshi.

"Kul! Fadi ba'a tambayeki ba. Ki natsu kisan a inda kike diyar talakawa!" Wani bafade ne ya daka mata tsawa. Waziri ne ya daga hannu kafin yayi magana "Yi maganar ki yan mata. Me yake faruwa?"

Gyara tsugunnin ta tayi, ko kallon inda Baba yake batayi ba dan kuwa tasan tana kallonshi duk wani kwarjinin ta zai kare. "Allah ya baka yawan rai. Mahaifiyata ce bata lafiya take aman jini, ina gudu na shigo masarautar nan dan in fada wa mahaifi na mu samh mu kaita asibiti a kan lokaci kafin na rasata. Kawai sai naji mota ta kusan bugeni, na fadi a kasa har naji ciwo. Shi kuwa wannan yana fitowa ya fara zagina, wai banda hankali ni mahaukaciya ce, ni kuma na maida mashi martani.

A nan na barshi tsaye dan inada abunda yafi kowa da komai mahimmanci. Na kusa karasowa fada kawai naji na juyar dani an kifa man mari, nima na rama. Sai wannan dayan yazo ya kara marina, sai naga suna neman su maida ni wata sakarya, nima kuwa na daga hannu biyu na rama. Shine fah." Tanayi tana nunasu, tsakanin Isma'il da Bilal wanda tunda suka shigo fadar kanshi yake kasa ko sau daya bai dago.

Nan take fada ta hau salati. Anya yarinyar na tasan inda take kuwa? Gaban mai matarba take fadin ta wanka wa danshi maruka har biyu? "Ke yarinya anya kuwa hankalin ki daya? Ki kalla samari kamar Isma'il da Yarima ki maresu? Shi Yarima ma har mari biyu?" Daya daga cikin yan zaman fada ne yayi magana, dan kuwa kowa abun ya masifar daure mashi kai.

Baba me ya dawo tsakiyar fada shima ya tsugunna, "Allah ya taimaki me martaba, Allah ya taimaki waziri. Dan Allah aimun aikin gafara. Wannan yarinya diyata ce, laifi nane da ban bata tarbiyar daya kamata ba. Ayi man aikin gafara, ranka ya dade. Duk wani hukunci da zaa yanke a shirye take ta daukeshi." Magana yakeyi cike da kaskantar da kai wanda hakan ba karamin bakanta ran Zeenah yayi ba kuma karamin bata tsoro yayi ba. Tasan yau babu wanda ya isa ya ansheta wajen Baba sai Allah.

Shiru ne ya kaure a cikin fadar kafin waziri ya fara magana, "Malam Kabiru, iyakar shekarun da muka dauka muna tare bamu taba samunka da wani laifi ba. Tunda ka roki alfarmar a yafe maka a yi sassauci zaayi. Yanzu abu na farko zata basu hakuri, na biyu kuma shine, wanda dalilin babban laifin da tayi na marin Yarima har sau biyu, daga yau har ranar da zatayi aure; zata kasance mai hidimar bangaren Yarima. Duk wasu kuyangu da bayi dake bangaren to a fidda su. Sarkin gida, sai a tabbatar hakan ya faru." Gyada kai suka farayi alamar hukuncin yayi daidai da abunda ta aikata. Ganin irin kallon da Baba yake mata yasa bata bata lokaci ba wajen basu hakuri. Sallamarsu akayi su dukansu, tana fita ta zura da gudu ta nufi gida tana kuka, yau tasan kashinta ya bushe.

Iske Mama tayi har baccin wahala yayi awon gaba da ita. A hankali ta fara gyara mata jikinta ta wanke mata jinin kafin ta zaune gefenta tana risgar kuka. Ita yanzu ina zata saka kanta, ai wallahi gara aikin gidansu sau dubu akan taje tanama wancan izgilin aiki. Kamar saukar aradu haka ta jiyo muryar Baba, jikinta babu inda baya rawa.

"Zeenatu!!!" Ya fada cikin karsashi, wanda hakan yayi sanadiyyar tayar da Mama daga baccin wahalar data fara. Jikinta babu inda baya rawa haka Zeenah ta kama hanya ta fita daga dakin, ko kafin takai guiwowinta kasa bulalar Baba takai mata su. Yau duk yadda takai da dauriya dole tayi kuka bawai dan ranta yaso ba. Dukan Baba yau babu imani a ciki.

Ranar kwana tayi tana kuka, tun Mama tana kallonta alamar lallashi har ta saka mata ido kawai. Karshe data lura Mamar nema take tayi kuka sai ta kwanta kamar tayi bacci amma batayi ba, takaicin irin halin Baba takeyi. Wato koma ya damu data ce Mama tayi aman jini ko?

Washe gari da safe ta tashi tayi aikin gidan kamar yadda ta saba. Saida ta taimakawa Mama tayi wanka ta bata abinci kafin tayi wankan itama tadan ci abinci. Kafin Baba ya tashi ta hanzarta gidansu Zainab ta roketa akan tazo fa bawa Mama abincin rana yau dan Allah, zata fara zuwa yiwa wancan mai fuska kamar garin kunu aiki. Zainab babu kalar dariyar da batayi ba, wai fuska kamar garin kunu.

