Chapter 8

3.7K 309 30
                                    

"Hannunta ya rike da karfin gaske ya karasa da ita kusa da sink din dake dakin,duk da tureshin da takeyi be hana deen wanke mata jinin da ke zuba a hancinta ba,tissue ya dauko ya karasa goge mata hancinta sai daya tabbata jini ya dena zuba a fuskarta tukunna ya saketa

"Dispenser ya karasa ya tsiyayo ruwan sanyi a cup ya mika mata,turewa tai tace leave me,stay away from me

"Heeeeeeeeeyyyy ya fada da karfi yana buga cup din akan table a take cup din ya fashe,kallonta yai da zafafan idonsa inda tuni nabeelah ta rikice jikinta ya dauki rawa

"Hannunsa yasa ya dago fuskarta cikin zafin nama yace first of all.don't you ever talk to me in that tone ever again,second of all.don't you dare raise your voice again to me,third of all.don't you ever think that i'm in love or i fucking care about you.....don't you ever put it in your mind....yana gama fadar haka ya fice daga dakin tare da janyo kofar da karfi

"Dakinsa ya shiga ya kwanta akan gadonsa idonsa na kan plasma din dake jikin bed din,kida ne yake tashi kadan-kadan waqa daga cikin film din rustom "tere sang yara" inda deen ke bin waqar cikin kwarewa

"Oh karam khudaya hai
Tujhe mujhse milaya hai
Tujhpe marke hi to
Mujhe jena aaya hai

O tere sang yaara
Khush rang bahara
Tu raat deewani
Main zard sitaara

O tere sang yara
Kush rang bahara
Main tera ho jaaun
Jo tu karde ishara

"Wayarsace ta fara ringing,ganin number dad ya sashi saurin dauka cike da ladabi yace

"Hi dad.....basu jima suna magana ba sukayi sallama,jefar da wayar deen yai akan gado cike da bacin rai ya dafe kansa yace oh my gosh....jikinsa sanyaye ya samu sadiq a gyming room,ganin deen babu wani kuzari yasa sadiq ajiye karfen dake hannunsa yace sup tiger?

"I dey fine,buh little bit boring,deen ya fada ba tare da ya kalli sadiq ba

"Murmushi sadiq yai yace what's wrong?

"Dad yace gobe in tafi Uk akwai contract din da muke dashi achan,zamuyi meeting da top 10 billionaires na kasar kuma fa atleast zan iya kaiwa 2 weeks ni gaskiya i don't want to go ya fada kamar me shirin yin kuka

"Tsaki sadiq yai yace so what?don dad yace ka tafi UK?ai dama kafison chan saboda kafi jin dadin nuna halinka na womaniser achan,yanzu kuma meyasa kace bakaso

"Kai banzane wlhy sadiq,you are not sharp at all,idan yanzu na tafi UK uban waye zai kula da yarinyar chan da nai kidnapping,yanda kake matsoracin nan dai nasan you can't may be ma ta zaneka watarana,yanzu ka bani shawara ya zanyi da ita?

"Kwashewa sadiq yai da dariya har yana tafa hannu yace you are baddest mehnn,kawai ka sakar musu yarinyarsu ta tafi gida,ni dama gaskiya bana jin dadin ajiyar yarinyar nan da mukeyi cikin gidan nan,ga alhakin ta gana iyayenta ga kuma babban lefin da mukewa ubangiji na kasancewa da macce wacce ba muharramarmuba.....

"Stop it please,stop it,banzo nan kayi min wani wa'azinka ko wani tafseer ba....idan wa'azi zakayi sai ka tafi masallaci kayi amma ba anan ba don ni bana bukatar wani wa'azi anan kawai inaso ka fadamin what to do ne?idan kuma babu ka fadamin coz i have alot of business to do...deen na gama fadar haka ya mike ya fita daga dakin,murmushi sadiq yai domin inda sabo dama ya saba indai akazo bangaren wa'azi ko nunawa deen abinda yakeyi wanda baya dacewa yakan yi fushi ko kuma ya dauki gaba da koma waye

"Dakin nabeelah ya sake turawa ya shiga,kwance take akan gado ta takure tana kuka mai tsuma zuciya,dagota yai a fusace ya hadeta da jikin bango

DeenWhere stories live. Discover now