SHIDA

3.4K 243 1
                                    

Hawaye kawai ke fita daga idanta, tana kallo kawannen su daya bayan daya suka fara fita daga bangaren har ya zama babu kowa daga ita sai Yarima. Shi kanshi ya kasa tashi daga inda yake. Tauna kalmomin Me Martaba kawai yakeyi. Yanzu abunda Mai Martaba zai mashi kenan? Auren dole? Dama duk alkawarin daya mashi shekarun baya da suka wasu bazai taba cika mashi su ba?

Yaji ma a mishi auren, amma ya rasa yarinyar da zai aura mashi sai wannan tambadaddiyar? Shi tunda yake bai taba ganin jarababbiyar yarinya masifaffiya irin Zeenah ba. Gashi bata tsoron kowa balle kuma fargabar hukuncin da zaayi mata idan tayi laifi.

Yana tsaka da wannan tunanin yaji karar shashekar kukanta saman kanshi, dagowa yayi yaga tana kallonshi. Kallo ne mai cike da tarin takaivi da bakin ciki, da kuma dumbin tsana ga wanda akeyiwa shi. "Bilal kake ko wa? To wallahi ka gaggauta zuwa ka warware wannan abun. Inma banda zalinci irin naka kanajin fa abunda suka fada, kai tsakanin ka da Allah duk yau ka ganni balle har ace na baka wani abu a drink?" Dukda yyaddakuka yaci karfinta amma hakan bai hanata masifa ba, gani take idan ta sauke a kanshi zataji rahama a zuciyarta kafin taje Baba ya sauke mata tashi gajiyar.

Yunda ya dago sau daya ya maida kanshi kasa har Zeenah tayi bambotai ta gaji bai kara dagowa ba, karshe ma tashi yayi cike da kasaita ya koma dakinshi, dan har yanzu bawai ya dawo daidai bane ba. Tafi kusan awa daya tana kuka cikin falon nan, bataso akace wannan mai fuskar dawon yaga kukanta ba, amma babu yadda ta iya.

Tana isa gida dakin Mama ta shiga, da kuka take fada abunda ya faru. Kyafta ido kawai Mama tayi tana girgiza kai alamar tayi hakuri ta daina kukan. Ko kafin ta gama nata kukan Baba ya shigo gidan da sallama, yanayin yadda muryarshi take fita kadai ya isa kada wa Zeenah yan hanji. Da karaji ya kira sunanta, jikinta babu inda baya rawa ta kalli Mama wasu hawayen na kara zubu mata.

"Mama wallahi ban aikata abunda sukace ba, amma bazai taba yarda dani ba." Kuka ne yakesan cin karfinta, amma batasan karawa Mama damuwa akan wacce take ciki a yanzu. Tana fita ta iske Baba tsaye ga Anty dasu Asiya sunyi cirko cirko sai rattaba uban salati suke alamar ya gama shaida masu abunda ya faru.

"Yanzu ke Zeenah kwartanci kikaje yi gidan sarkin? Malam shikenan ta zubar maka da mutunci." Har kasa Zeenah ta duka a gaban Baba tana kuka kamar ranta ya fita.

"Baba wallahi karya suke man, yadda kaji na fada a gaban mai martaba haka abun ya faru. Baba ka yarda dani koda sau daya ne a rayuwata." Daga yadda ta kaskantar da kanta zuwa yadda take kuka yasa zuciyar Baba ta karaya, hakan kadai kuma ya tabbatar mashi da tabbas ita take da gaskia.

"Tashi ki tafi, kiyi yan shirye shirye ranar juma'a dai ba fashi." Har ya juya zaiyi hanyar dakinshi ta ruga kasan rigarshi.

"Baba ka taimaka man, wallahi idan akwai wanda na tsana duniyar nan bayan Yarima Bilal yake. Ka taimakeni ka ceci rayuwata kaje ka bawa Sarki hakuri ya janye maganarshi, Baba wallahi..." buge hannunta Baba yayi yana murmushin takaici.

"Zeenatu ban cika san sakarcin ki ba kinji ni? Kin taba ganin inda Sarki yayi magana ya chanza? Ki wuce ki bani waje kafin in chanza maki halitta kinji?"

Cikin wani gunjin kuka wanda yake nuni da babu yadda zatayi da rayuwarta, "Mama fah? Wa zai rika kula da ita?" Bai juyo ba ya bata amsa, "Ko kafin kizo duniya ta rayu, dan kinyi aure bazata mutu ba." Yana furta hakan yayi shigewarshi daki.

Tanaji su Anty suka gama yan maganganun su amma yau batada lokacin kanta balle har ta wani tsaya basu amsa. Su a ganinsu kukan munafurci take. To wanda yake dan bafade da kuma baiwa ya samu auren Yarima kuka na me? Da tsakin bakin ciki dukkansu suka koma daki aka bar Zeenah a tsakar gida.

Gidansu Zainab ta nufa, taci kuka nan ma har ta gode Allah. Sai bayan Isha'i ta dawo gida, inda ta iske Anty ta dafa abincin dare. Nasu ta dauka ta wuce dakin Mama, abun mamaki sai taga hawaye na zuba daga idan Mama. Dakyar Zeenah ta samu ta lallashi Mama kafin a tare tana bata itama tanaci sukaci abincin su. Ajiye tata damuwar tayi a gefe, ganin inhar ta cogaba da nunawa to fa tabbas tana iya hasala ciwon Mama. Cikin kwana biyun nan babu irin kulawar da Zeenah bata bawa Mama ba. Labari kuwa na debe kewa duk ta samu dama sai ta bata shi, har wani lokacin Mama takanyi murmushi har hakoranta su fito. Iyaka idan ta fita gidan tasha kukanta kafin ta dawo, ko Mama ta gane alamun tayi kuka babu baki balle ta tambayeta.

