BAKWAI

3.4K 242 2
                                    

A kanta batajin komai haka kuma bata gane komai. Tashin hankalin da take ciki ya wuce misali dan ita kanta batasan ga abunda zatace ba. Saidai gani tayi Bilal ya shigar da ita wani daki, ko kara kallonta baiyi ba yasa kafa ya fita. Wani ihu ta fasa tana kuka kamar ranta ya fita. Zeenah tasan Mama bata mutu ba, dan babu yadda zaayi Mama ta mutu ta barta. Daga baya ma shiru tayi kawai ta zura ma daya daga cikin kayan dake dakin ido, ko hawayen sun daina zubo mata, lokacin da Mama tayi faduwar karshe kawai yake mata yawo cikin kai.

Tayi zaman kusan awa daya batajin yawon farin ciki ko bakin ciki a zuciyarta, ita dai kawai gata nan a zaune kamar wata butun butumi. Kiran sallar maghrib ne ya fara dawo mata da hankalinta, tunda liman ya fara karatun sallah ta fara binshi har saida takai karshen surar ta kuma shiga ta gabanta. A hankali kur'anin da take karantawa ya dinga shiga zuciyarta yana hudu duk wani dutse da yake neman mazauni a ciki. Kamar yadda ake jika soso haka taji zuciyarta ta fara jikewa da wannan jaratun kur'anin. Daya bayan daya wasu hawayen suka fara sauka, tana kuka tana karatun dan ta lura karatun nan kadai zai hana gushewar hankalin ta.

Har suka gama sallah tana zaune. Har lokacin isha'i ya gabato kafin kamar wacce kwai ya fashe mawa ta tashi ta shiga toilet. Ta kusa minti biyar tana watsama jikinta ruwa dakyar tayi wanka da alwalla ta fito. Daga alkyabbar har kayan jikinta sun jike sharkaf da ruwa, wajen da taga drawer din kaya ta nufa bawai dan tana da tabbacin samun abunda zata saka a ciki ba. Kaya ta gani ciki hada hijabai da duk wani ahun bukatar mace. Bata tsaya zabe ba ta janyo kawai ta saka ta tada sallah.

Dan kuka Zeenah tasha kuka har ya kasance tanajin zafi idan hawayen zasu fito. Nan saman sallayar ta kwanta tana kuka addua kuwa babu irin wacce batayi ba. Tasan dare yayi sosai, dan tanajin irin sanyin da garin yake kadawa amma haka ta kasa tashi akan sallayar nan. Karshe ma alwalla ta sake ta cigaba da sallah har saida liman ya kira assalatu.

A bangaren Yarima Bilal kuwa, tunda ya fita daga dakin direct masarautar ya fita gaba daya. Gidan su Isma'il ya nufa kuma koda yaje bai tsaya ko ina ba sai a dakin Isma'il ya kwanta ta rigingine. Yanayin yadda hankali ya gushe a jikinta, da kuma yadda take kuka kamar ranta zai fita komai yake dawo mashi cikin kai. Kwata kwata bata bashi tausayi ba, baisan yadda tata mahaifiyar ta rasu ba, amma yanada tabbacin duk zafin da zataji sa kuka bakin ciki baikai wanda yaji ba lokacin da yana shekara 8 kadai a duniya. Bayan mahaifiyarshi babu bai kara jin tausayin wata Ya Mace ba. A wajen shi mata mugaye ne, azzalumai ne, kuma munafukai.

"Gimbiya..." abunda ya furta kenan sai yaji kamar zaiyi kuka. Dan dole ya maida dukkan wani memory na mahaifiyar shi. Dan bai yadda ya karayin kuka ba saboda rashin ta. Gimbiya yake ce mata, dan gaba daya masarautar saidai ace mata Maman Yarima Bilal. Fulani ita ta kawo wannan doka, a cewar ta baiwa koda Sarki ta haifa sunanta bai taba zama gimbiya. Abunnan har kuka yake sakashi idan yaji ana kiran sauran matan sarki gimbiya wance amma shi tashi saidai ace Maman Yarima Bilal. Hakan yasa ya fara ce mata gimbiya, tun tana fadin ya daina kar Fulani ta hukantashi har ta hakura.

Bacci ne ya fara dibarshi, sallamar Isma'il yaji saman kanshi yana salati, "Amma wallahi Yarima ka iya rainin wayau. Ina can cikin masarauta ina nemanka sama ko kasa ashe kana nan bacci ma kake da niyyar yi?" Daka mashi duka yayi a cinya, hakan yasa Bilal ya mike zaune yana jan tsaki.

"Isma'il menene haka?" A duk lokacin da yayi magana ya kasance maganar shi bata cika yawa ba, yadda kasan duk kalma daya da zai furta sai ya biya kudin ta.

"Kamar ya menene haka? Tashi zakayi na rakaka mana, dama sauran friends dinmu sunsan halinka basu tsaya wani rakiyar ango ba." Fadan Isma'il kenan a lokacin da yake zama  saman daya daga cikin kujerun dake cikin dakin.

"Ina kenan?" Ya tambaya yana gyara kwanciyar shi, shi bacci ma yakeji. Dama yau mai Martaba ya aiko aka tada shi da wuri wai saboda daurin auren.

"Bilal bansan iskanci fah. Wajen amaryar ka mara kunya ko?" Yana fadin haka ya fashe da dariya. Tsaki Bilal yaja ya juya mashi baya, "Ka kashe mun wutar dakin." Duk iya juyin duniyar da Isma'il ya mashi akan ya tashi su tafi ko kallon shi baiyi ba balle yasaka ran zai mashi magana. A haka ya hakura ya kyaleshi.