"Yo eh mana Zee, babu alamar annuri cikin fuskar nan kamar an aiko mashi da mutuwa. Kuma wallahi sai na azabtar dashi aikin da zan mashi." Duka Zainab ta kawo mata amma tayi hanzarin kaucewa.

"Wallahi Zeenah kiji tsoron Allah, kila dukan da Baba ya maki bai gama ratsaki bane shiyasa har kike maganar azabtar wa. Nidai ba rhwana. Ko jinya bazan ba." A haka sukayi sallama Zeenah na komawa gida ta iske Baba yana karin kumallo, yana idarwa ya tasa keyarta suka nufi masarauta.

Bangaren Yarima Bilal aka nufa da ita. Bangare ne mai fadin gaske. Dan kuwa taji labarin ance bangaren mahaifiyarshi ne tun kafin ta rasu, yana yaro ta rasu amma dukda haka bai bar bangaren ba. Shiga tayi ta tsaya a tsakiyar falon, anma wajen gyara babu alamun sarauta a wajen, kamar ba gidan sarauta ba. Cike da bakin ciki ta fara gyaran ko ina. Sai gab da azahar ta gama, dan wasu dakunan har sunyi kura tsabar yadda baa kula dasu. Shi dana bawai san kuyangi mata yake ba, iyakarshi maza.

Sallah ta gabatar kafin taji cikinta ya fara kiran ciroma. Kitchen din ta koma kafin ta girka abinci dan kadan bada yawa ba, dan batasan yazo ace yanasan abinci kuma rai ya baci. Bayan ta gama ta zauna taci ta fito yar harabar domin tasha iska, ita mutum ce mai san yin magana, yanzu ji take duk an takura mata.

Takun mutane taji, da hanzari ta koma falon tana jiran shigowar su. Isma'il ne da Bilal suka shigo, shidai Bilal ana shigowa direct dakin data gani kulle taga ya bude ya shiga, tabe baki tayi. Isma'il ne ya kalleta, saida ya gama zabga mata kallon kaskanci kafin ya furta, "Ke, kije ki dafo mana abinci, pepper soup din kaza sai white rice da miya."

Nunawa tayi kamar bataji shi ba, saima hanyar waje data nufa, wata tsawa ya daka mata dan dole ta dawo tana kallonshi, "Ba magana nake maki ba? Ko kuwa bayan rashin kunyar ke kurma ce?"

"Dallah malam dakata mun. Kaga na maka kala da yar aiki ne? Ko da can da bana zuwa baku cin abinci ne? In zaka kama kanka ka kama kanka, dan wallahi babu wanda ya isa yasakani girki. Ga jollof rice can na dafa, in kunga dama kuci, in bakuga dama ba ku kwana da yunwa."

A harzuke Isma'il ya taso ya nufo inda take, da hannu ya nuna ta, "Ke har kin isa ki kalleni kina fadaman magana san ranki? Na rantse da Allah kibar ganin kinsha lallai jiya, wallahi yanzu zan maki dukan tsiya na barki kwance. Ku wuce kiyi abunda aka sakaki."

Wata irin shewa Zeenah ta saki. Ita yarda yaje hucin ma wata irin dariya ya bata, wai shi nan gani yake har zai iya tsorata ta ko? Lallai wannan baisan wacece ita ba. "Kai bari kaji, na wake daya? Allah ko? To billahillazi ban dafawa. Inma zaka hakura ka daina wani kakaro jijiyoyin wuya to ka daina, dan wallahi albasa hannuna bai rikewa balle har wani naman kaza."

Bilal yana jiyosu daga daki, shi baisan me yake damun Isma'il ba, yasan sarai yarinyar nan yar iskar yarinya ce bawai zatayi abunda ya sakata bane. Dan me zai bata lokacin shi a banza? Tabe baki yayi yana daga kafada.

Gyara tsayuwarshi Isma'il yayi yana nai mamakin karfin hali da jarumta irin na Zeenah. Dan wallahi da wata ce ko kallon banza bazata kara mashi ba. "Ke wai wace irin fitsararriya ce? Na rantse da Allah ki shiga ki dafa abincin nan. To wai ma tsaya, waccan kaskantattar shinkafar kikeso muci ko mi?"

Bata bari ya rufe baki ba ta bashi ansa, "Auu, lallai ma samun wuri. Wanda ko ruwan zafi bai iya dorawa shi zai kira jollof rice kaskantacciya? To sannu jinin sarauta, to sai ku kwada sarautar kuci muga in tana maganin yunwa. Aikin banza aikin wofi." Tana fadin haka ta buga uban tsaki ta fita daga bangaren gaba daya, kai tsaye gida ta nufa, dan kuwa har an fara kiraye kirayen sallar la'asar.

A JINI NA TAKEWhere stories live. Discover now