Fulani ce ta aiko da kayan da Zeenah zata saka a ranar juma'a da safe. Dakyar da lallami Zainab ta samu ta saka kayan kafin suka zauna zaman jigum, Zeenah na lura da yadda Mama ke ajiyar zuciya duk bayan yan mintina. Gefen Mamar ta koma ta dan rabu da jikinta duk sunyi shiru babu wanda yake magana. Kamar saukar aradu haka sukaji lasifikar masallacin gidan sarki na na furta, "An daura auren Zeenah Kabir Muhammad tare da Yarima Bilal Kabir Usman akan sadaki naira dubu dari da hamsin. Mai girma Waziri shine wakilin ango ya tambaya, wanda Mai Martaba Sarkin Katsina ya kasance waliyyin amarya ya bayar. Jama'a ku shaida!"

Zumbur ta mike ta fara zagaye dakin gana kiran, "Shikenan na shigo na lalace. Wayyo Allah na Zainab zan mutu na bani!" Kuka takeyi har wasu hawaye suna rasa wajen sauka a samn kuncinta. Dakyar Zainab ta samu ta lallaba ta ta fara jero Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun. Ita kanta bazata kayyace iyakar adadin Innalillahin da tayi ba.

Har yamma babu wanda ya saka wani abu cikin cikinshi tsakanin mutanen nan ukku. Mamarsu Zainab ma ta shigo yafi sau biyar gidan saidai ta bawa Zeenah hakuri ta tashi ta koma. Tsakanin Zeenah da Mama saidai kallo, dan Zeenah tasan akwai abubuwan da takeso ta fada mata.

Gefen Mama ta koma ta zauna a hankali tana kuka ta fara fadin. "Mama magana kikeso kiyi ko?" Mama ta daga mata kai hawaye na zubowa a idanta. Hannu Zeenah ta saka ta goge mata hawayen kagin ta cigaba. "Nasan Mama zakice nayi hakuri da rrayuwako? Na mishi biyayya kar na sake na bata mishi ko? Na kula da kaina kuma, na kasance mai addini da rikon amana..." jin da tayi kuka yana neman tafiya da numfashinta yasa ta tsagaita, ko kafin ta cigaba saidai sukaji sautin algaita yana tashi cikin gidansu, wai anzo daukar Amaryar Yarima Bilal.

Dum! Gaban Zeenah ya fadi, aikau duk yarda Anty tasu banbare Zeenah jikin Mama kasawa tayi. Dan dole ta aika Firdausi ta kira mata Baba da yake kofar gida yana amsa Allah yasa alkhairi. Yana shigowa dakin ya iske halin da suke ciki, kai tsaye inda Zeenah take ya nufa ya riko hannunta, fizgowa daya ya mata ta mike amma hannunta yana rike gam dana Mama.

Yunkurowa Mama tayi kamar wacce zatayi Mama, ko kafin su ankara saidai sukaga ta fara aman jini karshe ma ta fadi a wajen a mace. Duk yadda Zeenah ke kururuwa tana ihu akan Baba ya saketa taje ta duba Mama yaki, saima marin daya sakar mata saman kunci ya fitar da ita ya saka mota. Tanaji tana kallo kuma mata suna ta kabbara ana fadin cewar Mama ta rasu. Har wani ciccijewa takeyi kamar ranta zai fita. Ganin sun fita daga layin gidan yasa taji kamar fitar wani abu daga zuciyarta. Zar zar kawai hawaye ke fita amma bata iya ce maka ga abunda yake faruwa a gefenta ko kuma ga inda ta nufa.

Har aka isa bangaren Fulani batasan anje ba, anan taji suna shaidawa Fulani ai ana ruguguwar fiddota mahaifiyarta ta fadi ta mutu, ko gezau balle Fulani tace Allah ya jikanta. Har sunzo zasu nufa bangaren Yarima da ita kawai ta fizge ta fara gudu, burinta bai wuce taji dumin jikin Mama ba kafin su rufo gawarta, an tasan yau Mama saidai tayi kwanan makabarta.

Tanajin matan nan na binta suna "Kai ku riketa kar ta zare," amma Zeenah gudu kawai take bawai dan numfashi yana shige da fice a cikin kirjinta ba.

Kiran da Fulani ta aika a mishi ya amsa, saidai ya hangota tana gudu tun kafin ya isa bangarenshi, ta gefenshi tabi zata wuce, a nan take ya rikota ya hadata da kirjinta, tana dagowa taga fuskarshi ta fashe da kuka, "Dan Allah Yarima ka barni na tafi. Mamata ta rasu, yanzu yanzu, sunki bari ko gawarta na taba. Yarima kamun rai, Mamata fah!" Ya tabbatar babu hankali a jikinta, karshen zzarewatakai, kuka kawai takeyi ba tare da tasan inda take ba. Da dai bata shigo gidan ba, amma yanzu ko shi da yake mijinta bai isa yace taje gida ba.

Ganin zai bata mata lokaci yasa ta nemi ta fizge daga rikonshi. Bilal gani da gaske hauka tuburan takesan tayi gashi mutane sai kallonta suke yasa ya wanka mata mari, "Ke ki natsu! A masarauta kike ba gidan mahaukata ba!" Yana fadin haka ya rabata da jikinshi kafin yaja hannunta ya nufi bangarenshi, kaf matan tsayawa kawai suna kallon ikon Allah. Zeenah kam kwata kwata babu hankali a cikin gangar jikinta.

A JINI NA TAKEWhere stories live. Discover now