Chapter 40

2.7K 268 17
                                    

"Ta dade a tsaye a guest room tana tunani kafin ta bar dakin jin kafafuwanta sunyi mata nauyi ta wuce apartment dinta bata yarda sun hadu da aunty a'i ba

"Haba tiger,what the hell are you doing?taya zaka bari mace ta dora hannu a fuskarka da sunan wai ta mareka amma ka kasa taking wani action kuma nika hanani na daukar maka,,,what's wrong with you are you mad?sadiq ya fada yana kallon deen cikin takaici

"Yes i'm mad...i'm totally,completely,madly in love with her sadiq,deen ya karasa maganar yana kallon cellphone din dake hannunsa

"You are in love....well don't be stupid asap dubeka kamar wani mutumin kirki nan kuwa shashashar yarinya ke marinsa yana gani ya kasa komai

"Shut up!!!deen ya fada a zafafe yana buga sitiyarin motar dake hannun sadiq,da sauri yayi parking ya tsayar da motar cak ganin yanda yanayin deen ya sanja lokaci daya yana huci,sake kallon sadiq yai da jajayen idonsa yace don't you ever call nabeelah with that name "shashasha"again,saboda lokacin da nake aikata lefuka marasa kyau nabeelah ce kadai macen da bata gajiya da yimin nasiha akan inji tsoron Allah kuma inji tsoron haduwa ta da Allah,did you ever told me so?ya tambayi sadiq a fusace

"Da sauri sadiq ya girgiza kansa sannan ya sunkuyar da kansa kasa

"Well so don't you ever insult her again,a halin yanzu nabeelah kadai nake bukata a rayuwata,she's the most important person of my life

"Basu sake ce da juna komai ba har suka karasa parking space din gidan deen ya fito ya nufi apartment dinsa zuciyarsa a bace,bayan sunyi sallar magrib ne sadiq ya turo kofa ya shigo dakin ya tarar da deen zaune yana lazimi

"Sosai take regretting marin da tayiwa deen gaban sadiq tare da mamakin yanda deen be nuna fushi ko wani bacin rai ba,to meyake faruwa dashi haka?ko haukan ne be sakeshiba har yanzu?shine abubuwan da take tunani...mikewa tai zaune daga kwanciyar da take ta kalli agogon dake maqale a dakin it's 12:30am amma sam bata jin bacci sai yunwar dake damunta,a gajiye ta shiga kitchen ta fara duba abinci sedai bata samu komai da zata ciba don mostly aunty a'i kafin ta kwanta take bawa almajirai sauran abincin da akaci aka rage,tsaki tayi ta bude freezer dake gefen kitchen din ta dauko dambun nama da fresh mango juice ta wuce dakinta duk da ba abinda takeson ciba kenan

"Sai daya gama lazimin tukunna ya kalli sadiq dake gefensa yana jiransa yace what's up?

"Murmushi sadiq yai kadan irin na tsokana sannan yace toh kayi dariya mana albishir nazo maka dashi

"Tsaki deen yai yace you are not serious bro get out please....ya karasa maganar fuskarsa a daure

"Mikewa yai seda ya bude kofar tukunna yace toh shikenan na fita na baka guri dama akan maganar nabee.......da sauri deen ya mike tsaye yana fadin nabeelah?

"Daga mishi kai sadiq yayi yace of course sannan ya fita daga dakin da gudu

"Shima da gudu deen ya bishi dakinsa yana rokonsa ya fada masa menene,cigaba yayi da dariya sannan ya fada masa suje wajen mom ita zata raba gardamar

"Murmushi mom tayi tace ashe dama ka dade kana cutar kanka deen akan yarinyar da babu yanda mahaifinka beyi da kaiba akan ka aureta amma ka nuna sam baka sonta,yanzu taya zan kalli alhaji nayi mishi wannan maganar?

"Sosa keya kadan deen yai yace mom ki fadawa dad ze fahimceki please ina sonta sosai mom ya karasa maganar kamar zeyi kuka

"Ajiyar zuciya tai tace toh zan gwada amma ni kaina ina tsoron tunkarar alhaji da wannan zancen

"Shiru yai kadan sannan ya kalli mom yace mom ina junior me?sunan da deen ke fadawa little  deen kenan

"Yana chan daki yana bacci kasan jiya ya kwana da fever da kyar ya sauka daga jikinsa

"Mikewa yai ya nufi dakin little deen,sedai kiran sunan mom din dayai da karfi yasa mom da sadiq karasawa dakin da gudu

Manage it azumi things hehehe
Don't forget to vote,share and comment
Ramadan mubarak

DeenWhere stories live. Discover now