Chapter 52

3.2K 354 35
                                    

"A firgice ta mike tsaye tana kallon hajiya hindu data kasa cewa komai sai kallon boka da takeyi cikin tsananin rikicewa tace hajiya kina jin abinda yake cewa kuwa?ki gaggauta fada masa ya dakatar da duk wani aikinsa banaso kuma bana bukata deen shi kadai na mallaka a duniya shi nake bude ido a kullum idan na kalleshi yake daukemin damuwata taya za'ai ace na rasashi,da sauri hajiya hindu ta toshewa mom baki a tsorace ta kalli boka tace aljani kurungu ya taimakeka,kayi mana afuwa,,,bushewa yai da dariya sannan ya hade ransa ya kallesu yace ku tashi ku bani guri,ku bace min da gani anan,ya karasa maganar wuta na fitowa daga bakinsa yana dariya yana cewa ba dai ni zaki yiwa rashin kunya ba,jeki zaki ga abinda ze faru,da gudu suka bar gurin boka suka karasa gurin motarsu da sukai parking nesa da gurin bokan har suna zubar da takalmansu....
"A birkice ta koma gida zuciyarta na bugawa da sauri ta tarar da sadiq zaune a palour yana playing game,cikin mamaki yace mom lafiya?murmushi tai tace lfy lau mana ko kaga wani abune?ta karasa maganar tana kallon jikinta,,ajiyar zuciya sadiq yai yace mom na gankine kamar a tsorace sannan kalli kafarki ko takalmi babu fa,lumshe idonta tayi ta bude cikin damuwa tace kaga ka kwantar da hankalinka lafiyata kalau kawai na gajine da yawa shiyasa,murmushi yayi yace okay mom you are welcome,har ta nufi hanyar da ze kaita upstairs tai saurin juyowa a firgice tace ina deen?hannu yasa ya dauki phone dinsa daga inda yasa charge sannan ya dago ya kalli mom yace deen yana dakinsa kansa keyi masa tsananin ciwo,,,,what?ta fada da karfi tare da gajeran tari tace tun yaushe yake ciwon kan?dagowa yai ya kalleta yace be wuce 3 hours da fara ciwon kan ba kuma da alama he's suffering alot,okay kawai tace sannan ta juya ta nufi dakin deen hankalinta a matukar tashe shikenan maganar boka ta tabbata?
"Tura kofar dakin tai ta shiga jikinta a sanyaye ta tarar dashi kwance ya lullube duk jikinsa da blanket,da gudu ta karasa kan gadon ta yaye bargon daya rufe fuskarsa a hankali tace deen ya jikin naka?mom jikina sam-sam babu sauki ciwon kan nan yayi tsanani dayawa,gabantane ya sake faduwa muryarta na rawa tace am amm amma kasha magani kuwa?cije lower lip dinsa yayi yace nasha mom amma maimakon ya ragu sai karuwa yakeyi ni bantaba ciwon kai me tsanani ba haka mom....jikinta ne ya dauki rawa da sauri ta mike tace bari na sanar da dad dinka yanzu sai mu tafi asibiti,bata jira ya bata amsaba ta fita daga dakin duk da shima beyi niyyar bata amsaba saboda tsananin ciwon da kansa keyi masa
"A zaune ta tarar da Alhaji modibbo yana aiki a system dinsa hannunsa daya rike da coffee yana sipping,ganin yanayin ta daban dana kowanne lokaci ya sashi saurin ajiye cup din dake hannunsa yace lafiya?ba dai kan maganar auren deen da nabeelah bane ko?don indai akan zancen ne ya kamata ki gaggauta fitar min daga daki don na yanke hukunci kuma babu wanda ya isa ya sanjamin,ajiyar zuciya tai sannan ta samu guri ta zauna tace Alhaji niba maganar aurece ko rashinta ya kawoni ba,deen ne bashi da lafiya yana kwance a dakinsa don Allah ka tashi mu kaishi asibiti ta karasa maganar hawaye na zuba daga idonta,cikin mamaki ya kalli mom yace deen kuma,wanne deen din kike nufi a ciki little deen ko kuma deen dina?deen mana nake nufi deen dinmu babban deen nake nufi ta karasa maganar cikin sauri
"Cup din dake gefensa ya dauka yayi sipping coffee sannan ya ajiye yace menene yake damunsa?ciwon kai yakeyi alhaji don Allah ka tashi mu kaishi asibiti ta fada cikin rikicewa,shi kam abin mamaki yake bashi ganin yanda mom ta rikice saboda deen yana ciwon kai,kallonta ya sakeyi yace wai ke in tambayeki karamin deen ne dai ko babban deen yake ciwon kan zamu kai asibiti?tsaki tai tace alhaji deen dai daka sani yaron dana haifa da cikina yaronmu nida kai nake nufi yanzu na shiga dakinsa na tarar dashi kwance yace min kanshi ne yake ciwo please ya kamata mu kaishi asibiti,murmushi alhaji modibbo yai ganin cewa har yaushe mom ta