Chapter 28

2.6K 308 17
                                    

"Shiru tayi kadan ta rufe idonta,a hankali ta bude jajayen idonta ta kalli sadiq da shima ya zuba mata nashi jajayen idanuwan tace but kana ganin wannan shine solution?i don't think wannan zai iya zama solution saboda nabeelah ba wata babbar lawyer bace wacce zata iya tsayawa ta kareka fa....batul ta karasa maganar tana kallon sadiq cikin damuwa

"I know it batul,amma tunda har kika ji na ambaci sunan nabeelah ya kamata ki aikata abinda nace miki

"Kana tunanin yaya deen zai saurari a hada case dinsa da karamar lawyer kamar nabeelah?

"Keep quite batul!!!just do what i said ya fada a zafafe

"Jikin batul sanyaye ta fita ta nufi inda motar ta ke ajiye ta shiga ciki ta nufi hanyar gidansu nabeelah

"Yawo yake yi a palour din zuffa duk ya jiqa mishi jiki duk da sanyin AC din dake sanyaya dakin,mom ce ta fito daga daki fuskarta babu alamar walwala sai damuwa hannunta rike da newspaper ta tsaya gaban deen tana huci,juyowa yai ya kalleta cikin damuwa yace mom....hannu tasa ta sauke mishi kyawawan mari guda 3 sannan ta jefa mishi newspaper din dake hannunta tace kaga abinda zafin zuciyarka ya jawo mana ko?kaga abinda rashin nutsuwarka ya jawo mana ko?kaga abinda zallar rashin tunaninka ya jawo mana ko deen?duba ka gani saboda rashin hankali irin naka har yan jarida sun samu damar buga jarida akan batul suna fadan cewar anyi raping dinta amma anyi nasarar kama wanda yayi mata fyade,duba ka gani da kyau hoton kanwarkane yake yawo a duniya tare da sunan mahaifinka akan cewar yar gidan modibbo ce aka yiwa fyade

"Kallon jaridar yake yana karantawa cikin sauri-sauri ya jefar da jaridar yayi yace what????who did this to me?taya za'a bazawa duniya wannan labarin?

"Tsaki mom tai tace zafin kai irin naka mana shine ya jawo mana duk wannan matsalar

"Toh amma mom taya za'ayiwa batul fyade mu zauna muyi shiru?ashe mace bata da wani yanci kenan?ashe idan muna bari maza suna bata rayuwar mata ya kike tunanin duniyar zata kasance?mom kin fini sanin darajar mata,mom kin fini sanin irin ciwon da mace takeji idan anyi mata fyade,mom mata dayawa suna rasa mazajen aure ta dalilin fyade,mata dayawa suna kamuwa da cututtuka kala-kala ta dalilin fyade,mata dayawa suna shiga damuwa saboda anyi musu fyade,mata dayawa suna rasa farin cikinsu na har abada saboda fyade,mata dayawa suna rasa rayukansu ta dalilin fyade toh meyasa zamu zuba ido muna kallo?idan har fyade yana faruwa a cikin al-umma toh dukanin mata kannenmu da ya'yanmu zai zamo ana kiransu da suna guda daya wato karuwai,ya zama dole muyi amfani da human rights don samowa mata yanci.....deen ya karasa maganar yana kallon mom datake kallon deen cikin birgewa da sha'awar kasancewa mallakinta wato yaronta

"Ajiyar zuciya tai tace amma deen menene fa'idar bayyana hotunan batul a social-media ana fallasa asirin da muke shirin boyeshi?idan har sai an bayyana hotunan batul dana mahaifinta akan cewar anyi mata fyade amma anyi nasarar kama wanda yai abin toh ina ganin gara abar zancen kawai domin hakan zai sake jefa rayuwarta cikin tashin hankaline

"Girgiza kansa yai yace mom bani nasa aka buga bayani akan batul ba,banida wata masaniya akan haka amma ki bani dan lokaci zan duba na gani,yana gama fadan haka ya fita daga gidan zuciyarsa na bugawa

"Kan cushion ya fada,gaba daya duniyar zafi take masa komai na duniyar baya birgeshi,meyasa sadiq zemin haka?shine kalmar da deen yafi ambata a duk sanda ya tuno da abinda ya faru,daga idonsa yai ya saukesu akan babban picture din dake ajiye a palour,deen ne da sadiq a picture sanda sukaje Morocco yin wani project sanye suke cikin Ash suits din datai matukar yi musu kyau kowa yayi smile a hoton...saurin rufe idonsa yai ya dora hannunsa akansa yayi tsaki

"Tabbas idan deen yace baya missing din sadiq karya yakeyi,domin yayi matukar shaquwa da sadiq,sadiq ne kadai yake jure duk wani abu da deen zeyi masa ko wanne irine amma sam bazai nuna masa bacin rai ba,mikewa yai ya nufi bar din dayake cike da kwalaben kayan mayen deen wanda yake amfani dasu aduk lokacin da ransa ya baci,vodka ya dauko da whiskey don sune favourite dinsa ya ajiye ya fara sha,sai da yasha kwalba 4 tukunna ya mike ya fara fasa hotunan sadiq dinda ke ajiye a palour din yana fadan kalamai barkatai.....i hate you,i will kill you sune kalaman da deen yafi bawa mahimmanci a wannan lokacin

"Kuka batul keyi sosai idan ta tuno da halin da sadiq yake ciki,tsaki tai ta jefar da wayarta tace wai meyasa yaya deen ze takurawa kansa akan abinda be kamata ya damu kansa ba?tayaya slay queen kamar ni a kalleni ace wai anyi raping dina?this is unfair gaskiya.....i'm beautiful ina da right din da zan nemi duk namijin da nakeso a duk lokacin da naga dama,murmushi tai ta karasa gaban babban mirror din dake dakin tace yanda nake kyakkyawa ga figure kuma every man dream taya zan zauna babu slaying.....knocking din kofar da aka farayine yasa batul saurin komawa kan gado ta zauna kamar wata mara lafiya tace come in"

Short chapter
But you know my problem guys banda lafiya
And you are not voting fah😭😭

DeenWhere stories live. Discover now