Haka aka dauka kusan sati biyu, kullum sai taje tayi aiki kuma kullum sai sunyi fada da Isma'il. Tunma tanajin kunyar zaginshi wani sa'in har ya koma zaginshi take san ranta. Ya cika shegen san a sani gaida uwar miji a kasuwa. Ko ina ruwa shi da ita? Yabar dan sarkin magana yayi magana? Sai shi zakakke? Daga waziri ubanshi bai kau ba. Bilal kuwa tunda ta fara aiki ko sau daya bai daga ido ya kalleta ba har zaman da ake yau kuwa.
Yau batazo da wuri ba, kasancewar saida ta taje takai Mama asibiti kafin ta dawo, hakan yasa sai gab da laasar ma ta shigo gidan. Kamar yadda ta saba gyare gyarenta ta farayi tanayi tana rera karatun kur'ani. Dan yawanci haka take, ita ba wata waka ta iya ba, dan kuwa daga ita har Zainab babu mai waya balle taji wakar ciki. Iya karta da waka inta bi ta wajen dj din dake zama bakin titi. Dan ko biki bata zuwa. Ita dai bata yarda wani abu ya nisanta ta da Mama ba.
Batasan yadda akayi ba, amma yau a bude yabar dakinshi, wanda unda ta fara aikin bata taba ganin dakin a bude ba. Dan tsaki tayi, "Yanzu haka wancan dan rigimar ne yace a barshi bude ko? Dan inzo aita jaraba dani ace ban gyara ba, to ta Allah ba tashi ba munafikin banza." Ita duk a ranta ta kawo aikin Isma'il ne, dan yadda ya tsaneta tasan tabbas tafi tsanarshi.
Dakin ta shiga sai bambotai take, dukda dakin ba wani tsaf tsaf yake ba amma babu irin dattin nan sosai. Toilet ta fara shiga, dan uta duniya babu abunda ta tsana kamar wankin toilet, saigasa ta gwanmace ta fara gyarashi kafin tayi gyaran komai.
A bangaren Bilal kuwa, a hankali yake takawa zuwa bangaren Fulani, wacce ta kasance mace ta farko a wajen mai martaba. Yasan yayi laifi, dan kuwa a dokar masarautar dole yaje da safe ya gaidata kamar yadda sauran matan sarki da yaran sarki keyi, amma shi bai iya wannan al'adar itama ta sani. A haraba ya ganta tanashan ababen marmari, tana ganinshi ta tashi daga kishingiden da take. Dukda cewar tanada nata dokokin, shima Bilal yana da nashi. Dan bai yarda yazo gaishe ta tayi wani kishingide tana ansa shi ba, dan indai bata mike zaune ba to sai suyi awa bazai gaishe ta ba har sai ta gaji ta gyara. Wannan halin izgilancin fa miskilanci na Bilal na daya daga cikin ababen da suka kara rura wutar tsanarshi a zuciyarta.
"Barka da zuwa Yarima." Abunda kuyangin suka furta kenan, kafin daya daga cikinsu ta koma ciki domin kawo mashi abun jika baki. Tana ajiye kofin duk sukayi baya suka basu waje.
Ya saba duk lokacin da yazo sai yasha abun jika baki a bangaren Fulani. Dan haka yau bai kawo komai a ranshi ba ya kurbi kusan rabin kofin. "Barka da hutawa." "Yauwa Barka kadai Yarima. Sai yanzu na samu ganinka? Da fatan dau babu wata matsala ko?" Magana take tana murmushi, dan kuwa Fulani irin matan nan ne da duk bala'in ka baka taba gane menene cikinsu balle abunda suke tunani.
Sama sama yake amsa ta, duk juwa da kokarinta na tajashi hira abun ya gagara, karshe ma tashi yayi ya mata sallama ya nufi bangaren shi. Tun a hanya ya fara jinshi ba daidai ba, aabundabai taba jiba a rayuwar shi, wasu yanaye yanaye yakeji wanda dakyar ya karasa bangaren shi. Kai tsaye dakinshi ya nufa, dan kuwa har marar shi ta fara kullewa. Wannan wane irin abu ne? Buji buji yake gani a lokacin daya iso dakin kuma ya ganshi a bude, to meya faru? Yasan dai shi a kulle yabar dakinshi. Dage kafada yayi ya shiga dakin.
Tsaye ya iske ta tana karkade bargo, cikin kira'a mai dadin sauraro take rera karatun ta. Yafi minti biyar yana kallonta, magana yakeso yaji waya shigo da ita dakinshi amma ya kasa, dan gaba daya jikinshi babu inda bai mutu ba. Rigib! Ya fada kan gadon yana sauke numfashi, addua kawai yakeyi a zuciyarshi Allah ya kareshi da aikata dukkan wani aikin zunubi a wannan yanayin.
Zeenah batasan da mutum ba saidai taji sautin fadowarshi saman gado, a tsorace ta juyo tana kallonshi, yadda yake fitar da numfashi yana kallonta ba karamin tsorata ta yayi ba. "Dallah malam miye haka ka wani shigo cikin daki ka baje kan gado kamar kitse? Banfa san iskanci." Tabbas yasan magana take amma kwata kwata bayajin abunda take furtawa, yanayin budewa da rufewa labbanta kawai yake kallo.
"Kai dallah ka tashi!" Ta fada a hargitse, duk kuwa da irin dokawar da zuciyarta take mata. Hanyar futa dakin take nema, dan ta duk inda zatabi jikinshi ya kare, dama can lungun gadon take. Yanzu kuwa tana hawa gadon dole wani abu ya faru.
Dakyar Bilal ya tattaro dukkanin karfinshi ya miko mata hannunshi, "Tayar dani..." ya furta da kyar, duk inda karfinshi yake nemanshi yayi ya rasa.