damu da deen kuma tasan kula da lafiyarsa matar da bata damu da rayuwar kowaba sai rayuwarta....jin yayi shiru bece komaiba yasa mom sake kallonsa tace kayi shiru wai me kake nufine haka ina ta yi maka bayani kayi min shiru,dagowa yai ya kalleta yace ina ganin ba abinda zaki sawa kanki damuwa bane wannan saboda kinsan deen yarone mai kokari shike rike da companies dina har guda 3 ina ganin yayi stressing kansa ne dayawa shiyasa kansa ke masa ciwo but i'm sure idan yayi wanka yasha magani kuma ya samu full time rest ze warware,,,,kije yanzu aiki nakeyi banaso ki katsemin aikina,ganin alhaji modibbo bashi da niyyar saurararta yasa mom ficewa cikin damuwa ta koma dakin da deen yake a kwance,sake kallonsa tai tace deen ya jikin naka?da kyar ya bude bakinsa yace mom ciwon kan nan sai karuwa yakeyi kamar karomin shi akeyi...idontane ya fara zubar da hawaye cikin damuwa tace shikenan yanzu deen mutuwa zakayi?na shiga 3 na lalace,da sauri ya dago ya kalli mom dake magana batasan ma tana yiba yace mom mutuwa kuma?shi kam dariya ma ta bashi,,,,,saurin girgiza kanta tayi tace mutuwa zakayi ko deen?shikenan na shiga 3 na lalace amma deen kana jin alamun mutuwane a jikinka?murmushi ya danyi kadan duk da azabar ciwon kansa yace mom yanzu fa naji kince min mutuwa zanyi shiyasa kikaji na maimaita ina tambayarki ai,,,,bata jira ya sake cewa komaiba ta fita daga dakin ta dauko jakarta a palour ta sake tarar da sadiq ganin zata fita batai mishi magana ba ya sashi saurin cewa mom,cak ta tsaya tana kallonsa,karasawa inda take yayi yace mom yanzu kika dawofa kuma naga kina shirin sake fita lafiya kuwa?tsaki tai tace eh fita zanyi sai kuma akayi yaya?ko so kake in zauna ina ji ina gani deen ya mutu ina kallo?toh fita zanyi in nemo doctor ya dubamin lafiyarsa,bata jira ya sake cewa komaiba tai ficewarta cikin tsananin tsoro,girgiza kai sadiq yai yana mamakin yanda mom ta damu da deen yau rana daya haka
"Shiga dakin deen yai ya tarar dashi kwance sedai wannan karon akwai alamar sauki don wayace a hannunsa,kallon deen yai yace wai menene yake damun mom ne haka yau duk ta rikice ta rude saboda kawai nace mata kanka yana ciwo ko mom batasan ka saba wannan ciwon kan ba?murmushi deen yayi yace eh nima nayi mamaki sosai naga mom ta rikice sosai kuma kasan mom batasan ina wannan ciwon kan ba saboda lokacin i was in my mansion shiyasa,gyara kwanciyarsa yayi yace asap bakasan ma wani abin dariya ba dazu fa mom har cewa takeyi wai mutuwa zanyi abin ya bani dariya sosai i was shocked da naji ta fadi haka but sena fuskanci she's out of her mind ta fadi haka,,a tare sukayi dariya har suna dafe ciki sannan deen yace wai dama haka mom take sona toh lallai ya kamata muyi playing wani game da mom,,,,a tare sukayi dariya
"Gidan hajiya hindu ta wuce direct ta umarceta data rakata gurin boka me ruguzau don ta bashi hakuri,sedai suna parking tun daga inda suka saba ajiye mota suka fara ganin bakin hayakin wuta yana tashi,komai na gurin boka me ruguzau ya kone tare da gawarsa a gefe itama tana ci da wuta ga wasu macizai a gefe suna jiran wutar ta gama cinye shi suma suyi nasu aikin wa'iyazubillah Allah ya tsaremu da shirka amin(kamar yanda wuta ta gama qona boka ne ruguzau haka macizai da sauran abubuwan kyama ke jiransa a kabari tare da mala'ikan da zeci gaba da hukuntashi da hukunci mafi tsanani da muni har zuwa ranar da za'a tashi duniya yaje ya hadu da mahaliccinsa daga nan wutar jahannama zata zama nan ne gidansa na karshe,kamar yanda karshen boka me ruguzau ze kasance toh haka karshen duk wata mace ko namiji me zuwa gurin boka zai kasance domin dukaninsu shirka suke aikatawa)
"Sosai mom ta zube kasa tana tsananin kuka kamar mahaukaciya tana fadin shikenan ya mutu be karya asirin da yayiwa deen ba,yanzu shima deen mutuwa zeyi,hajiya hindu ke rarrashinta wayarta ya fara ringing ganin number sadiq yasa mom dagawa da sauri sedai jin abinda sadiq ya fada mata ya sata jefar da wayar ta fasa ihu ta fadi kasa sumammiya

Don't forget to vote,share and comment

DeenWhere stories live. Discover now