Kamar wasa kullum sai Isma'il ya roki Bilal akan ya tashi suje gida amma fir yaki, har sati daya ya yayi. Yau bayan sun dawo daga masallacin juma'a suna cin abincin rana saiga kiran waziri wayar Isma'il. "Kai Isma'il Yarima yana gidan nan nasani, ku tashi yanzu ba sai anjima ba ku wuce fada. wane irin rashin hankali ne haka? Ashe sati daya kenan tun ranar daurin aure Yarima baije gida ba?" Fada ya farayi, da kyar Isma'il ya lallaba shi ya bashi hakuri kafin ya fatattaki Bilal suka tashi suka nufi kofar soro. Inda nan masarautar take.

Suna shiga suka falon sarki suka nufa, inda yake ganawa da yan gida. Fulani suka gani zaune sai ga Zeenah a rabe daga can gefe. Duk tabi ta rame idanunta sun fada sunyi jajir. Zama sukayi suka gaidasu kafin Mai Martaba ya fara magana.

"Yanzu Yarima abinda kayi daidai kenan? Masarautarmu zaka tozarta? Sati daya da aurenka amma baka kwana gida ko sau daya ba? To daga yau ban yarda ka kara kwana ko ina ba bayan cikin gidan nan a bangarenka kuma."

Fulani ce ta fara magana, "Allah ya baka yawan rai Allah yaso naje dubo yarinyar nan, dan danaga har sati batazo ta gaishe ni ba yasa nace kodai lafiya? Ashe ko ganinshi batayi ba balle ya koya mata yadda zaman masarautar yake."

Shidai Bilal yana jinsu baice komai ba tunda ya duke kanshi kasa, yau ko hakurin ma bai bada ba dan gani yake ai baiyi laifi ba. Isma'il ne ya saki baki sai bawa mai martaba hakuri yake. Daga haka aka sallame su, ko kallon inda yake Zeenah batayi ba ta wuce ta koma bangaren su.

Tana cikin daki tana kuka, daga ido tayi taga agogon na nuna mata 10:30 na dare. Iskar dake kadawa cikin daki tayi mata kadan, ji take kamar zata sike. Tun tana saka ran zaa aiko wani ace mata Mama nada rai har ta fidda. Gashi tayi tunanin Zainab zatazo amma har yau, tasan Baba ya hanata zuwa.

A hankali ta taka ta fita bakin haraba, kujerjn shakatawar dake wajen ta samu daya ta zaune fa rungume guiwowinta, kuka take kamar ranta zai fita. "Mama yanzu haka mukayi dake? Ba kince zaki jira nayi kudi na kaiki asibiti ba? Haba Mama. Yanzu kinsan irin rayuwar da nake ciki? Bacin kisan kai haramun ne da wallahi na kashe kaina Mama. Na tsani kowa da komai na duniyar nan Mama. Dama ashe dukkan mutane azzalumai ne? Ashe Mama babu wanda ya damu da damuwar ka? Har na rasaki amma bayan Mai Martaba da waziri babu wanda yamun gaisuwa a gidan nan? Ko suce Allah ya miki rahama naji dadi?

Bazan kara yyiwakowa mutunci ba Mama, rashin mutunci kuwa yau na fara yinshi..." tsanar dukkan mutanen da take tare dasu taji tana shigarta a hankali. Tunda har babu wanda ya damu da damuwarta ita ma daga yau bazata kara bari damuwar ta nuna ba.

Tana cikin kuka tana fadawa Mama maganganun dake cin zuciyarta, wanda hakan ya kasance mata al'ada tun daga lokacin da aka kawota gidan sarki a matsayin matar yarima Bilal. Takun tafiyar mutum taji daidai gefenta, tana dagowa ta ganshi tsaye a kanta fuskar nan tamke kamar ta kashe mashi wani abu mafi soyuwa a rayuwarshi.

"Ki tashi ki koma ciki, ban damu ba idan zaki kashe kanki da hawaye ba, amma babu yadda zaayi kije kikai karata wajen Mai Martaba, na dawo kuma ki fito waje kina kuka. Duk neman sharrin ki na gaji dashi."

Mikewa Zeenah tayi a tsaye, dama marin daya mata ranar da aka daura auren su yana nan cikin  ranta. Ta dade da jiran ranar haduwarsu tun bayan bikin sai yau. Yadda takejin zuciyarta ta kakashe bata damu da duk wani abu da zai faru ba, marin ta sauke mashi saman kunci.

"Idan kai ka manta, ni ban manta ba. Tsabar baka da imani baka da tausayi, ina kuka ina fada maka mahaifiyata ta rasu ko gawarta baa bari na taba ba ka mareni? A gaban bainar nasi ko? To bari kaji, daga yau mu kulla zanin azabtar da juna, azzalumi kawai." Har tayi gaba zata wuce ya fizgo ta ta dawo baya.

Maruka ya ringa sauke mata saida yaji ranshi ya mishi sanyi, da karsashi ya furta "Badaru!" Baayi minti biyu ba saiga wani bafade rike da doguwar bulala.

Kallon Zeenah yayi cikin ido, "Ki natsu kisan gidan da kika shigo da kuma wanda kike zama dashi. Ranar kinci sa'a an shigar damu fada, yau bazaki ci ba. Badaru, ka tabbatar kayi mata bulala hamsin." Yana fadin haka ya juya ya koma ciki. Zeenah batayi aune ba taji saukar bulalar Badaru saman bayanta, daga daya har hamsin haka ya mata su babu ko kakkautawa.

A JINI NA TAKEWhere stories live. Discover now