Sai daga baya ta lura kamar baida lafiya, ganin yadda yake zufa ga numfashinshi dake fita dakyar. Sai taji ya dan bata tausayi, dan kuwa dukda bata cika ciwo ba amma tasan ciwo. Hannun shi ta karba, duk iya kokarin da tayi ta mikar dashi ta kasa, karshe ma data saka karfi saidai taji ta afka saman kanshi. Kafin tasan meka faruwa taji an kurma ihu daga window din dakin, bayi ne tagani mata guda biyu sunata salati karshe taga sun ruga.
Hankalinta a tashe tayi hanzarin mikewa tana kallonshi, gaba daya ma yanzu ya rufe idanunshi. Kafin kace kwabo sai sukaji sallama, Fulani ce ta shigo ga bayi kuma. Hankada kafafun Bilal Fulani tayi kafin ta karasa wajen Zeenah ta rungume ta, "Sannu yar nan, ai baiyi nasarar afka maki ba ko?" Ita Zeenah jin abun tayi wani banbarakwai.
Ko kafin ta amsata sai sukashi sallamar Mai Martaba. Dan kuwa Fulani da kanta taje ta kirashi akan yazo wata matsalar cikin gida ta taso. Hada yan kwalla Fulani ta kalli Mai martaba, "Ka gani ko Mai Martaba? Tun yaushe nake ce maka ga abunda Bilal ya koyo a kasar wajen nan amma kakiji. Yanzu bacin wadannan bayin guda biyu ai da ya afka wa diyar mutane shikenan yaja mana abun kunya cikin gari. Ace dan sarki guda yana irin wannan halayya?"
Girgiza kai kawai Mai Martaba yayi, a hankali ya taka yaje inda Bilal yake kwance. Yanajin duk aabundake faruwa amma ko bude ido ya kasa. A hankali mai Martaba yadan daki hannunshi, "Bilal, tashi ka fito falo yanzu." Yana fadin haka ya fita, suma sukabi bayanshi.
Dakyar Bilal ya shiga toilet ya wanke fuskarshi kafin ya samesu falon duk sun zazzauna. Baba yagani a tsaye gefen Mai Martaba sai kallon Zeenah yake da idon tuhuma. Waje ya samu ya zauna a kasa shima kafin mai martaba ya fara magana. "Bilal kaji abunda Fulani tace, me zakace akan afkawa wadda take maka hidima da ka kusan yi?" Nan take zuciyar Baba ta dau dukan tara tara, kallon Zeenah yake alamar da gaske anyi hakan?
Bilal tunda yazo wajen ya duke fuskarshi bai kara dagowa ba, kuma dukkansu da suke wajen face Zeenah sunsan bazaiyi magana ba. Shi haka halinshi yake, in zaka mashi tambaya dari indai bai aikata abu ba to bazai taba dagowa ya kalleka ba. Idan yayi dinma bazai kalleka ba. Mai Martaba kadai yake bawa hakuri in yayi laifi, shima sai ya taki saa. Da wuya ma tunda Bilal bai cika laifi ba.
Ganin an kusa minti biyar yasa Zeenah ta gyara tsugunninta. "Inada magana Mai Martaba." Bilal saurara kawai yakeyi dan jin me zata furta, yasan wannan yarinyar tsaf zata ja mashi sharri.
Daga mata kai Mai Martaba yayi ta cigaba. "A gaskia ni babu abunda Yarima yamun ko kuman ya kusan yimun. Abunda ya faru shine..." kaf ta zayyana abunda ya faru da yadda ya shigo ta fadawa Mai Martaba.
Ko kafin wani ya furta wata magana Fulani tayi karaf, "Zo nan Larai, fadi abunda kikace mun kin gani." Jikin Larai har bari yakeyi. "Allah ya taimaki mai Martaba, dazu na shigo bangaren Yarima, Fulani ta aikoni in saida mashi sakon bukatar ganinshi da takeyi sai naga ita wannan tana zuba magani a cikin lemu, wanda da lemun Yarima yazo a hannu yanasha a wajen Fulani. Tunda naga haka na fadawa Fulani shine tace muzo muduba abunda yake faruwa, sai mukaga tana kokarin afkawa Yarima, tana ganinmu ta fasa kuka wai muzo mu cece ta Yarima zai keta mata haddi." Wani irin kukan kura Zeenah tayi kan Larai, amma ko kafin takai mata dukan farko ita dukan Baba ya fara sauka akan bayanta.
Kuka Baba ya fashe dashi, bayan Mai Martaba yayi gyaran murya akan dukan Zeenah da yakeyi. Fadowa yayi saman guiwowinshi, "Tuba nake ranka ya dade, amma bansan me zance ba. Tunda har Zeenatu ta fara zuwa da wadannan dabi'un, ina neman alfarma wajen Mai Martaba akan ya bayar da ita sadaka koda kuwa daya daga cikin bayin da suke kurkuku ne." Wani kukan Baba ya fashe dashi.
Zeenah kuwa tanajin furucin Baba ta fashe da kuka, shikenan tata ta kare. Bilal dago ido yayi suka hada ido, tana kallonshi alamar ya fadi mana, ita duk yau bata ganshi ba inda lokacin nan ba amma ya dauke kai. Zumbur su dukansu suka mike a lokacin da sukayi furucin mai martaba kafin ya fita daga bangaren Yarima.
"Insha Allahu Ranar Juma'a bayan anyi sallah zan daura auren Zeenatu Kabir Muhammad da Bilal Kabir Usman." Babu abunda Zeenah take hange a idanunta banda 'Yau Laraba!'
YOU ARE READING
A JINI NA TAKE
RomanceLabari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun ma...